DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mai dakin shugaban Nijeriya Remi Tinubu ta kaddamar da shirin bai wa mata dubu 18,500 a Nijeriya tallafi

-

 

Remi Tinubu

Uwargidan shugaban Nijeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta tabbatar da cewa mata dubu18,500 a fadin shiyyoyi shida na kasar za su ci gajiyar shirin bayar da tallafin jari domin karfafa musu gwiwa, wanda aka fara a Arewa ta tsakiyar Nijeriya.

Remi ta bayyana haka ne a lokacin da take jawabi a garin Bida, na jihar Neja, a ranar Juma’a, 21 ga Fabrairu, 2025, a lokacin da ta gabatar da kayayyaki ga mata domin karfafa musu gwiwa da suka hada Firiza, Tanda, Janareta, da injin nika ga wadan da suka amfana. 

Mai dakin gwamnan Jihar Neja, Hajiya Fatima Umaru Bago ce wakilce ta, a yayin bikin da ta jaddada cewa karfafawa mata gwiwa na da matukar muhimmanci wajen cimma muradun ci gaba kasa.

Remi ta ce shirin ya yi daidai da tsarin Shugaba Bola Tinubu, wanda ke ba da fifiko ga ci gaban tattalin arziki, da ci gaba mai dorewa. 

A shiyyar Arewa ta tsakiya, mata 500 daga kowace jiha – Niger, Nasarawa, Kogi, Kwara, Plateau, da kuma babban birnin tarayya Abuja, sun karbi kayan tallafi ta hannun ko’o dinetocin kungiyar mata ta shugaban kasa ta Renewed Hope Initiative.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Sabon Paparoma ya gayyaci Shugaba Tinubu zuwa Rome, Italy

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amsa goron gayyatar da sabon Paparoma Pope Leo XIV ys yi masa zuwa birnin Rome na kasar Italy. Daga cikin tawagar...

Da yiwuwar a samu ambaliyar ruwa a jihohi 12 na Nijeriya – NEMA

Hukumar ba da agajin gaggawa a Nijeriya NEMA, ta yi kira ga jihohin kasar da su zamo cikin shiri domin tunkarar ambaliyar ruwa da ke...

Mafi Shahara