Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 32

Bincike ya nuna manoma a Nijeriya sun tafka asarar kusan Naira tiriliyan 5 a cikin watanni 24 da suka gabata

0

Wannan asara ta samu be sakamakon wasu manufofin gwamnati da suka haddasa faduwar farashin kayayyaki, sai kuma dogaro da hasashen yanayi daga hukumar kula yanayi ta Nijeriya NIMET da dai sauran su.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kungiyar Foundation for Peace Professionals ta fitar, inda ta bayyana cewa fannin noma a Nijeriya na fuskantar babbar matsalar da ke barazana ga samar da abinci.

Daraktan Abdulrazaq Hamzat, ya ce asarar da aka kiyasta na nufin manoma da dama sun rasa jarinsu a wannan yanayi da gwamnati ta shigo da sabbin tsaruka da suka karya kayayyakin da ake nomawa a cikin gida.

Kofa a bude take ga Rabi’u Musa Kwankwaso – Jam’iyyar APC

0

Jam’iyyar APC ta ce har yanzu kofarta a buɗe take ga jagoran NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, idan har ya yanke shawarar shiga cikinta.

Shugaban Jam’iyyar na Nijeriya Farfesa Nentawe Yilwatda ne ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Trust a ranar Lahadi, a daidai lokacin da ake ci gaba da rade radin sauya sheƙar Kwankwaso.

Farfesa Yilwatda ya ce ko da yake ba a fara wata tattaunawa kai tsaye da Kwankwaso ba a halin yanzu, APC za ta karɓe shi hannu bibbiyu idan ya zaɓi shigowa jam’iyyar.

Babban lauya a Nijeriya Femi Falana ya soki Majalisar Dattawa kan yin jinkiri wajen gyaran dokar zabe

0

Babban Lauya Lauya a Nijeriya Femi Falana, ya yi kakkausar suka ga Majalisar Dattawan Nijeriya kan jinkirta gyaran dokar zaɓe, yana mai gargaɗin cewa hakan na iya lalata sahihancin zaɓukan shekarar 2027.

Falana ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a gidan talabijin na Arise a ranar Lahadi, inda ya nuna damuwa kan matakin majalisar dattawa na sake kafa wani kwamiti domin nazarin kudirin dokar, duk da cewa majalisar wakilai ta amince da shi tun watan Disambar 2025.

Ya ce wannan mataki ba wai anyi ne don gyara tsarin zaɓe ba, illa dai ƙoƙarin ci gaba da amfani da tsohon tsari da ke da kura kurai, yana mai cewa ana yaudarar ‘yan Nijeriya ne da suna cewa ana aiki kan dokar.

‘Yan sanda sun nemi NLC ta dage zanga-zanga saboda barazanar tsaro a Abuja

0

Rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta shawarci ƙungiyar kwadago NLC da ta sake duba jadawalin zanga-zangar da ta shirya yi a ranar Talata, 3 ga Fabrairu 2026, bayan bayanan sirri sun nuna yiwuwar wasu ƙungiyoyi da ba na gwamnati ba, na kitsa yadda za su karkatar da zanga-zangar, lamarin da ka iya jefa jama’a cikin hatsari.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja SP Josephine Ade da ta aike wa kafafen yada labarai ciki hada DCL Hausa.

Shugaba Tinubu ya shafe kwanaki 22 a kasashen waje cikin Janairun 2026

0

Faransa, Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Turkiyya ne kasashen da shugaba Tinubu ya je a tsakanin wannan lokaci, inda ya halarci taruka daban-daban, baya ga kulla yarjejeniya a fannoni da dama.

Sai dai shugaban ya fuskanci suka daga wasu kungiyoyin fararen hula da kuma jam’iyyun hamayya, wadanda suka ce bai kamata Tinubu ya shafe lokaci mai tsayi a waje ba, daidai lokacin da Nijeriya ke fuskantar kalubale a cikin gida.

Amma shugaban jam’iyyar APC na Nijeriya Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce duk wata yarjejeniya da Tinubu ya kulla, ta kasance wadda za ta amfani ‘yan Nijeriya ne da kuma samar musu da ci-gaba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Rufa’i Hanga ya nemi a dawo da motocin da ya raba don aikin NNPP

0

Sanatan Kano ta tsakiya Rufa’i Sani Hanga ya nemi shugabannin kananan hukumomin yankinsa su dawo da motocin da ya ba su bayan ficewar su daga NNPP.

