Nijeriya ta fara kai iskar gas ta LNG a kasashen China da Japan

-

Nijeriya ta fara kai iskar gas ta LNG a kasashen China da Japan

Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC Ltd.) ya fara jigilar jigilar iskar Gas (LNG) zuwa kasashen Japan da China bisa dogaron Ex-Ship (DES).

Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin NNPC, Mista Olufemi Soneye ya rawaito Mista Segun Dapo, Shugaban zartarwar na, NNPC Ltd., na bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin.

An ambato Dapo yana cewa ci gaban ya yi daidai da dabarun da kamfanin ke da shi na zama amintaccen mai samar da makamashi a duniya.

“Baya ga samun karin kudi, tsarin na DES ya baiwa NNPC Ltd. damar kutsawa cikin sassan da ke karkashin LNG,

Kamfanin Dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Delivered Ex-Ship (DES) wani tsarine na kasuwanci na kasa da kasa wanda ke buƙatar mai siyarwar ya kai kayan sa a wata tashar jiragen ruwa.

Soeye ya kuma ruwaito Dapo na cewa, kamfanin na NNPC ya samu nasarar hakan ne tare da hadin gwiwar wasu rassansa guda biyu.

Ya lissafta kamfanonin kamar NNPC LNG Ltd da NNPC Shipping Ltd.

Ya ce ta isar da kayanta na farko na DES LNG daga jirgin ruwan LNG mai tsawon mita 174,000,a Japan, a ranar 27 ga Yuni, 2024.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kotu a Kano ta daure wani mutum saboda laifin sare bishiya ba bisa ka’ida ba

Wata kotun majistare da ke zamanta a unguwar Rijiyar Zaki dake jihar Kano, ta yanke wa Inuwa Ayuba hukuncin daurin watanni biyu a gidan yari...

An ji karar harbe-harbe a wurin taron magoya bayan Wike a jihar Bayelsa

An shiga cikin tashin hankali a birnin Yenagoa ta jihar Bayelsa, bisa karar harbe-harbe da aka ji a wurin masu biyayya ga ministan babban birnin...

Mafi Shahara