DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 109

Gwamnati ta bukaci ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankalinsu kan barazanar Trump

0

Gwamnatin Nijeriya ta bukaci ’yan kasar su kwantar da hankalinsu dangane da sabanin diflomasiyya da ke tsakaninta da Amurka.

Ministan yada labarai Alhaji Mohammed Idris ne ya yi wannan kira yayin da ya kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi a ranar Litinin.

A cewar sanarwar da Malam Rabiu Ibrahim, mataimakin minista na musamman kan yada labarai ya fitar a Abuja, Idris ya je Jigawa ne domin halartar taron matasan Arewa maso Yamma na 2025 da kuma gabatar da nasarorin da shugaba Tinubu ya cimma cikin shekaru biyu da suka gabata.

Ministan ya ce shugaba Tinubu na da cikakkiyar kwarewa da karfin guiwa wajen kare martabar Nijeriya da gyara duk wata matsala ta dangantaka da kasashe abokan hulɗa.

A cewarsa, ’yan Nijeriya kada su firgita, su kwantar da hankali, Tinubu zai iya warware lamarin cikin lumana kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin Nijeriya na neman a dawo da Ekeremadu gida

0

Tsohon mataimakin majalisar dattawan Nijeriyar na fuskantar daurin shekaru 9 a gidan yarin Birtaniya, bayan samun sa da laifin siyan sassan jikin dan Adam.

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin Nijeriya ta aike da tawaga ta musamman, wadda ta hada da ministan harkokin waje Ambasada Yusuf Tuggar da kuma ministan shari’a Lateef Fagbemi SAN domin tattaunawa da hukumomin Birtaniya.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa wannan yunkuri na daga cikin bukatar shugaba Tinubu na neman a saki Ekeremadu da wuri, ko kuma sake bibiyar hukuncin da aka yanke masa, ta hanyar bin tsarin dokokin shari’a da ‘yancin dan Adam.

‘Yan sandan Nijeriya sama da 100,000 na tsaron rayuwar manyan mutane – Rahoton EU

0

Wani rahoto ya nuna cewa jami’an ‘yansandan Nijeriya sama da dubu dari ne ke aikin tsare rayuka da dukiyoyin ‘yan siyasa da kuma mutane masu muhimmanci a kasar.

 

Rahoton wanda hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Turai ta wallafa a watan Nuwamba da muke ciki, ya nuna damuwa kan yadda ake samun karancin jami’an da za su kare sauran al’ummar kasar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

 

Kazalika ya kuma yi hasashen cewa rundunar ‘yan sandan Nijeriya na da jami’ai akalla 371,800 wadanda kare rayukan mutane sama da miliyan 236 ya rataya a wuyansu.

 

A cewar rahoton, ba karamin abin damuwa bane yadda ake ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro da kuma karancin jami’ai, a daidai lokacin da ake aika da yawa daga cikin ‘yansandan aikin kare wasu mutane kalilan.

Yadda cibiyar Nana Khadija ke taimakon wadanda aka ci zarafin su a Sokoto

Cin zarafin mata da yara yana daga cikin manyan matsalolin da ke ci gaba da barazana ga lafiyar jama’a da mutuncin al’umma. Duk da haka, yawanci waɗanda abin ya shafa ba sa kai rahoto saboda tsoro, kunya, da al’adun da ke hana magana.

A Sokoto, wannan matsala ta dade tana ɓoye ne a cikin shiru — har sai da aka kafa Cibiyar Nana Khadija Sexual Assault Referral Centre (SARC), wadda ta tashi tsaye wajen tallafa wa mata da yara da aka ci zarafinsu ta hanyar ba da kulawa, shawara, da taimakon da suke bukata.

A cewar rahoton ƙungiyar Invictus Africa, an samu rahotanni 1,762 na cin zarafi a Sokoto a shekarar 2023. Wannan adadi ya nuna irin yawaitar matsalar da ake fama da ita a cikin al’umma.

Alhaji Sani Umar Jabbi Sarkin Yakin Gagi, wani shugaban al’umma ne a jihar Sokoto, ya bayyana cewa, rashin ilimi da rashin dokoki ko hukunta wadanda suka aikata laifin cin zarafi, na daga cikin abubuwan da ke kara haddasa wannan matsalar.

Sarkin Yakin Gagi, Sokoto.

