Sunday, April 5, 2026
Home Blog Page 3

Bankin Duniya ya amince da bashin $500m domin bunkasa noma a Nijeriya

  • Bankin Duniya ya amince da bayar da bashin dala miliyan 500 ta karkashin shirin International Development Association domin farfado da bangaren noma a Nijeriya, musamman ga kananan manoma da kuma inganta tsaron abinci.

Kudin za su tallafa wa shirin Nigeria Sustainable Agricultural Value Chains for Growth Project (AGROW), wanda ke da burin kara yawan amfanin gona, hada manoma da kasuwanni, da kuma samar da ayyukan yi a fadin kasar.

A cikin wata sanarwa da Bankin Duniya ya fitar, ya bayyana cewa an amince da bashin ne a ranar 30 ga Maris, 2026, domin inganta aikin kananan manoma, karfafa darajar noma, da kuma bunkasa wadatar abinci da abinci mai gina jiki.

Bankin ya kuma jaddada cewa noma shi ne babban bangaren da ke daukar ma’aikata a Nijeriya, amma har yanzu yana fuskantar kalubale kamar karancin kayan aiki masu inganci, sauyin yanayi, da kuma rashin isasshen hanyoyin kai kayayyaki kasuwa.

Haka kuma, ya ce da dama daga cikin kananan manoma na rayuwa ne a matakin noma don ciyar da kansu kawai, yayin da matsalar rashin wadataccen abinci da ingantaccen abinci ke ci gaba da damun al’umma a fadin kasar.

An saka ranar 14 ga Afrilu don yanke hukunci kan bukatar ba da belin El-Rufai

Kotun Tarayya da ke Kaduna ta sanya ranar 14 ga watan Afrilu, 2026 domin yanke hukunci kan bukatar beli da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya gabatar.

A yau Laraba ne lauyoyin El-Rufa’i wanda ake kara da kuma masu gabatar da kara wato ICPC suka gabatar da hujjojinsu a gaban kotun da ke Kaduna domin duba batun bukatar ba da tsohon gwamnan na jihar Kaduna beli.

Babban lauyan masu kare El-Rufai, Adewole Iyamu, ya bayyana cewa suna da kwarin gwiwar samun sakamako mai kyau, yana mai cewa sun gabatar da dukkan hujjojinsu yadda ya kamata a gaban kotu.

Iyamu ya tabbatar da cewa an gabatar da bukatar belin a hukumance, kuma bangaren masu kara sun mayar da martani akan bukatar.

Haka kuma, ya ce ana sa ran El-Rufai zai gurfana a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar 10 ga watan Afrilu kan wata kara daban da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta shigar.

A cewarsa, bangaren wanda ake kara sun kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin sauraron karar ranar 10 ga Afrilu, inda ya ce sun riga sun shigar da dukkan takardun da ake bukata.

Kotu na tuhumar direban matar Sarki Sanusi a Kano da wasu mutane bisa zargin sata

Wata kotun majistare da ke Nomansland a karamar hukumar Fagge, jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare direban matar Sarki Muhammadu Sanusi II, tare da wasu mutum biyu bisa zargin satar wayar matar sarkin, da kudade da wasu kayayyaki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wadanda ake tuhuma sun hada da Sulaiman Yakubu Kulkude, Idris Musa da Abdullahi Usaini, inda aka gurfanar da su kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hadin baki, sata da karbar kayan sata.

Mai gabatar da kara, Barista Abubakar Ibrahim, ya bayyana wa kotu cewa Sulaiman, wanda ke aiki a matsayin direban matar Sarki Sanusi, ya shiga dakinta ba bisa ka’ida ba, ya sace kayayyakin da aka kiyasta kudinsu ya kai naira miliyan 60, tare da wasu kudade da wayar salula.

A lokacin da aka karanta tuhume-tuhumen, Sulaiman ya amsa laifi, yayin da sauran biyun suka musanta. Koda yake Lauyan wadanda ake tuhuma, Barista A.A. Abdullahi, ya gabatar da bukatar beli.

Alkalin kotun, Mai shari’a Halilu Abdurahman, ya amince da bayar da beli ga wadanda ake tuhuma tare kuma da dage shari’ar zuwa ranar 14 ga Afrilu, sai dai za a ci gaba da tsare su har sai sun cika sharuddan belin.

