DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 110

Jam’iyyar APC ta yaba wa Tinubu bisa tabbatar da adalci a zaben jihar Anambra

0

Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta yabawa shugaban Nijeriya Bola Tinubu bisa kare dimokuraɗiyyar Nijeriya ta hanyar guje wa tsoma baki a zaben gwamnan Anambra da aka gudanar a ranar Asabar.

Mai magana da yawun jam’iyyar a jihar, Mista Seye Oladejo, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce matsayar shugaban ta nuna jajircewarsa wajen tabbatar da sahihin zabe da kare dimokuraɗiyya.

Oladejo ya ce rashin tsoma bakin shugaban kasa a harkar zaben ya ƙara tabbatar da cancantarsa a matsayin gwarzon dimokuraɗiyya, tare da karfafa gwiwar jama’a a tsarin zabe.

Haka kuma, ya yabawa hukumar zabe ta INEC bisa gudanar da abin da ya kira zabe mai inganci da gaskiya, yana mai cewa jagorancin sabuwar hukumar ya kawo sabon salo na dimokuraɗiyya a Nijeriya.

A cewarsa, sakamakon zaben ya nuna rashin daidaito da tsari a cikin haɗakar jam’iyyun adawa, inda ya bayyana su a matsayin “taron ’yan siyasar da ke fafutuka da son zuciya ba tare da tsari ko hangen nesa ba.”

Rikon sakainar kashi da gwamnatin Nijeriya ke yi wa ilimi ne silar tarin matsaloli a bangaren – ASUU

0

Shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya (ASUU), Farfesa Chris Piwuna, ya ce gwamnatin kasar ba ta ɗauki harkar ilimi a matsayin abu mai muhimmanci ba, domin yawancin jami’an gwamnati ba sa kallon matsalolin fannin a matsayin lamari na ƙasa da ke buƙatar haɗin kai.

Yayin tattaunawar da aka yi da shi a shirin “The Toyin Falola Interviews” a ranar Lahadi, Piwuna ya bayyana cewa halin ko in kula na manyan jami’an gwamnati ne ke hana samun kyawawan sauye-sauye masu ɗorewa a fannin ilimi.

A cewarsa, mambobin majalisar zartarwa ta Nijeriya kan ɗauki matsalolin ilimi a matsayin aikin ministan ilimi kaɗai, ba abin da ya shafi sauran ma’aikatun gwamnati ba.

Piwuna ya ƙara da cewa rashin fahimta da cin hanci suna ƙara tsananta matsalar, yayin da ƙungiyar ASUU ke yin yajin aiki don neman a aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tun 2009 da kuma warware batutuwan da suka shafi albashi, tallafi da sabunta jami’o’in gwamnati.

’Yan bindiga sun kai hari tare da sace mata 5 a kauyen ‘yan Kwada da ke jihar Kano

0

Wasu ’yan bindiga sun kai hari a kauyen ‘Yan Kwada da ke cikin kauyen Faruruwa, karamar hukumar Shanono a jihar Kano, inda suka sace mata biyar da suka haɗa da masu shayarwa a daren Lahadi.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa ’yan bindigar sun iso da yawansu dauke da makamai, inda suka kutsa gidaje da dama kafin su tafi da matan.

A cewarsa, daga cikin matan da aka sace, biyu sun dawo gida, yayin da uku har yanzu ke hannun ‘yan ta’addan.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa wannan harin ya faru ne mako guda bayan rundunar soji ta kashe ’yan bindiga 19 a fafatawar da suka yi a yankin.

Har ila yau, mazauna Faruruwa da sauran yankunan da ke kan iyakar Kano da Katsina na ci-gaba da rayuwa cikin fargaba sakamakon hare-hare ba kakkautawa, lamarin da ya tilasta wasu mazauna kauyukan yin ƙaura zuwa birane don tsira da rayuwarsu.

Shehu Sani ya shawarci ’yan Nijeriya da aka soke musu biza da su komo gida kafin a kama su a Amurka

0

Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya shawarci ’yan Nijeriya da sauran ’yan Afirka da aka soke musu biza a Amurka su gaggauta komawa gida kafin jami’an tsaron kasar su kama su.

A rubutunsa da ya wallafa a shafin X (Twitter) a ranar Litinin, Shehu Sani ya ce duk tsawon lokacin da mutum zai zauna a ƙasar waje, za a tuna masa wata rana cewa ba gidan mahaifinsa ba ne.

Wannan na zuwa ne bayan rahoton da ya nuna cewa gwamnatin Donald Trump ta soke fiye da biza 80,000 tun daga watan Janairun 2025, ciki har da bizar dalibai da wasu da ake zargi da laifukan ta’addanci da kuma karya dokoki kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce sabbin matakan sun haɗa da rage wa’adin wasu nau’ikan biza ga ’yan Nijeriya da kuma buƙatar masu neman biza su buɗe asusunsu na sada zumunta domin ƙarin bincike a kansu.