“A baya idan an sami mace ko yaro da aka yi wa fyade, iyalai kan yi shiru saboda suna tsoron abin kunya ko zargi. Wannan shiru shi ke sa mutane su ƙara shiga cikin raɗaɗi.”

Sai dai a yanzu, Cibiyar Nana Khadija wacce aka kafa a shekarar 2020 ƙarƙashin haɗin gwiwar Tarayyar Turai da Majalisar Ɗinkin Duniya (EU–UN Spotlight Initiative) tare da Gwamnatin Jihar Sokoto, ta zama mafaka ga waɗanda abin ya shafa.

Koodinetan cibiyar, Dokta Auwal Ahmad, ya ce suna karɓar mutanen da suka fuskanci cin zarafi cikin sirri da mutunci.

Dr Auwal Ahmed Musa

“Muna ba su taimako domin tabbatar da lafiyarsu, muna basu shawara don kwantar da hankalinsu, sannan muna tura su zuwa wani wurin idan matsalar ta fi karfinmu,” in ji Dokta Auwal.

A cewarsa, cibiyar tana tallafa wa mutum akalla 25 a kowane wata, adadin da ya nuna cewa yanzu mutane sun fara fita daga tsoron neman taimako.

Shugabannin al’umma sun tabbatar da cewa aikin cibiyar na sauya yadda mutane ke kallon batun cin zarafi.

“Yanzu mutane sun fara magana. Iyayen mata suna kai rahoto kai tsaye idan wani abu ya faru, kuma malamai suna faɗakar da jama’a cewa kare yara da mata wajibi ne. Wannan babban sauyi ne a al’umma,” in ji Sarkin Yakin Gagi.

Yayin da duniya ke gudanar da kwanaki 16 na yaƙi da cin zarafin mata da yara, cibiyar Nana Khadija ta zama alamar yadda haɗin gwiwar likitoci, malamai, da shugabannin al’umma ke samar haifar da mafita ga masu rauni a cikin al’umma.

Za ku iya kallon cikakken rahoton a nan: https://www.facebook.com/share/v/19n1XGyyth/

Wannan labari ya zo muku ne da tallafin kungiyar Nigeria Health Watch a wani ɓangare na shirin yaɗa labarun samar da sauyi a Afirka

EFFC na neman tsohon karamin ministan man fetur na Nijeriya ruwa-a-jallo

0

Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa ta ayyana tsohon karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, wanda ake nema ruwa-a-jallo bisa zargin hada baki da karkatar da kudade har dala miliyan 14.8.

EFCC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, inda ta ce kudaden sun shafi jarin da hukumar NCDMB ta saka a kamfanin matatar Atlantic International don gina masana’antar sarrafa mai.

Sanarwar, wadda mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale ya sanya wa hannu, ta ce an ayyana neman Sylva ne bayan kotun jihar Legas ta bayar da takardar kama shi a ranar 6 ga watan Nuwamban 2025.

EFCC ta roki duk wanda ke da bayanai game da inda yake ya kai rahoto zuwa ofishin hukumar mafi kusa ko kuma ya sanar da hukumomin tsaro.

Gwamnatin Nijeriya za ta cigaba da taimaka ma ‘yan gudun hijira da masu karamin karfi – Ministan jin kai

0

Ministan jin kai da rage talauci Bernard Doro, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya da ke cikin mawuyacin hali cewa gwamnati tana da cikakken kudiri na taimaka musu da kuma tabbatar da tsaron rayukansu.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a Jos a ranar Litinin, Doro ya ce manufar ma’aikatarsa ita ce tabbatar da cikar buri ga talakawa, masu gudun hijira, da sauran marasa galihu.

A cewarsa, ma’aikatar za ta inganta tsarin tallafi, fadada damar samun shirye-shiryen rage talauci, tare da tabbatar da cewa taimakon jin kai yana isa ga wadanda suka fi bukata.

Ministan ya kara da cewa gwamnati za ta aiwatar da ayyukan jin kai ba a matsayin taimako ba, sai a matsayin hakkin da gwamnati ke da shi ga ‘yan Nijeriya, domin tabbatar da abinci, ilimi, da mafaka ga marasa karfi.

Wani mutum ya rasa ransa a wani gidan mata masu zaman kansu a jihar Rivers

0

Wani mutum da ba a tantance bayanansa ba ya rasa ransa bayan ya yanke jiki ya fadi a wani gidan mata masu zaman kansu da ke titin Azikiwe, Mile 2 Diobu, a Fatakwal, Jihar Rivers a ranar Lahadi.

