DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 111

Shugaba Tinubu ya taya Soludo murnar sake lashe zabe

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya taya Gwamna Chukwuma Soludo murna bisa sake lashe zaben gwamnan jihar Anambra, yana mai cewa nasarar da ya samu ta tabbatar da irin jagoranci na gari da yake gudanarwa.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fita, Tinubu ya ce nasarar Soludo a zaɓen da aka gudanar ranar Asabar ta sanya shi zama gwamna na uku a tarihin siyasar jihar da ya yi nasara a wa’adi na biyu.

Tinubu ya kuma yaba wa al’ummar jihar,jami’an tsaro da hukumar zaɓe INEC bisa yadda aka gudanar da zaɓen cikin lumana da kwanciyar hankali.

Wajibi ne saka kyamarorin tsaro a gidajen man Burkina Faso – Hukumomin tsaron kasar

0

Gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ta umurci masu gidajen mai na kasar da su saka kyamarorin tsaro daga yanzu, zuwa 1 ga watan sabuwar shekara mai kamawa ta 2026.

Umurnin na kunshe a cikin wata takarda da ministan tsaron kasar ya aike wa masu gidajen man.

Matakin ya biyo bayan wata ganawa ce da hukumomin kasar ta Burkina Faso suka yi da jagorori gidajen mai da dillalen man fetur na kasar wadanda suka dauki alkawalin ba da gudunmawar su domin yaki da ta’addanci a kasar.

Sojojin Nijeriya sun fatattaki ’yan ta’adda tare da halaka bakwai da kama mutum 27

0

Sojojin Nijeriya sun kai farmaki kan ’yan ta’adda da masu aikata laifuka a faɗin Nijeriya, inda suka halaka mutane bakwai, suka kama 27, tare da kwato danyen mai da aka sace a wasu hare-haren da aka kai cikin sa’o’i 48 da suka gabata.

Wannan ci gaban ya biyo bayan umarnin da babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayar na ganin an kawar da duk wata ƙungiyar ta’addanci da masu laifi.

Ya kuma sake karfafa gwiwar dakarun rundunar yayin ziyararsa ta aiki zuwa yankin Arewa maso Gabas.

Messi ya taimaka an zura kwallaye 400 a tarihin tamaularsa

0

Messi ya kafa sabon tarihi a duniyar kwallo bayan ya taimaka wajen cin kwallaye 400 a tarihinsa na kwallo wani abin da ba a taba yi ba.

Wannan nasara ta tabbata ne a wasan da Inter Miami ta lallasa Nashville SC da ci 4-0 a gasar Major League Soccer, kamar yadda mai rahoto kan harkokin wasanni Fabrizio Romano ya bayyana.

Messi ya taimaka wajen cin kwallaye biyu da Tadeo Allende ya zura a mintuna na 73 da 76.

A tsawon kusan shekaru 20 na aikinsa, Messi ya yi fice a kungiyoyin Barcelona, Paris Saint-Germain, da yanzu Inter Miami, inda ya ke ci gaba da kafa tarihi.

‘Yan sanda sun kama dan fashi da makamin da ya boye bindigarsa cikin biredi a Nijeriya

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta kama wani matashi da ake zargin dan fashins, wanda aka gano ya boye da bindiga a cikin Burodi.

Mai magana da yawun rundunar, SP Bright Edafe, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar a garin Asaba, babban birnin jihar.

Edafe ya ce jami’an sun kama wanda ake zargin, Nnamdi Stanley Chibuike mai shekaru 24, lokacin da suke gudanar da binciken ababen hawa a Koka Roundabout, Asaba, ranar 6 ga Nuwamba, 2025, a cewarsa, an gano bindiga kirar gida a cikin Burodi, kuma an kama wanda ake zargi nan take.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abaniwonda Olufemi, ya jinjinawa jami’an bisa wannan nasara, yana mai cewa hakan na nuna yadda rundunar ke ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin kwarewa domin dakile laifuka.

Soludo na jam’iyyar APGA, ya sake lashe zaben gwamna a Anambra

Gwamna Chukwuma Soludo ya samu nasarar sake lashe zaben gwamnan jihar Anambra na shekarar 2025, inda hukumar zaben Nijeriya INEC,ta bayyana shi a hukumance a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u masu yawa.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa sakamakon da aka sanar da shi da safiyar Lahadi ya nuna cewa Soludo ya yi nasara a dukkanin kananan hukumomi 21 na jihar.

Farfesa Omoregie Edoba, wanda shi ne jami’in tattara sakamakon kuma Shugaban Jami’ar Benin UNIBEN, ne ya bayyana Soludo a matsayin wanda ya ci zaben.

