Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 31

Jinkirin gyaran Dokar Zabe na iya shafar jadawalin zaben 2027 — INEC

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta ce jinkirin yin gyara ga Dokar Zabe na iya shafar jadawalin gudanar da zaben 2027.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da Kungiyoyin Fararen Hula (CSOs) a ranar Laraba a Abuja.

Ya ce duk da jinkirin amincewa da kudirin gyaran Dokar Zaben da ke gaban Majalisar Tarayya a halin yanzu, hukumar INEC na ci gaba da shirye-shirye domin gudanar da babban zaben 2027.

Ba sai kundin tsarin mulki ya ban dama ba, zan iya bai wa duk wani mai mulki shawara – Sarki Sunusi II

Sarkin Kano, Alhaji na 15 Muhammadu Sanusi II, ya ce ba sai kundin tsarin mulki ya ba shi dama kafin ya ba Shugaban kasa ko Gwamna shawara kan muhimman al’amuran da suka shafi ƙasa ba, yana mai jaddada muhimmancin sarakuna wajen gina ƙasa da kyakkyawan shugabanci.

Sarkin ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels Television a ranar Laraba, 4 ga Fabrairu, 2026.

Ya ce ikon ba da shawara yana fitowa ne daga matsayin da yake da shi a matsayin jagoran al’umma, ba wai dole sai doka ta bashi damar ba.

Sarkin ya nanata buƙatar shigar mata a siyasa da harkokin mulki, yana cewa hakan zai ƙara inganta shugabanci da haɗin kai.

’Yan sanda sun dakile yunkurin kai hari a Zamfara, tare da kama masu bai wa ’yan bindiga bayanai

0

Rundunar ’yan sandan jihar Zamfara sun dakile wani yunkurin kai hari da ’yan bindiga suka yi kan titin Gusau–Talata Mafara, inda aka jikkata jami’inta guda ɗaya yayin musayar wuta.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa tawagar ’yan sanda karkashin jagorancin DSP Ma’aji Ndagunu na dawowa ne daga Gusau, a lokacin da ‘yan bindigar suka yi musu kwanton bauna a kauyen Kwanar Kirya.

’Yan sandan sun mayar da martani, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa zuwa dazuka, ana zargin wasu sun jikkata da harsasai.

A yayin artabun, Insp. Jamilu Abdullahi ya samu rauni a cinyarsa ta dama, inda aka garzaya da shi Asibitin Talata Mafara domin jinya.

Ba gudu ba ja da baya kan gyare gyaren tattalin arziki a Nijeriya – Shugaba Tinubu

0

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ba gudu babu ja da baya kan gyare-gyaren tattalin arziƙi, duk da radadin da aka fuskanta a farkon aiwatar da su, yana mai jaddada aniyar ci gaba da aiwatar da wadannan manufofi.

Jaridar Punch ta raiwato Tinubu na bayyana hakan ne a ranar Talata, 4 ga Fabrairu, 2026, lokacin da ya karɓi tawagar Bankin Duniya karkashin jagorancin Anna Bjerde.

A cewarsa, gyare gyaren ciki har da cire tallafin man fetur da gyara farashin canjin kuɗaɗe sun kasance masu wahala da farko, amma sun zama dole domin ƙarfafa tattalin arziƙin Nijeriya, musamman don ƙirƙirar dama ga matasa masu tasowa a kasar.

Trump ya cancanta a bashi lambar yabo ta zaman lafiya ta duniya – FIFA

0

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Gianni Infantino, ya kare matakin da ya dauka na bai wa Shugaban Amurka, Donald Trump, lambar yabo ta FIFA Peace Prize da yayi a kwanakin baya, duk da sukar da ya sha wajen mutane a sassa daban-daban na duniya.

Infantino ya yi wannan bayani ne a wata hira da jaridar Sky News a ranar Litinin, bayan ya sha suka saboda bai wa Trump lambar yabo a yayin bikin fidda jadawalin gasar kofin duniya ta 2026 da aka gudanar a Washington DC a watan Disamba.

Shugaban FIFA ya ce a ganinsa, Trump ya cancanci lambar yabon, yana mai cewa duk wani abu da zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a duniya ya dace a ƙarfafa shi.

Ya bayyana cewa FIFA ta dade tana tunanin samar da wata lambar yabo domin karrama mutanen da ke bayar da gudunmawa ga zaman lafiya a duniya.

