Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 33

Kungiyar AES ta yi Allah wadai da harin da aka kai filin jirgin saman Yamai a Jamhuriyar Nijar

0

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta kuma shugaban kasar Burkina Faso kyaften Ibrahim Traoré, ta yi kakkausan suka kan harin da ta danganta da na dabbanci akan kasar ta Nijar da ke memba a kungiyar.

AES ta ce wannan hari wata barazana ce ga tsaron harin gwiwa na kasashen, kwanciyar hankalin yankin da kuma kokarin da suke yi tare na kawo zaman lafiya da ci gaban yankin Sahel.

Kazalika kungiyar ta yi kakkausan suka da gargadi ga duk masu tallafawa ‘yan ta’adda da kudi, makamai, ko da bayanan sirri ko kuma goyan baya a siyasance cewa sai sun amsa alhakin abinda suka aikata.

An sako jagororin adawa a Guinee Bissau bayan kamasu da sojoji suka yi

0

‘Yan adawa da kungiyoyin fararen hula da ECOWAS a kasar Guinée Bissau na nuna farin ciki da sakin manyan ‘yan adawar kasar bayan shafe sama da wata biyu a tsare.

Daga yanzu dai Domingos Simoes Pereira zai ci gaba zama karkashin saka ido yayin da shi kuma Fernando Dias da ya yi ikirarin lashe zaben shugaban kasa ya bar ofishin jakadancin Nijeriya cikin ‘yancin inda a yake samun mafaka a baya .

Sakin ‘yan siyasar ya zo ne sakamakon shiga tsakani da ministan tsaron Sénégal janar Birame Diop wanda shugaba Bassirou Diomaye Faye ya aika a matsayin dan aike na musamman shiga takani.

‘Yan bindiga sun kona coci da Ofishin ’yan sanda, tare da sace mutane a jihar Neja

0

Da safiyar Lahadi, 1 ga Fabrairu, 2026, ’yan bindiga sun kai mummunan hari a karamar hukumar Agwara, ta jihar Neja, inda suka kone Ofishin ’yan Sanda suka kona wani ɓangare na cocin UMC, tare da sace aƙalla mutane biyar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa maharan sun isa garin da misalin 3:40–4:00 na asuba, inda suka yi musayar wuta da jami’an tsaro kafin daga bisani su yi amfani da abubuwan fashewa suka kona ofishin ’yan sanda bayan sun ci karfin jami’an da ke wurin.

Bayan haka, maharan sun nufi cocin UMC, inda suka kona wani ɓangare, sannan suka bazu zuwa cikin al’umma suka sace akalla mutane biyar, yayin da tsoro ya mamaye mazauna, da dama suka gudun hijira.

NNPP ta musanta batun komawar Kwankwaso APC

0

Jam’iyyar NNPP ta musanta rahotannin da ke cewa jagoranta na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yana tattaunawa don sauya sheƙa zuwa APC, tana mai cewa karya ce tsagwaronta ta da aka kirkira domin ruɗar jama’a.

A cewar Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na kasa Ladipo Johnson, babu wata ganawa ko tattaunawa da aka taɓa yi tsakanin Sanata Kwankwaso da Shugaba Tinubu, ko APC game da sauya sheƙa, duk da jita-jitar da ta bazu a wasu wurare.

Rahotannin sun biyo bayan da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauya sheƙa zuwa APC, inda wasu ke danganta hakan da manyan bukatu da ake zargin Kwankwaso ya gabatar a yayin wata tattaunawa da jam’iyyar mai mulki da hakan ya kawo tsaiko game da komawarsa APC.

Muna kalubantar Nijar kan zargin da ya yi mana – Bénin da Côte d’Ivoire

0

Kasashen Bénin da Côte d’Ivoire sun maida martani ga shugaba Tiani na Nijar kan zargin da yi musu na tallafawa ‘yan ta’addar da suka kai hari filin jirgin saman Diori Hamani a Yamai

Kasar Benin ce a baya bayan nan ta yi martanin a game da zargin na Tiani a kan shugaban ta Patrice Talon wanda kakakin gwamnatin kasar Wilfried Léandre Houngbédji ya ce Bénin kasa ce da ke cigaba da jan hankali masu zuba jari da masu ziyara sakamakon karfin tattalin arzikin ta da na ma’aikatun ta, dan haka ya ce kasar ba za ta taba bari ba a ci mutuncinta ba ta hanyar wasu zarge.

