DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 113

NAPTIP ta ceto mutane 221 daga hannun masu fataucin mutane a jihar Jigawa

0

Hukumar da ke kula da hana fataucin mutane, NAPTIP ta jihar Jigawa ta ce ta ceto mutane 221 da aka yi fataucinsu cikin shekaru biyu da suka gabata.

Kwamandan hukumar a jihar, Malam Abdulladir Turajo, ya bayyana hakan a taron wayar da kai da aka gudanar a Kazaure, inda ya ce an maido da waɗanda aka ceto zuwa ga iyalansu tun bayan kafa ofishin hukumar a watan Yuli 2023.

A cewarsa, hukumar ta samu hukunta masu laifina sau biyu tare da gudanar da shirye-shiryen wayar da kai guda 175 a makarantu, kasuwanni, wuraren ibada da tashoshin mota a fadin jihar.

Taron wanda aka shirya tare da ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Jigawa, na cikin shirin fadakarwa a matakin ƙananan hukumomi 27 na jihar, kuma an fara shi da yankin arewa maso yamma na jihar Jigawa.

Gwamnatin Tinubu ta kaddamar da shirin ba da bashi ga ma’aikatan manyan makarantu kasar

0

Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da ba da bashin Naira miliyan 10 ba tare da ruwa ba a karkashin shirin tallafa ma ma’aikatan manyan makarantu (TISSF), domin karfafa guiwa da inganta walwalar ma’aikatan manyan makarantu a fadin kasar.

Ministan Ilimi na Nijeriya, Tunji Alausa, ya bayyana haka a bikin kaddamar da shirin a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Akure (FUTA), inda ya ce wannan mataki wani muhimmin bangare ne na ajandar Renewed Hope ta shugaban Nijeriya Bola Tinubu, wacce ta mayar da hankali kan ci-gaban ilimi da habaka jarin jama’a.

Shirin yana bai wa ma’aikata damar samun bashin har zuwa Naira miliyan 10 ba tare da ruwa ba, don tallafawa bukatu irin su gina gida, kula da lafiya, sufuri da kananan sana’o’i.

Fiye da ma’aikata 9,000 daga manyan makarantu 219 na jihohi da na tarayya sun riga sun karɓi wasiƙar amincewa, inda fiye da mutum 400 suka samu kudinsu.

Alausa ya yi kira ga wadanda suka ci gajiyar shirin da su biya cikin lokaci domin tsarin ya cigaba da taimakawa wasu, yayin da gwamnati ta tabbatar da cewa gaskiya, bin doka da kulawa a kowane lokaci za su kasance ginshikan nasarar shirin nan gaba.

Duk da tallafin kudaden tsaro daga Amurka, an kasa kare rayukan Kiristoci a Nijeriya – Dan majalisar Amurka

0

Ɗan majalisar Amurka Riley Moore ya zargi gwamnatin Nijeriya da gazawa wajen kare Kiristoci duk da biliyoyin dalolin tallafin tsaro da take samu daga Amurka.

Jaridar Punch ta ruwaito Moore, wanda ke jagorantar kwamitin binciken da shugaban Amurka Donald Trump ya kafa kan zargin gallaza wa Kiristoci a Nijeriya, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a wani shiri na The Dinesh D’Souza a daren Alhamis.

Moore ya ce ‘yan’uwansa Kiristoci ana kashe su saboda imaninsu ga Yesu Almasihu, yana mai sukar shiru daga hukumomin Nijeriya da kuma kasashen duniya tare da gargadi cewa rashin daukar mataki kan matsalar na iya jawo tasirin tsaro mai muni.

Hakazalika, Moore ya bayyana halin da ake ciki a matsayin “kisan kiyashi da aka manta da shi”, inda ya bukaci Nijeriya da abokanta na waje da su dauki matakan gaggawa don kare rayukan Kiristoci da kawo karshen tashin hankali.

Majalisar dattawan Nijeriya za ta haramta barasar leda daga karshen wannan shekarar

0

Majalisar dattawa ta umurci NAFDAC da kada ta ƙara wa’adin hana samar da giya a leda da ƙananan kwalabe bayan 31 ga Disamba, 2025.

Sanata Asuquo Ekpenyong ya ce matakin na bin ƙa’idar duniya ne don rage illar shan giya tsakanin matasa, inda ya zargi wasu masana’antu da neman ƙarin lokaci don karya doka.

Shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya ce wajibi ne a aiwatar da dokar gaba ɗaya don kare matasa daga illolin giya mara ƙa’ida.

Hukumar alhazan Nijeriya ta kammala duba gidajen saukar alhazai a Madina don aikin hajjin 2026

0

Hukumar alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta bayyana cewa ta kammala duba wuraren saukar alhazai da masu samar da abinci a birnin Madina a cikin shirin farkon da take yi na gudanar da aikin hajji na shekarar 2026.

Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban hukumar ta fuskar yada labarai, Ahmad Muazu, ya fitar a ranar Juma’a.

A cewar Muazu, kwamitin ya duba sama da otal 20 da wuraren dafa abinci guda bakwai a yankin markaziyya, inda suka tabbatar da bin ƙa’idojin tsaro, tsafta da sharuddan hukumar.

Hukumar ta NAHCON ta bayyana cewa za ta cigaba da tabbatar da cewa dukkan alhazai daga Nijeriya suna samun ingantaccen ayukka da ya dace da kuɗin da aka biya, tare da ƙarfafa tsare-tsaren da ke tabbatar da gaskiya da inganci wajen hidimomin aikin Hajji.

