DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 112

Ya kamata Nijeriya ta farka daga barcin da take yi saboda barazanar da Trump ya yi mata – Bishop Kukah

0

Shugaban Cocin Katolika a Sokoto Archbishop Matthew Kukah ya bayyana cewa barazanar Shugaban Amurka Donald Trump kan yiwuwar kai harin ga Nijeriya a matsayin nuni ga kasar da ta farka daga baccin da take yi.

Da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru 60 da haihuwa na Dr. Reuben Abati a Legas, Bishop Kukah ya lokaci ya yi da Nijeriya za ta tashi daga dogon barcin da ke yi, ta sake ginuwa da gaskiya da kishin kasa.

A makon da ya gabata ne Shugaba Trump na Amurka ya yi ikirarin cewa ana cin zarafin Kiristoci a Nijeriya, yana kuma barazanar daukar matakan soja da ci-re tallafin da Amurka ke bai wa kasar.

Wata dattijuwa ta barke da kuka bayan an hanata kada kuri’a

0

Wata datijuwa mai shekaru 96 a duniya, Mrs. Elizabeth Onike, ta barke da kuka a rumfar zaɓe saboda an hana ta kada kuri’a a Anambara

Dattijuwar wadda ke zabe a akwatin Umudim Akasi Polling Unit 019, Agulu II, Ward 8, a ƙaramar hukumar Anaocha, jihar Anambra, a ranar Asabar.

Da take magana cikin harshen Igbo, tsohuwar ta bayyana takaicinta cewa a nan take yin zaɓe tun da dadewa.

Rahoton jaridar Punch ya ce ta ma kada kuri’a a zaɓen da ya gabata, amma yanzu jami’an INEC suna cewa katinta ba shi da inganci.

Elizabeth ta ji takaici matuka saboda ba za ta kada kuri’a a wannan zaɓen ba, wanda zai tantance wanda zai zama sabon gwamna ta.

Lamarin ya jawo tausayawa da damuwa daga wasu masu zaɓe da ke wajen, inda da dama suka yi kira ga hukumar INEC da ta duba irin waɗannan matsaloli domin kare haƙƙin zaɓen tsofaffi a nan gaba.

Lewandowski ba zai bar Barcelona a watan Junairu ba

0

Rahotanni na nuni da cewa Robert Lewandowski ba zai bar Barcelona a watan Janairu ba, amma akwai yiwuwar kashi 90 cikin 100 zai bar ƙungiyar a kakar wasa mai zuwa.

A dai-dai lokacin da dan wasan mai shekaru 37 kwantiraginsa ke shirin karewa da kungiyar, rahotanni sun nuna cewa Barcelona na duba yiwuwar sabunta tawagarsu da sababbin ‘yan wasa masu tasowa.

An ce ƙungiyar tana son rage yawan albashin da take fitarwa da kuma ba da dama ga sabbin ‘yan gaba matasa kafin kakar 2025/2026.

Ka nemi yafiya bayan janye kalamanka na barazana ga Nijeriya – Barau Jibrin

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Barau Jibrin, ya caccaki Shugaban Amurka, Donald Trump, bisa barazanar kai wa Nijeriya hari da ya yi,saboda zargin ana yi wa Kiristocin kasar kisan kiyashi.

Jaridar Punch ta rawaito cewa a cikin wani faifan bidiyo an gano Sanata Barau Jibrin na cewa furucin Trump ya saba wa dokar ƙasa da ƙasa bisa wannan kuduri da ya dauka.

Ya kuma bukaci shugaban Amurkan da ya janye kalamansa tare da bai wa Nijeriya hakuri, yana mai cewa, bai dace shugaban Amurka ya ce zai kai wa wata ƙasa hari saboda ra’ayi ba, idan akwai matsala kamata ya yi a bi ta hanyar diflomasiyya.

Miyetti Allah ta koka kan hare-haren da ake kai wa Fulani a jihar Benue

0

Kungiyar Miyetti Allah reshen Jihar Benue ta roki gwamnatin Nijeriya da ta jiha da su shiga tsakani kan abin da ta bayyana a matsayin hare-hare da ake ta kaiwa ‘ya’yanta a karamar hukumar Ohimini a jihar Benue.

Shugaban kungiyar na jiha, Ardo Muhammad, wanda ya sa hannu kan wata sanarwa a ranar Juma’a, ya zargi al’ummar Awule tare da jami’an sa-kai na jihar da kai hare-hare kan sansanonin Fulani a yankin.

Muhammad ya bayyana cewa rikicin ya fara ne a karshen watan Agusta 2025 lokacin da wasu ‘yan bindiga daga al’ummar Awule tare da taimakon jami’an sa-kai suka kai hari kan sansanonin Fulani, inda suka kona sansanoni shida, suka kashe shanu 30, suka sace wasu, tare da kashe wani makiyayi mai suna Isu Abdulkarim.

A cewarsa, hare-haren sun ci-gaba a makonnin baya-bayan nan, abin da ya janyo asarar dabbobi da kuma raba makiyaya da muhallansu, yana mai musanta rahotannin da ke cewa makiyaya sun kai farmaki kan manoma.

Manyan Arewa za su tattauna yadda za a shawo kan matsalar tsaro a yankin

0

An shirya gudanar da babban taron tsaro a Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi, a ranar Litinin, 10 ga Nuwamba, 2025, domin tattauna hanyoyin magance karuwar matsalar tsaro a Arewacin Nijeriya.

Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III zai jagoranci taron tare da tsohon hafsan hafsoshin soji kuma tsohon ministan cikin gida, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau (rtd), tare da halartar gwamnonin Arewa, masana tsaro da sauran manyan jami’ai.

Shugaban kungiyar Arewa Broadcast Media Practitioners Forum, Alhaji Yelwa, ya ce taron zai samar da dandalin tattaunawa da hadin kai domin dawo da zaman lafiya da karfafa hadin kan kasa.

A cewarsa, taron zai hada ‘yan jarida, masu tsara manufofi, jami’an tsaro da kungiyoyin ci-gaba domin tsara dabarun sadarwa da za su taimaka wajen gina yardar jama’a, hana tsattsauran ra’ayi da tallafa wa gyaran tsarin tsaro na Nijeriya.

Gwamnan Neja ya sallami shugaban hukumar SUBEB daga aiki

0

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya kori shugaban hukumar ilimin firamare ta Jiha (SUBEB), Muhammad Baba Ibrahim, tare da dukkan mambobin dindindin na hukumar.

Sanarwar ta fito ne daga sakataren gwamnatin jiha, Alhaji Abubakar Usman, a ranar Juma’a, inda ya ce matakin yana cikin kokarin gwamnati na sake fasalin tsarin ilimi domin inganta aiki da gaskiya a fannin ilimi.

A cewarsa, dukkan mambobin hukumar da sakataren su mika dukkan takardu, kadarori da ragamar aiki ga babban sakataren ma’aikatar ilimin firamare da sakandare ta jihar.

Gwamna Bago ya gode wa wadanda aka kora bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci-gaban ilimi a jihar, tare da yi musu fatan alheri a ayyukan da za su gabatar nan gaba.

Shugaba kasar China Xi Jinping ya taya Paul Biya murnar nasarar zabe a Kamaru

0

Shugaban kasar China, Xi Jinping, ya taya shugaban Kamaru, Paul Biya, murnar sake lashe zaben shugabancin kasa, yana mai jaddada karfafa dangantaka mai karfi da dadadden tarihi tsakanin kasashen biyu.

A cewar rahoton da ma’aikatar harkokin wajen kasar China ta wallafa a ranar Juma’a, Xi ya bayyana cewa kasashen biyu sun gina amincewar juna ta siyasa tare da cimma manyan nasarori a fannonin hadin gwiwa daban-daban a cikin ‘yan shekarun nan.

Xi ya kara da cewa kasar China za ta cigaba da inganta huldar diflomasiyya, tattalin arziki da al’adu da kasar Kamaru a kokarin da take yi na karfafa alaka da nahiyar Afirka.

Haka kuma, ya jaddada cewa kasashen biyu suna ci-gaba da marawa juna baya kan muhimman al’amura da bukatun da suka shafi kasashensu.

Majalisar wakilan Nijeriya ta yi Alla-wadai da harin da aka kai ma dan majalisa a jihar Neja

0

Majalisar Wakilan Nijeriya ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa tawagar dan majalisa Jafaru Mohammed Ali, wanda ke wakiltar mazabar Borgu/Agwara ta Jihar Neja, a kan hanyar Lumma–Babanna a ranar Talata da yake kan hanyar taron mazabu.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun majalisar, Akin Rotimi, ya fitar a ranar Juma’a, harin ya yi sanadiyyar mutuwar wasu jami’an tsaro da ke rakiya tare da raunata direba da wasu daga cikin tawagar dan majalisar. Haka kuma an lalata wasu motoci a cikin tawagar.

Majalisar ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan jami’an da suka rasa rayukansu da kuma hukumomin tsaro, tare da rokon Allah ya ba wadanda suka ji rauni lafiya, tana mai kira da a gudanar da cikakken bincike domin kama wadanda suka aikata laifin.

Hakazalika, ta kuma jaddada cewa lamarin ya sake nuna gaggawar bukatar daukar mataki mai karfi da hadin gwiwa wajen yaki da matsalar rashin tsaro a yankunan kan iyaka, tare da alkawarin goyon bayan majalisa ga duk wani yunkuri na gwamnati wajen kawo karshen ta’addanci da garkuwa da mutane a fadin kasar.

Muna bibiyar barazanar hari da Amurka ke yi ma Nijeriya sau da kafa – Gwamnatin Rasha

Gwamnatin Rasha ta bayyana cewa tana sa ido sosai kan rahotannin da ke nuna yiwuwar Amurka ta kai farmaki a Nijeriya, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Maria Zakharova, ta tabbatar a ranar Juma’a.

A yayin taron manema labarai a Moscow, Zakharova ta ce Rasha tana kira ga Washington da sauran bangarorin da abin ya shafa da su bi doka da ka’idojin kasa da kasa wajen magance matsalar.

Rahotanni sun nuna cewa a ranar 1 ga watan Nuwamba, shugaban Amurka Donald Trump ya umurci Pentagon da ta tsara matakan soja da za a iya dauka a Nijeriya don kare al’ummar Kiristoci daga kungiyoyin ta’addanci kamar yadda jaridar TRT Afrika ta wallafa.

Sai dai gwamnatin Nijeriya ta ce ba ta lamuntar wariyar addini, inda ministan harkokin wajen kasar, Yusuf Tuggar, ya jaddada cewa tsarin mulkin Nijeriya yana tabbatar da ‘yancin addini da bin doka da oda.