Wata sanarwa da ofishin Sanatan ya fitar, ta yi nuni da cewa tun da fari an raba wa shugabannin kananan hukumomin da ke yankin Kano ta tsakiya motocin ne don gudanar da ayyuka da suka shafi jam’iyyar NNPP, gabanin sauyin da aka samu a fagen siyasar Kano.

A makon da ya gabata ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya koma jam’iyyar APC bayan ficewa daga NNPP tare da daukacin shugabannin kananan hukumomin Kano da wasu yan majalisar dokokin jiha da na tarayya.

Kananan hukumomin da umarnin ya shafa sun hadar da Dala, Dawakin Kudu, Fagge, Garun Mallam, Gezawa, Gwale, Kano Municipal, Kumbotso, Kura, Madobi, Minjibir, Nasarawa, Tarauni, Ungogo da kuma Warawa.

Gyaran tattalin arzikin Tinubu ya kubutar da jihoji 27 daga durkushewa – Ministan yada labarai

0

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma Mohammed Idris, ya bayyana cewa gyare gyaren tattalin arziki da shugaban Tinubu ya aiwatar sun ceto jihohi 27 daga durƙushewar tattalin arziki.

Ministan ya bayyana haka ne yayin da yake bayani kan tasirin manufofin gwamnatin Tarayya, yana jaddada cewa sauye-sauyen da aka yi sun taimaka matuƙa wajen daidaita kuɗaɗen jihohi wajen biyan albashi da aiwatar da ayyukan raya ƙasa.

A cewar Mohammed Idris, kafin aiwatar da waɗannan gyare-gyare, jihohi da dama na fuskantar matsanancin ƙalubalen kuɗi, amma matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka karkashin shirin Renewed Hope Agenda sun kawo sauƙi tare da ƙara wa jihohi hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.

Kungiyar AES ta yi Allah wadai da harin da aka kai filin jirgin saman Yamai a Jamhuriyar Nijar

0

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta kuma shugaban kasar Burkina Faso kyaften Ibrahim Traoré, ta yi kakkausan suka kan harin da ta danganta da na dabbanci akan kasar ta Nijar da ke memba a kungiyar.

AES ta ce wannan hari wata barazana ce ga tsaron harin gwiwa na kasashen, kwanciyar hankalin yankin da kuma kokarin da suke yi tare na kawo zaman lafiya da ci gaban yankin Sahel.

Kazalika kungiyar ta yi kakkausan suka da gargadi ga duk masu tallafawa ‘yan ta’adda da kudi, makamai, ko da bayanan sirri ko kuma goyan baya a siyasance cewa sai sun amsa alhakin abinda suka aikata.

An sako jagororin adawa a Guinee Bissau bayan kamasu da sojoji suka yi

0

‘Yan adawa da kungiyoyin fararen hula da ECOWAS a kasar Guinée Bissau na nuna farin ciki da sakin manyan ‘yan adawar kasar bayan shafe sama da wata biyu a tsare.

Daga yanzu dai Domingos Simoes Pereira zai ci gaba zama karkashin saka ido yayin da shi kuma Fernando Dias da ya yi ikirarin lashe zaben shugaban kasa ya bar ofishin jakadancin Nijeriya cikin ‘yancin inda a yake samun mafaka a baya .

Sakin ‘yan siyasar ya zo ne sakamakon shiga tsakani da ministan tsaron Sénégal janar Birame Diop wanda shugaba Bassirou Diomaye Faye ya aika a matsayin dan aike na musamman shiga takani.

‘Yan bindiga sun kona coci da Ofishin ’yan sanda, tare da sace mutane a jihar Neja

0

Da safiyar Lahadi, 1 ga Fabrairu, 2026, ’yan bindiga sun kai mummunan hari a karamar hukumar Agwara, ta jihar Neja, inda suka kone Ofishin ’yan Sanda suka kona wani ɓangare na cocin UMC, tare da sace aƙalla mutane biyar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa maharan sun isa garin da misalin 3:40–4:00 na asuba, inda suka yi musayar wuta da jami’an tsaro kafin daga bisani su yi amfani da abubuwan fashewa suka kona ofishin ’yan sanda bayan sun ci karfin jami’an da ke wurin.

Bayan haka, maharan sun nufi cocin UMC, inda suka kona wani ɓangare, sannan suka bazu zuwa cikin al’umma suka sace akalla mutane biyar, yayin da tsoro ya mamaye mazauna, da dama suka gudun hijira.