DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 114

Majalisar dokokin Amurka ta gabatar da kudirin hukunta jami’an gwamnatin Nijeriya

0

Majalisar dokoki ta Amurka ta gabatar da sabon kudiri mai taken “Nigeria Religious Freedom Accountability Act of 2025”, wadda ke neman hukunta jami’an gwamnatin Nijeriya da ake zargin suna da hannu wajen take hakkin ’yancin addini da cin zarafin jama’a.

Kudirin, wanda dan majalisa Marlin Stutzman daga jihar Indiana ya dauki nauyinsa, an gabatar da shi ne a ranar 21 ga Oktoba, kuma yanzu yana gaban kwamitocin kula da harkokin wajen Amurka da na shari’a domin nazari.

A cikin kudirin, an umarci shugaban Amurka da ya sanya takunkumi ga jami’an Nijeriya da ke da hannu ko suka amince da cin zarafi na addini, ciki har da gwamnoni, alkalai, da jami’an tsaro da suka aiwatar da dokokin batanci ko suka rufe ido kan tashin hankali da aka yi da sunan addini.

Idan aka amince da kudirin, zai bai wa Amurka damar sanya takunkumi kan duk wani jami’i ko hukumomi a Nijeriya da ake zargin suna goyon bayan zalunci ko laifukan da suka saba wa ’yancin addini, abin da zai kara tsananta matsin lamba daga Washington kan Nijeriya.

Akpabio ya gargadi minista a majalisa da ka da ya amsa duk wata tambaya kan kalaman Trump

0

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, ya gargadi wanda aka zaba domin mukamin minista, Barista Kingsley Udeh (SAN), da kada ya amsa kowace tambaya da ta shafi kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da Nijeriya.

Udeh, wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zaba domin maye gurbin tsohon ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, ya bayyana a gaban majalisar a ranar Alhamis don tantancewa.

Nnaji ya yi murabus ne a watan da ya gabata bayan cece-kuce kan sahihancin takardun karatunsa.

Lokacin tantancewar, Akpabio ya bukaci Udeh da ya gabatar da kansa sannan ya ce, tambayar da kawai zan roƙe ka kada ka amsa ita ce wadda ta shafi Trump.

Daga karshe, majalisar ta amince da nadin Udeh a matsayin minista ta hanyar kada kuri’ar murya.

Shugaba Tinubu ya yi alwashin murkushe ta’addanci tare da karfafa dangantaka da kasashen waje

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na kawar da ta’addanci da kuma karfafa dangantaka tsakanin Nijeriya da abokan hulɗarta na duniya.

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis kafin zaman majalisar zartarwa na kasa da aka gudanar a fadar shugaban kasa, Abuja, zama na farko tun watan Yuli.

A cewarsa, ana tattaunawa da kasashen duniya ta hanyar diflomasiyya, kuma ya tabbatar da cewa za a murkushe ta’addanci.

Jawabin Tinubu ya zo ne kwanaki bayan shugaban Amurka Donald Trump ya sanya Nijeriya cikin jerin “Kasashen da ke da damuwa ta musamman,” abin da gwamnatin Nijeriya ta ce ba daidai ba ne wajen bayyana hakikanin matsalar tsaro.

Hakazalika Tinubu ya ce gwamnatinsa na ci-gaba da tattaunawa da kasashen duniya domin tabbatar da tsaro, zaman lafiya, da bunƙasar tattalin arzikin ƙasa.

Sarakunan gargajiya ne kan gaba wajen samar da zaman lafiya – Kungiyar International Alert

0

Gudunmuwar da sarakunan gargajiya ke badawa wajen samar da zaman lafiya, ba abin yadawa ba ce – Kungiyar International Alert

Ƙungiyar International Alert Nigeria ta bayyana cewa sarakunan gargajiya na taka muhimmiyar rawa wajen hana rikice-rikice a jihohin Zamfara da Katsina.

Shugaban ƙungiyar a Nijeriya, Sunday Momoh Jimoh, ne ya bayyana hakan a jawabin maraba yayin bude taron horar da sarakuna da manyan shugabannin al’umma kan warware rikici da hanyoyin daidaitawa, wanda aka gudanar a Katsina.