Soludo, dan takarar Jam’iyyar APGA, ya samu kuri’u 422,664, ya doke babban abokin takararsa Nicholas Ukachukwu na APC wanda ya samu 99,445. Sai Paul Chukwuma na YPP da ya zo na uku da 37,753, sannan George Moghalu na LP da 10,576, yayin da Jude Ezenwafor na PDP ya samu 1,401 kacal.

Gwamnatin Katsina ta musanta jita-jitar tashin hankali a wasan Katsina United da Barau FC

0

A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Katsina, Injiniya Sirajo Yazid Abukur, ma’aikatar ta bayyana cewa labarin da ake yadawa cewa magoya bayan Katsina United sun tayar da tarzoma a lokacin wasan su da Barau FC ba gaskiya ba ne.

Ma’aikatar ta ce bayan cikakken bincike daga jami’an tsaro, jami’an wasan, da masu sa ido masu zaman kansu, babu wani abu da ya nuna an samu tashin hankali ko jikkata mutum. An tabbatar cewa wasan ya gudana cikin kwanciyar hankali, inda magoya baya daga ɓangarorin biyu suka nuna ladabi da girmamawa.

Sanarwar ta yaba da yadda ’yan wasan da magoya bayan Katsina United ke ci gaba da zama abin koyi wajen nuna halin kirki a filayen wasa, tare da jaddada cewa Jihar Katsina ta dade tana da suna wajen nuna ɗabi’a da biyayya a wasanni.

Ta kuma shawarci jama’a da su guji yada labaran ƙarya da jita-jita marasa tushe da ka iya tayar da hankali, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da kula da harkokin wasanni cikin zaman lafiya da tsaro ga kowa da kowa.

An ceto mataimakin kakakin majalisar dokokin Jihar Kebbi daga hannun ‘yan bindiga

0

Gwamnatin Jihar Kebbi ta tabbatar da ceto mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Honarabul Samaila Muhammad Bagudu, daga hannun ‘yan bindiga bayan wani samame da jami’an tsaro suka gudanar.

A wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi, Yakubu B. Tafida, ya fitar ranar Asabar, gwamnati ta bayyana cewa an ceto dan majalisar lafiya lau, kuma yana karɓar kulawar da ta dace daga hukumomin lafiya.

DCL Hausa ta ruwaito cewa, gwamnatin ta yaba ƙoƙarin hadin gwiwar jami’an tsaro da suka jagoranci aikin ceton.

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa gwamnatin Kebbi ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin kawar da matsalar ‘yan bindiga da sauran barazanar tsaro a jihar.

Gwamnati ta roƙi jama’a su ci gaba da goyon bayan hukumomin tsaro tare da kasancewa masu lura da abin da ke faruwa a yankunansu, da kuma sanar da hukumomi duk wata alama ta abin da ake zargi.

Shugaban kasar Djibouti zai sake tsayawa takara karo na shida

0

Shugaban ƙasar Djibouti mai shekaru 77, Ismail Omar Guelleh zai sake tsayawa takara karo na shida

Shugaban kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh, wanda yake mulki tun daga 1999, zai sake tsayawa takara a karo na shida a zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar a shekara mai zuwa, bayan majalisar dokokin ƙasar ta cire dokar da ke hana wanda ya haura shekara 75 tsayawa takara.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa shugaban majalisar dokokin kasar, Dileita Mohamed Dileita, ne ya tabbatar da hakan bayan taron jam’iyyar RPP, inda ya ce sun gama amincewa da Guelleh a matsayin ɗan takara.

Guelleh, mai shekaru 77, ya kasance cikin jerin tsoffin shugabannin Afirka da ke neman tsawaita mulkinsu, irin su Paul Biya mai shekara 92 na Kamaru, da Alassane Ouattara mai shekara 83 na Côte d’Ivoire.

A zaɓen shekarar 2021 ya samu nasara da kaso 97 cikin ɗari, yayin da jam’iyyarsa ke da rinjaye a majalisar dokokin kasar.

Dan takarar ADC a zaben gwamnan Anambara ya zargi jam’iyyar APGA da sayen kuri’u

0

Dan takarar ADC a zaben gwamnan Anambra, John Nwosu, ya zargi jam’iyyar APGA da sayan da kuri’a a zaben da yake ci-gaba da gudana a jihar.

Nwosu ya bayyana hakan ne bayan ya kada kuri’arsa a Oduda Central School, Ward 2, da ke karamar hukumar Nnewi North ranar Asabar da misalin karfe 11:28 na safe, inda ya jaddada cewa ya gamsu da yadda jama’a suka fito, sai dai ya soki yadda ake raba kudi don jan hankalin masu kada kuri’a domin su zabi wata jam’iyya.

Kazalika, dan takarar jam’iyyar APC, Nicholas Ukachukwu, shi ma ya yi korafin cewa ana sayan kuri’a da tsoratar da wakilan jam’iyyu a wasu sassan jihar.