El-Rufai ya isa kotu kan neman beli a Kaduna

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya isa Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna domin ci gaba da sauraron bukatar ba da belinsa.

Ya isa kotun da misalin karfe 9 na safe a ranar Laraba, a karkashin tsauraran matakan tsaro da jami’an ‘yan sanda da na DSS suka kafa.

Zaman kotun ya biyo bayan dage shari’ar da alkalin kotun, Mai shari’a Rilwan Aikawa ya yi a ranar Talata, sakamakon wasu sabbin matakan shari’a tsakanin bangaren wanda ake kara da na masu gabatar da kara.

Lauyoyin El-Rufai karkashin jagorancin Ubong Akpan sun fara gabatar da bukatar alkalin ya janye daga shari’ar bisa zargin son kai, amma daga baya suka janye wannan bukata, lamarin da ya janyo tsaiko a shari’ar.

Bangaren masu gabatar da kara ma sun gabatar da takardar martani suna adawa da bayar da beli, abin da ya bai wa bangaren wanda ake tuhuma lokaci kadan don mayar da martani, wanda hakan ya sa aka dage sauraron shari’ar zuwa ranar Laraba.

Ana zargin El-Rufai da aikata laifuka da suka hada da zamba, wawashe kudade da kuma mallakar kudaden jama’a ba bisa ka’ida ba, inda Hukumar ICPC ta shigar da karar.

Tallata hajarka a DCL Hausa I Advertise with DCL Hausa

 

Reach Millions Across Northern Nigeria

DCL Hausa is a leading Hausa-language digital media platform, reaching over 60 million users monthly across Facebook, TikTok, YouTube, Instagram, and our websites.

We help brands, institutions, and public figures connect directly with Hausa-speaking audiences through impactful digital storytelling.

Why Choose DCL Hausa?

  • 60M+ Monthly Reach across Northern Nigeria
  • Highly Engaged Hausa Audience
  • Multi-Platform Visibility (Facebook, TikTok, YouTube, Web)
  • Trusted & Credible Media Brand
  • Tailored Campaign Solutions

Our Advertising Services

Video Production & Promotion

Interviews, reports, campaign videos, branded content

Audiograms & Jingles

Audio promotions optimized for digital engagement

Sponsored Posts

Picture posts, pinned posts, story placements

Event & Campaign Coverage

Full media coverage including video, LIVE, and social clips

 Facebook LIVE Streaming

Live broadcast for events, press briefings, and campaigns

Articles & Sponsored Content

Published on dclhausa.com and dcl-english.com

Who We Work With

  • Government & Public Institutions
  • Political Parties
  • NGOs & Development Partners
  • Corporate Brands
  • Religious & Community Organisations

Editorial Standards

All advertisements must comply with DCL Hausa’s editorial and ethical standards. We reserve the right to reject content that does not meet our guidelines.

Start Your Campaign Today

👉 Request Our Rate Card
👉 Book a Campaign Consultation

📞 Contact Us

Phone / WhatsApp:
+234 703 465 6392
+234 814 161 6576
+234 808 333 0298
+234 806 117 9716

Email:
media@dclhausa.com


DCL Hausa – Connecting You to the Hausa Audience That Matters


 

Atiku ba shi da kashi daya bisa dari na kudin kamfen din Tinubu – jigo a jam’iyyar ADC

Wani jigo a jam’iyyar ADC, Dele Momodu, ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ba shi da karfin kudin da zai iya fafatawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Momodu ya yi wannan bayani ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.

A cewarsa, yanayin siyasar Najeriya na nuna alamun komawa tsarin jam’iyya guda, inda ya kwatanta halin da ake ciki da lokacin mulkin tsohon shugaban soja Sani Abacha.

Momodu ya kuma karyata rade-radin cewa yana shirin cin amanar Atiku, yana mai cewa bai taba halartar wani taro a boye ba ba tare da sanin Atiku ba.

Sai dai ya bayyana cewa dangantakarsa da Tinubu ta fi kusa fiye da ta Atiku, lamarin da ya sa wasu ke zargin cewa yana iya zama dan leken asirin Tinubu a cikin bangaren adawa.

Ziyarar Tinubu zuwa Landan hanyace ta sabunta hadin gwiwar Birtaniya da Nijeriya

Yayin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke shirin kai ziyara birnin Landan na kasar Birtaniya, a wani mataki da ake kallon zai taimaka wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya bayyana cewa ziyarar wata dama ce ta sake farfado da mu’amala mai karfi tsakanin kasashen biyu.