Ƙungiyar International Alert, wacce ba ta gwamnati ba ce, tana aiki a Nijeriya don ƙarfafa zaman lafiya, ƙarfafa cibiyoyin al’umma, da bunƙasa tattaunawa tsakanin jama’a.

Mr. Jimoh ya jaddada cewa ba za a iya watsar da rawar da sarakuna ke takawa ba wajen rage tashin hankali da rikice-rikice, inda ya ce horon na da nufin ƙara musu ƙwarewa wajen sasantawa da warware rikici ta hanyar da ta dace kuma mai adalci.

Ya kuma tabbatar da cewa ƙungiyar tana da niyyar ci gaba da tallafa wa gwamnoni da cibiyoyin shari’a domin inganta warware rikici a matakin ƙauyuka da al’umma.

Mahalarta taron sun haɗa da jami’an ma’aikatun Shari’a, Hukumomin Kananan Hukumomi da Masarautu, da kuma sarakunan gargajiya daga jihohin Zamfara da Katsina.

Rundunar sojin saman Nijeriya ta yi alkawarin kare rayukan farar hula lokacin gudanar da ayyuka

0

Babban hafsan sojin saman Nijeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya ce rundunar sojin sama za ta mayar da hankali kan kare rayukan fararen hula da gujewa mummunan hari kan farar hula yayin ayyukanta.

Aneke ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin ganawarsa ta farko da manyan hafsoshin rundunar a hedikwatar rundunar da ke Abuja, inda ya ce wannan mataki na cikin abin da shugaban Bola Tinubu ke bukata daga dakarun kasa.

Aneke ya ce rundunar za ta karfafa hulɗa da al’umma da kuma hadin kai da sauran hukumomin tsaro domin murkushe ta’addanci da hana maƙiya samun mafaka, sannan kuma kare rayukan fararen hula da gujewa mummunan hari shi ne ginshikin kwarewar aikin.

Hakazalika, ya kuma tabbatar wa hafsoshin cewa dukkan matakan rundunar za su bi umarnin shugaban kasa kai tsaye, tare da mayar da hankali kan inganci, tsaro da kare martabar sojin sama.

’Yan Majalisar Amurka 9 sun bukaci Amurka ta dauki mataki kan rikicin zaben Kamaru

0

Wasu ’yan majalisar dokokin Amurka tara sun rubuta wa sakataren harkokin wajen kasar, Marco Rubio, suna nuna damuwa kan tashin hankali, kisa, da kama mutane da dama da suka biyo bayan zaben shugaban kasa na Kamaru da aka gudanar a ranar 12 ga watan Oktoba.

A cikin wasikar, ’yan majalisar sun soki yadda gwamnati ke danniya kan masu zanga-zanga cikin lumana, tare da kira da a hukunta wadanda ke da hannu wajen kashe fararen hula. Sun bukaci gwamnatin Amurka ta matsa wa hukumomin Kamaru lamba domin su mutunta dimokuradiyya da hakkin dan Adam.

Wannan mataki ya biyo bayan yadda ake samun matsin lamba daga kasashen duniya, bayan rahotannin kashe mutane da dama da kama daruruwan mutane da kuma takurawa ’yan adawa bayan sake zaben shugaba Paul Biya da ake tantama a kai.

Masana harkokin diflomasiyya na ganin wannan matakin na ’yan majalisar Amurka a matsayin alamar cewa Washington na bin lamarin Kamaru da ido sosai kamar yadda jaridar MMI News ta wallafa.

Majalisar dokokin Amurka na neman haramta biza da toshe dukiyar mambobin Miyetti Allah

0

Sabon kudiri da majalisar dokokin Amurka ke tattaunawa ya bukaci kakaba takunkumin biza da kulle dukiyar mambobin kungiyoyin Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) da Miyetti Allah Kautal Hore, bisa zargin take hakkin ‘yancin addini a Nijeriya.

Kudirin, wanda dan majalisar Amurka Christopher Smith ya gabatar a ranar Talata, ya zo ne bayan shugaban kasa Donald Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasa mai damuwa ta musamman kan batun kisan Kiristoci, duk da musantawar gwamnatin Nijeriya.