Ita ma kasar Côte d’Ivoire ta maida martani a game da zargin Tianin inda ministar harkokin wajen kasar ta kirayi jakadiyar Nijar a kasar domin neman bada bahasi akan kalaman na shugaba Tiani

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar ya zargi shugaban Faransa Emmanuel Macron da Patrice Talon da kuma Alassan Ouattara da tallafawa ma ‘yan ta’addar da suka kai hari filin jirgin saman Diori Hamani a yayin da yake tsokaci a gaban manema labarai lokacin da ya ziyararci inda aka kai hari

Ba ta amfani da jami’an tsaro kaɗai za a samu zaman lafiya ba – Gwamna Uba Sani

0

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya ce dorewar zaman lafiya ba ta taƙaitu ga matakan tsaro kaɗai ba, sai dai ta haɗa da ci gaba, haɗin kai da samar da damar tattalin arziki ga al’umma. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin kaddamar da gidaje, titin kwalta mai tsawon kilomita shida, Cibiyar Lafiya ta Matakin Farko da kuma Cibiyar Koyon Sana’o’i a Tudun Biri, Jihar Kaduna.
A cewar Gwamnan, an zaɓi Tudun Biri a matsayin wurin aiwatar da shirin ne bayan harin bama-baman kuskure da ya kashe fararen hula a watan Disambar 2023.

Ya bayyana cewa umarnin da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar ya haifar da tsarin ci gaba na haɗin gwiwa wanda ya wuce taimakon gaggawa zuwa cikakken sake gina rayuwar al’umma, ta hanyar samar da gidaje na zamani tare da muhimman ababen more rayuwa domin zaman lafiya mai ɗorewa.

Gwamna Uba Sani ya ce Gwamnatin Jihar Kaduna ta taka muhimmiyar rawa tun daga farkon aukuwar lamarin har zuwa kammala ayyukan sake gina Tudun Biri. Ya ƙara da cewa an yi amfani da wasu filayen noma wajen gina gidaje da ababen more rayuwa, inda aka tattauna da manoma da abin ya shafa tare da tallafa musu ta hanyar samar da kayan aikin noma, shirye-shiryen koyon sana’a da hanyoyin dogaro da kai.

Ya ce tun da farko gwamnati ta samar da kulawar gaggawa ta lafiya da tallafin walwala, sannan daga baya aka faɗaɗa mayar da hankali kan lafiya, ilimi, ababen more rayuwa da hanyoyin samun kuɗi, bisa manufar cewa jihar ba za ta amince da kafa sansanonin ‘yan gudun hijira ba.

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta gina Cibiyar Lafiya mai gadaje 25 a Tudun Biri, wadda ke bayar da ire-iren kiwon lafiya guda biyar ciki har da kula da mata masu juna biyu, ƙananan tiyata da kula da cututtukan ido.

Haka kuma an gina titin kwalta mai tsawon kilomita shida da ke haɗa al’ummar da hanyar Filin Jirgin Sama na Kaduna, tare da fifita mazauna Tudun Biri a shirye-shiryen tallafin gwamnati, raba takin zamani, shinkafa da masara, da kuma kafa Cibiyar Koyon Sana’o’i domin matasa. A fannin ilimi kuwa, an gina sabuwar makarantar firamare tare da goyon bayan Rundunar Sojin Najeriya da abokan hulɗar ci gaba.

Rikicin PDP na ƙara zurfafa tsakanin bangaren Wike da Turaki

Tsagin PDP na Tanimu Turaki ya ɗaukaka ƙara kan rushe taron PDP na Ibadan na jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida Alhaji Tanimu Turaki.

Sun yaɗaukaka ƙarar ne kan hukuncin babbar kotun tarayya da ta soke taron jam’iyyar na ƙasa da aka gudanar a Jihar Oyo, a ranar 15 ga Nuwamba, 2025.

Da yake magana da ’yan jarida ranar Juma’a, Shugaban kwamitin gudanarwa na PDP Alhaji Tanimu Turaki ya ce duk da hukuncin kotu, jam’iyyar tana nan daram bisa doka, kuma ba ta girgiza ba, yayin da take jiran hukuncin kotun ɗaukaka Ƙara.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Ibadan, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Uche Agomoh, ta yanke hukuncin soke taron ƙasa na PDP da aka yi a Ibadan, tare da umartar Turaki da sauran mambobin NWC da su daina bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar na ƙasa.

Kotun ta kuma tabbatar da Kwamitin Rikon Ƙwarya ƙarƙashin jagorancin Mohammed Abdulrahman da Samuel Anyanwu a matsayin sahihin NWC har sai an gudanar da ingantaccen taron ƙasa.