Wasu majiyoyi sun ce mutumin ya yi sa-in-sa da guda daga cikin ma’aikatan gidan kafin ya fadi kasa inda aka garzaya da shi asibiti, likitoci kuma suka tabbatar da mutuwarsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa an mika binciken ga sashen binciken manyan laifuka (SCID).

Rundunar ta kuma tabbatar da kama wani mutum da ake zargi da hannu a lamarin, yayin da wasu daga cikin matan da ke wurin suka arce bayan faruwar abin.

Wike ya ba masu kadarorin da suka karya doka wa’adin kwanaki 14 su biya tarar Naira miliyan 5 a Abuja

0

Ministan Abuja Nyesom Wike, ya bai wa masu kadarori a Asokoro, Maitama, Garki da Wuse wa’adin ƙarshe na kwanaki 14 daga ranar 11 ga watan Nuwamba, 2025, don su bi dokokin amfani da ƙasa.

Mai taimaka wa ministan, Lere Olayinka, ya ce wa’adin ya biyo bayan ƙarewar wa’adin farko na kwanaki 30, inda ya gargadi masu kadarori cewa duk wanda bai bi doka ba za a ɗauki matakin karfi a kansa.

FCTA ta ce wuraren da abin ya shafa sun haɗa da Gana da Usuma a Maitama, Yakubu Gowon a Asokoro, da Aminu Kano da Adetokunbo Ademola a Wuse II inda aka umarci masu kadarorin da suka karya doka su biya tarar Naira miliyan biyar tare da sabunta takardunsu.

Wike ya kuma amince da sabbin takardun mallaka na shekaru 99 ga wadanda suka daidaita amfani da filaye, sai dai rangwamen bai shafi waɗanda aka riga aka soke filayensu ba.

Kotu ta ba da tsohon shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy beli daga gidan yari

0

Wata kotu a birnin Paris ta bayar da belin tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy a ranar Litinin, bayan da ya daukaka kara kan hukuncin da aka yanke masa bisa laifin hada baki wajen neman kudin kamfen daga tsohon shugaban Libiya, marigayi Muammar Gaddafi.

Sarkozy, wanda ya mulki Faransa daga 2007 zuwa 2012, ya fara zaman gidan yari ne a ranar 21 ga watan Oktoba bayan kotu ta same shi da laifin hada baki a watan Satumba, inda ya bayyana cewa zama a kurkuku ya kasance mawuyaci gare shi.

Kotu ta bayyana cewa Sarkozy ba barazanar guduwa yake ba, don haka zai fita daga gidan yari amma karkashin kulawar shari’a, ciki har da takaita tafiyarsa zuwa kasashen waje da kuma hana shi magana da jami’an ma’aikatar shari’a.

Dan karamin dansa Louis ya wallafa rubutu a shafinsa na X cewa, ” Taimakon Allah ga ‘yanci” tare da tsohon hotonsa da mahaifinsa bayan kotu ta amince da belin kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Gwamnatin Nijeriya ta sha alwashin inganta tsaro bayan rahoton Birtaniya

0

Gwamnatin Nijeriya ta ce tana daukar matakai don inganta tsaro a duk fadin Nijeriya biyo bayan sabon gargadi game da tafiye-tafiye da Birtaniya ta fitar kan jihohi da dama sakamakon ta’azzarar ayyukan ta’addanci, sace mutane tare da yin garkuwa da su.

Ofishin harkokin waje na Birtaniya ya ja hankalin ‘yan kasarsa da su guji dukkan tafiye-tafiye zuwa jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Gombe, Katsina, da Zamfara, sannan ya yi gargadin kaucewa dukkan tafiye-tafiye sai dai idan ya zama dole.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya ce gwamnati ta san da matsalolin tsaro kuma tana aiki tukuru wajen magance su, da kara inganta kayan aiki da ayyukan leken asiri, haka kuma dukkan baki a Nijeriya za su kasance cikin tsaro yayin da matakan ke ci-gaba da aiki.

Sai dai gwamnatin Jihar Gombe ta musanta gargadin, tana mai cewa bayanan da Birtaniya ta fitar basu dace ba kuma babu adalci a cikin su.