Shugaba Tinubu ya rantsar da Doro da Udeh a matsayin ministoci

0

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis, ya rantsar da Dr. Bernard Doro da Dr. Kingsley Udeh a matsayin sababbin ministoci, kafin fara zaman majalisar zartarwa na farko tun watan Yuli.

Dr. Doro, kwararren likita daga Filato, ya maye gurbin Farfesa Nentawe Yilwatda, yayin da Dr. Udeh daga Enugu ya maye gurbin Uche Nnaji wanda ya yi murabus kan takardun karatu.

Bayan rantsuwar, Tinubu ya jagoranci zaman majalisar inda ministan kudi, Wale Edun, ya bayyana cewa dawowar Nijeriya kasuwar lamuni ta duniya ta jawo karuwar sha’awar masu saka jari, inda kudin Eurobond ya samu karin bukata mai yawa.

Edun ya ce gwamnati za ta cigaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, ta inganta kasuwanci, da tabbatar da rarraba ribar ci-gaba ga ’yan kasa kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Akwai yiwuwar madugun adawar Kamaru Isa Tchiroma yana Nijeriya ya boye – Rahotanni

0

Madugun adawar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, wanda ya kalubalanci nasarar Paul Biya, yana iya kasancewa yana a Nijeriya kamar yadda Africa Intelligence ta ce, amma wasu majiyoyi sun ce ya koma Abuja a ruwaitowar jaridar Daily Trust.

Rahoton ya ce an fitar da shi daga gidansa da ke Marouaré a Garoua tsakanin 28 da 29 ga watan Oktoba inda a sakonsa na Facebook, ya gode wa sojojin da suka raka shi zuwa wuri mai aminci.

A cewar rahoton, an tsallaka da shi zuwa Nijeriya bayan fargabar kai masa hari daga jami’an tsaro yayin da a safiyar 29 ga watan Oktoba, aka ji harbe-harbe a unguwarsa.

Ministan harkokin cikin gida, Paul Atanga Nji, ya gargade shi kan tada rikicin bayan zabe, yana mai cewa ya karya doka da ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zabe kafin sakamakon hukuma ya fita.

Fusatattun matasa sun hallaka limamin masallaci a jihar Kwara bisa zargin maita

0

Wasu fusatattun matasa a garin Sokupkpan da ke ƙaramar hukumar Edu a jihar Kwara sun hallaka limamin masallacin yankin, Malam Abdullahi Audu, bisa zargin cewa shi ne ya haddasa mutuwar wani mazaunin garin mai suna Ibrahim Gana ta hanyar maita.

Shaidu sun ce lamarin da ya faru a ranar Laraba inda ya jefa al’umma cikin firgici da tashin hankali. Gana, wanda ya rasu yana fama da rashin lafiya, ya sha cewa limamin ne ke damunsa a mafarki, abin da ya sa wasu suka fara yarda cewa yana da hannu cikin ciwonsa.

A cewar majiyoyi, bayan rasuwar Gana, ’yan’uwansa suka tattara wasu matasa suka kai wa limamin hari, duk da ƙoƙarin dattawa na hana su. Sun bugi malamin har lahira suna zargin ya kashe Gana ta hanyar maita.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kakakin ’yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar al’amarin, tana mai bayyana shi da mummunan al’amari.

Majalisar dokokin Amurka ta gabatar da kudirin hukunta jami’an gwamnatin Nijeriya

0

Majalisar dokoki ta Amurka ta gabatar da sabon kudiri mai taken “Nigeria Religious Freedom Accountability Act of 2025”, wadda ke neman hukunta jami’an gwamnatin Nijeriya da ake zargin suna da hannu wajen take hakkin ’yancin addini da cin zarafin jama’a.

Kudirin, wanda dan majalisa Marlin Stutzman daga jihar Indiana ya dauki nauyinsa, an gabatar da shi ne a ranar 21 ga Oktoba, kuma yanzu yana gaban kwamitocin kula da harkokin wajen Amurka da na shari’a domin nazari.

A cikin kudirin, an umarci shugaban Amurka da ya sanya takunkumi ga jami’an Nijeriya da ke da hannu ko suka amince da cin zarafi na addini, ciki har da gwamnoni, alkalai, da jami’an tsaro da suka aiwatar da dokokin batanci ko suka rufe ido kan tashin hankali da aka yi da sunan addini.

Idan aka amince da kudirin, zai bai wa Amurka damar sanya takunkumi kan duk wani jami’i ko hukumomi a Nijeriya da ake zargin suna goyon bayan zalunci ko laifukan da suka saba wa ’yancin addini, abin da zai kara tsananta matsin lamba daga Washington kan Nijeriya.

Akpabio ya gargadi minista a majalisa da ka da ya amsa duk wata tambaya kan kalaman Trump

0

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, ya gargadi wanda aka zaba domin mukamin minista, Barista Kingsley Udeh (SAN), da kada ya amsa kowace tambaya da ta shafi kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da Nijeriya.

Udeh, wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zaba domin maye gurbin tsohon ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, ya bayyana a gaban majalisar a ranar Alhamis don tantancewa.

Nnaji ya yi murabus ne a watan da ya gabata bayan cece-kuce kan sahihancin takardun karatunsa.

Lokacin tantancewar, Akpabio ya bukaci Udeh da ya gabatar da kansa sannan ya ce, tambayar da kawai zan roƙe ka kada ka amsa ita ce wadda ta shafi Trump.

Daga karshe, majalisar ta amince da nadin Udeh a matsayin minista ta hanyar kada kuri’ar murya.