Gwamnonin PDP sun mara wa taron Ibadan baya, inda aka zaɓi Turaki da sauran mambobin NWC na wa’adin shekaru huɗu. Sai dai Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, tare da Abdulrahman da Anyanwu, sun nace cewa su ne shugabannin rikon ƙwarya na jam’iyyar, inda suka kafa kwamitin mutum 13 a ranar 8 ga Disamba, 2025, da wa’adin kwanaki 60, duk da cewa an riga an tsara mika mulki daga tsohon shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum, kafin wa’adinsa ya ƙare a ranar 9 ga Disamba.

Sabani tsakanin ɓangarorin biyu ya kai ga ƙin amincewar Hukumar zaɓe mai zaman Kanta ta Ƙasa INEC da kowanne ɓangare, lamarin da ya haddasa shigar da ƙara da dama a kotu yayin da ake shirin tunkarar zaɓen 2027.

Real Madrid za ta kara da Benfica yayin da PSG za ta fafata da Monaco a wasan neman shiga zagaye na 16 na kofin nahiyar Turai

0

An fitar da jadawalin wasannin gurbin shiga zagaye na 16 na gasar UEFA Champions League, inda Real Madrid za ta kara da Benfica, yayin da Paris Saint-Germain za ta fafata da Monaco, bayan kammala fitar kuri’a a birnin Nyon na kasar Switzerland.

Wasannin sun haifar da manyan fafatawa, ciki har da Borussia Dortmund da Atalanta, Galatasaray da Juventus, Atlético Madrid da Club Brugge, Olympiacos da Bayer Leverkusen, yayin da Qarabağ za ta hadu da Newcastle United karon farko a tarihi. Inter Milan kuma za ta buga da Bodø/Glimt ta Norway.

Karawar Benfica da Real Madrid ta kara daukar hankali ne bayan Benfica ta doke Madrid 4–2 a karshen wasannin league phase a ranar 28 ga Janairu 2026, lamarin da ya sa Madrid ta fadi zuwa matakin play-off maimakon shiga zagaye na 16 kai tsaye.

UEFA ta bayyana sabon tsarin gasar a matsayin mai cike da kayatarwa, inda aka ce wasannin sun yi matukar daukar hankali. Za a buga wasannin play-off din ne kafin a tantance kungiyoyin da za su shiga zagaye na 16, yayin da wasan karshe zai gudana a birnin Budapest.

Kotu ta soke babban taron da PDP ta yi a Ibadan tare da hana Turaki da wasu bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar

Kotun Tarayya da ke Ibadan ta soke taron ƙasa na jam’iyyar PDP da aka gudanar a ranar 15 ga Nuwamba 2025 a Ibadan, Jihar Oyo, tare da hana Kabiru Turaki da wasu gabatar da kansu a matsayin shugabannin ƙasa na jam’iyyar.

Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Juma’a, bayan shari’o’in rikicin shugabanci da ke addabar PDP, duk da cewa jam’iyyar ta gudanar da taron zaɓe na kwanaki biyu a filin wasa na Lekan Salami da aka yi wa lakabi da Ibadan2025, inda dubban wakilai da magoya baya suka halarta.

Da yake mayar da martani, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na PDP, Ini Ememobong, ya ce jam’iyyar na jiran hukuncin kotunan ɗaukaka ƙara, inda ta bayyana cewa bangaren Kabiru Turaki na nan daram bisa doka. Ya bukaci mambobi su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa babu dalilin fargaba.

Jam’iyyar ta ce za ta ci gaba da fafutukarta yayin da shari’ar ke gaba a kotunan ɗaukaka ƙara, lamarin da ake sa ran zai yi tasiri kan makomar PDP gabanin manyan harkokin siyasa masu zuwa.

Ba mu damu da batun tsige gwamnan Rivers ba saboda lamarin yana gaban kotu – Gwamna Abdullahi Sule

0

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce gwamnonin jam’iyyar APC ba su cikin fargaba kan yunkurin tsige Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, inda ya jaddada cewa batun yana gaban kotu kuma doka ce ke tafiyar da shi.

Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin hirarsa a shirin Politics Today na tashar Channels Television, inda ya ce ba za a iya tsige gwamna kawai ba tare da bin tanadin doka da ka’ida ba, yana mai cewa gwamnonin APC na sa ido kan lamarin amma ba su ga dalilin firgici ba.

A halin yanzu dai, yunkurin tsige Gwamna Fubara ya tsaya cik bayan Babbar Kotun Jihar Rivers da ke Oyigbo ta dage sauraron shari’ar har sai Kotun Daukaka Kara ta yanke hukunci, yayin da Alkalin Alkalan jihar, Mai shari’a Simeon Amadi, ya ƙi kafa kwamitin bincike bisa umarnin kotu.