A wata rubutacciyar sharhi da ya fitar gabanin ziyarar, Dare ya ce Burtaniya na daga cikin kasashen yamma da suka fi fahimtar tsarin siyasa da cibiyoyin gwamnati na Najeriya tsawon lokaci.

Sai dai ya kara da cewa a wasu lokuta kasar Burtaniya na nuna kamar ta nesanta kanta idan aka fara yada wasu rahotanni ko zarge-zarge game da Najeriya a tattaunawar duniya.

Ya ce ana sa ran ziyarar za ta taimaka wajen karfafa tattaunawa da hadin kai tsakanin kasashen biyu kan muhimman fannoni kamar siyasa, tattalin arziki da tsaro.

Kashi 82 bisa 100 na ‘yan Nijeriya ba sa koshi a mulkin Tinubu – ADC

Jam’iyyar adawa ta ADC ta mayar da martani ga jam’iyyar APC kan kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda ta ce ‘yan Najeriya suna cikin ukuba a mulkin Tinubu.

A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, ADC ta musanta zargin cewa tana tunzura ‘yan ƙasa, tana mai cewa rahotannin da ke nuna ƙaruwar talauci zuwa kashi 63 cikin ɗari ba maganar siyasa ba ce, illa sakamakon bincike da ke nuna halin da jama’a ke ciki a kasar.

Jam’iyyar ta ce kafin cire tallafin man fetur, talauci a Najeriya na tsakanin kashi 50 bisa ɗari, amma yanzu ya ƙaru zuwa kashi 63, lamarin da ta ce ya jefa miliyoyin mutane cikin ƙuncin rayuwa.

A cewar jam’iyyar, bayanai sun nuna cewa kashi 82 na ‘yan Najeriya sun taɓa rasa isasshen abinci a cikin shekarar da ta gabata, kashi 82 ba su samu kulawar lafiya ba, kashi 79 ba su samu man girki ba, yayin da kashi 74 suka rasa ruwan sha mai tsafta.

Gwamnatin Nijeriya ta bankado masu shirin kunyata Tinubu a Birtaniya

Gwamnatin Nijeriya ta bankado shirin wasu kamfanonin waje na kunyata Tinubu yayin ziyararsa a Birtaniya

Gwamnatin Tarayya ta ce ta gano wani shiri da wasu kamfanonin hakar ma’adinai na kasashen waje ke yi domin bata wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu suna a lokacin ziyararsa ta kasa zuwa Birtaniya.

Ma’aikatar Ma’adinai ta kasa ta ce wani kamfani mai suna Jupiter Ltd na shirin kaddamar da wata manufa ta yada jita-jita da kuma daukar nauyin zanga-zanga domin kunyata shugaban kasa yayin ziyarar.

A wata sanarwa da mataimakin ministan ma’adinai kan harkokin yada labarai, Segun Tomori, ya fitar, ya ce kamfanin na shirin daukar nauyin kamfen na kafafen yada labarai domin sukar gwamnati kan matakan da take dauka wajen tsaurara dokokin hakar ma’adinai.

Ana sa ran shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar kwanaki biyu kasar Birtaniya tare da matarsa uwargidan shugaban kasa Oluremi Tinubu.

Jaridar The Nation ta ruwaito wannan ita ce ziyarar kasa ta farko da Najeriya za ta kai a fadar Windsor cikin shekaru 37.

Ƙungiyar kwadago ta Nijeriya ta buƙaci gwamnati ta rage haraji

Ƙungiyar kwadago ta Nijeriya ta buƙaci gwamnati ta rage haraji bayan tashin farashin ma

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC, ta buƙaci gwamnatin tarayya ta samar da matakan rage raɗaɗin rayuwa ga ma’aikata bayan tashin farashin fetur da aka samu a ƙasar.

Shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa inda ya ce tashin farashin mai ya ƙara tsananta wahalar tattalin arziki da ke addabar ma’aikata da sauran ‘yan ƙasa.

NLC ta buƙaci gwamnati ta bayar da alawus da zai saukaka wa yan kasa da kuma ƙarin albashi na wucin gadi ga ma’aikata, tare da rage wasu haraje-haraje musamman ga masu ƙaramin albashi domin rage wahalar rayuwa.