An garkame mutane sama da 700 bisa laifukan da suka shafi ta’addanci – Gwamnatin Nijeriya

0

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa an yanke wa mutane sama da 700 hukunci saboda laifukan da suka shafi ta’addanci a fadin kasar, yayin da wasu ke ci-gaba da fuskantar shari’o’i a kotuna daban-daban.

Ministan yada labarai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce kotun musamman ta shari’ar ‘yan ta’addan Arewa maso Gabas ta gudanar da zama sau bakwai, inda aka samu sama da mutane 700 da laifuka tare da aikewa da su gidan yari, kuma yanzu tana zaman nata na takwas don sauraron sabbin shari’o’i.

Idris ya kara da cewa hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta kammala bincike kan manyan laifuka kamar harin cocin Owo da Nyanya, yayin da ‘yan sanda da jami’an NSCDC ke ci-gaba da shari’o’i a fadin kasar kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cewarsa, babban lauyan gwamnati na jagorantar dukkanin hukumomi wajen tabbatar da adalci cikin lokaci da kuma hukunta masu aikata laifukan ta’addanci har ma da satar albarkatun kasa.

Ku rungumi zaman lafiya a tsakaninku duk wanda muka kama zai fuskanci fushin hukuma – Gwamna Nasir Idris ga manoma da makiyaya

0

Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya gargadi manoma da makiyaya da ke rikici a karamar hukumar Arewa ta jihar su daina fada su zauna lafiya, inda ya ce duk wanda aka kama yana tayar da fitina za a kama shi a gurfanar da shi gaban kotu.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara ga mutanen da suka rasa matsuguni sakamakon rikicin, wadanda ke samun mafaka a ofishin karamar hukumar da ke Kangiwa.

A cewarsa, yaje ne don jajanta wa iyalan wadanda suka mutu a wannan mummunan rikici, sai dai ya gargadi garesu da su daina daukar doka a hannu.

Gwamnan ya kuma ce ana nan ana gudanar da bincike,duk wanda aka kama da hannu kan wannan rikici tabbas zai fuskanci fushin hukuma tare da gurfanar da shi domin daukar mataki na gaba.

Hukumomin kasar Madagascar sun kama mutane biyu ‘yan kasar waje bisa zargin kitsa juyin mulki

0

Hukumomin kasar ta Madagascar sun ce an kama mutanen biyu ne ‘yan kasar waje a kasar biyo bayan zargin da ake musu da yunkurin kitsa wa shugaban kasar Michael Mandrianirina juyin mulki.

Wannan zargi ya biyo bayan wani bincike da hukumomin leken asiri ta kasar Madagascar ta kaddamar kamar yadda sabon babban darakta janar dinta Rufin Tolojara Lebiria ya sanar a yayin wani taron manema labarai.

Mutanen biyu da ba a bayyana kasar su ta asali ba ‘yan kasuwa ne da ke zaune a kasar sun dauki a kalla shekaru biya, kuma binciken da aka yi a wata babbar masana’antar daya daga cikin su ya sa an gano kudin da ya kai kwatankwacin Euro 385,000 da wadansu tarin makamai.

Tinubu ya yaba wa shugaban hukumar zaben Nijeriya INEC bisa gudanar da sahihin zabe a Anambra

0

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya yaba wa shugaban hukumar zabe ta kasa INEC, Farfesa Joash Amupitan, bisa gudanar da abin da sahihin zabe a jihar Anambra a ranar Asabar.

A cewar shugaban kasa, hukumar ta nuna ci gaba wajen gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci, inda ya bukaci ta ci gaba da inganta ayyukanta don ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya.

Hukumar INEC ta bayyana Farfesa Charles Soludo na jam’iyyar APGA, a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 422,664.

Babbar kotun kolin Guinée Conakry ta fitar da sunayen ‘yan takarar da ta amince da su

0

Babbar kotun kolin Guinée Conakry ta fitar da sunayen ‘yan takarar da ta amince da takardunsu ne a zaben shugaban kasar a ranar Asabar 8 ga watan Nuwamba 2025.

‘Yan takara 9 ne ta amince da takardun bukatar tasu ciki har da shugaban gwamnatin mulkin sojin kasar, Mamadi Doumbouya da ke kan karagar mulki tun 2021, bayan ya yi wa Alpha Condé juyin mulki.

Sai dai kotun ta yi watsi da wadansu takardun ‘yan takarar a kalla talatin.

A ranar 28 ga watan Disamba mai 2025, ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a Guinée Conakry.

’Yan Republican na neman a kwace shaidar zama dan Amurka daga Zohran Mamdani

0

’Yan jam’iyyar Republican ta Donald Trump neman a kwace shaidar zama dan Amurka daga hannun Musulmin da ya lashe zaben Magajin birnin New York, Zohran Mamdani.

Wasu ’yan jam’iyyar Republican ne suka fara kira da a karbe shaidar zamansa dan kasa, zargin cewa ya samu shaidar zama ɗan ƙasar ta hanyar da bata dace ba.