Rahotanni daga The New York Times sun nuna cewa rundunar sojin Amurka ta riga ta tsara shirin kai hare-hare idan lamarin ya dauki zafi. Kudirin ya kuma hada ‘yan Fulani a jihohin Benue da Filato cikin jerin kungiyoyin da ake zargi da take ‘yancin addini.

Idan kudirin ya wuce, Amurka za ta samu damar kakaba takunkumin biza da kulle kadarorin duk wanda aka samu da hannu a irin wadannan ayyuka.

Baba-Ahmed ya bukaci Tinubu ya fito ya yi ma ‘yan Nijeriya bayani kan barazanar Amurka

0

Tsohon mai ba wa shugaban kasa shawara, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya bukaci shugaba Bola Tinubu da ya fito fili ya yi wa ’yan Nijeriya jawabi kan barazanar mamayar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa ƙasar.

A wata sanarwa da ya wallafa a Facebook ranar Alhamis, Baba-Ahmed ya bayyana damuwa cewa shugaban kasa bai ce komai kai tsaye ba tun bayan da lamarin ya faru kuma wannan shiru na iya nuna rauni da rashin tsari a shugabanci.

A cewarsa, bai kamata ministoci ko kakakai su rika magana ba, sai shugaban kasa da kansa ya fito ya tabbatar da matsayin Nijeriya da matakan da gwamnati ke ɗauka.

Haka kuma ya gargadi Tinubu da kada ya yi niyyar tafiya Amurka don ganawa da Trump, yana mai cewa hakan zai kara bata sunan Nijeriya.

Baba-Ahmed ya bukaci shugaban kasa da ya dauki mataki cikin gaggawa ta hanyar nada jakadu, farfaɗo da hulɗar diflomasiyya, da yin jawabi kai tsaye ga ’yan ƙasa don tabbatar da cewa Nijeriya tana da murya da matsayin kanta.

Sojojin Amurka na jiran umarnin Trump don kai farmaki Nijeriya

0

Rundunar sojin Amurka da ke Afirka, AFRICOM, ta gabatar da shirin kai farmaki a Nijeriya bayan umarnin shugaban Amurka, Donald Trump, bisa zargin kisan Kiristoci a arewacin ƙasar kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Rahoton ya nuna an tsara matakai uku wato mai nauyi, matsakaici da mai sauƙi domin bai wa gwamnati damar zabar irin martanin da ya dace ta ɗauka.

Shirin mai nauyi ya haɗa da tura jiragen yaƙi zuwa tekun Guinea don kai hare-hare a Arewacin Nijeriya, yayin da matsakaicin mataki zai dogara da jirage marasa matuka wajen kai farmaki kan sansanonin ’yan ta’adda.

Matakin na uku mai sauƙi kuma zai kasance haɗin gwiwa da sojojin Nijeriya domin yakar Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ta’addanci, tare da kare fararen hula a yankin.

Cristiano Ronaldo zai yi ritaya daga kwallon kafa nan ba da jimawa ba

0

Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa zai yi ritaya daga wasa nan ba da jimawa ba, yana mai cewa abu ne mai wahala kawo ƙarshen kyakkyawar rayuwarsa ta wasa. Ya bayyana haka ne a wani shirin tattaunawa da aka watsa a Burtaniya.

Ronaldo, wanda yanzu ke bugawa Al Nassr ta Saudiyya, shi ne mafi yawan zura kwallo a tarihin ƙwallon ƙafa da kwallaye 952 ga ƙungiyoyi da ƙasa. Kwanan nan ya ce yana fatan kai kwallaye 1,000 kafin ya ajiye takalman sa.

Ronaldo ya ce, tuni ya fara shirin rayuwa bayan ƙwallo tun yana da shekara 25 zuwa 27 kuma zai yi ritaya ne domin mai da hankali kan iyalinsa da tarbiyyar ’ya’yansa.

A cewarsa, har yanzu yana bibiyar tsohuwar ƙungiyarsa ta Manchester United duk da yadda ya bar kulob ɗin cikin rashin jituwa amma ya damu da halin da kungiyar ke ciki, domin kulob ɗin yana da tarihin ban mamaki kuma har yanzu yana da matsayi a zuciyarsa.