Gwamnoni na shan suka na rashin taɓuka abin a zo a gani duk da karɓar Tiriliyan 9 daga asusun FAAC a 2025

Duk da samun kimanin Naira tiriliyan 9 daga rabon hukumar rarraba kudaden shiga na tarayya (FAAC) a shekarar 2025, gwamnonin jihohi na fuskantar suka daga ƙungiyoyin ƙwadago, ƙungiyoyin fararen hula da jam’iyyun adawa, bisa zargin cewa akwai tazara mai faɗi tsakanin karuwar kudaden shiga da ƙarancin ayyukan jin daɗin jama’a.

Bincike kan bayanan rarraba kudaden Asusun Tarayya da Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ta wallafa, wanda jaridar The PUNCH ta tattara, ya nuna cewa rabon FAAC ga jihohi ya ƙaru da sama da N2tn cikin shekara guda.

Wannan ya jawo suka daga ƙungiyoyin ƙwadago da jam’iyyun adawa.

Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi gargaɗin cewa, duk da ƙarin kudaden da jihohi ke samu, ba a ga canji mai ma’ana a rayuwar jama’a ba, tana danganta hakan da raunin shugabanci, fifiko marar dacewa, da cin hanci da rashawa a matakin jihohi.

Amurka za ta kori ’yan Nijeriya 79 da suka aikata manyan laifuka

Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka ta bayyana cewa za ta kori ’yan Nijeriya ba ƙasa da 79 da aka yanke wa hukunci bisa aikata laifuka a ƙasar.

Binciken jaridar PUNCH a shafin yanar gizon DHS a ranar Litinin ya nuna cewa ’yan Nijeriyan 79 din sun samu hukunci ne kan laifuka da suka haɗa da zamba, fataucin miyagun ƙwayoyi, duka da raunatawa, kisan kai da fashi, da sauransu.

Wata sanarwa ta nuna cewa an kama mutanen ne a cikin yakin da Amurka ke yi na kama ’yan ƙasashen waje masu aikata laifuka, kafin a shirya korarsu daga ƙasar.

Gwamnatin Tinubu za ta horas da ’yan Nijeriya miliyan 10 kan hada-hadar kudi

0

Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da shirin horas da ’yan Nijeriya miliyan 10 kyauta a fannin ilimin hada-hadar kudi da shigar da kowa cikin tattalin arziki, inda ta ce mayar da hankali kan matasa da mata shi ne mabuɗin cin gajiyar yawan al’ummar kasar.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayyana hakan ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja, yana mai cewa Nijeriya ba za ta iya gina tattalin arziki mai karfi ba sai an gina kwarewa, gaskiya da basirar zamani.

A cikin sanarwar da Stanley Nkwocha, hadimi kan yada labarai na Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, ya fitar, ta ce an rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimta (MoU) tsakanin Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa da kungiyoyin kwararru guda shida, domin tsara horaswa, takardun shaidar kwarewa, da bunkasa basirar zamani ga ’yan kasa, musamman matasa da mata.

Sanarwar ta kara da cewa shirin, wanda ake aiwatarwa karkashin Kwamitin Shugaban Kasa kan Hada-hadar Kudi da Shigar da Kowa (PreCEFI), zai bai wa mahalarta ilimin zuba jari, sarrafa kasuwanci da amfani da fasahar zamani yadda ya kamata.

Bincike ya nuna manoma a Nijeriya sun tafka asarar kusan Naira tiriliyan 5 a cikin watanni 24 da suka gabata

0

Wannan asara ta samu be sakamakon wasu manufofin gwamnati da suka haddasa faduwar farashin kayayyaki, sai kuma dogaro da hasashen yanayi daga hukumar kula yanayi ta Nijeriya NIMET da dai sauran su.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kungiyar Foundation for Peace Professionals ta fitar, inda ta bayyana cewa fannin noma a Nijeriya na fuskantar babbar matsalar da ke barazana ga samar da abinci.

Daraktan Abdulrazaq Hamzat, ya ce asarar da aka kiyasta na nufin manoma da dama sun rasa jarinsu a wannan yanayi da gwamnati ta shigo da sabbin tsaruka da suka karya kayayyakin da ake nomawa a cikin gida.

Kofa a bude take ga Rabi’u Musa Kwankwaso – Jam’iyyar APC

0

Jam’iyyar APC ta ce har yanzu kofarta a buɗe take ga jagoran NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, idan har ya yanke shawarar shiga cikinta.

Shugaban Jam’iyyar na Nijeriya Farfesa Nentawe Yilwatda ne ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Trust a ranar Lahadi, a daidai lokacin da ake ci gaba da rade radin sauya sheƙar Kwankwaso.

Farfesa Yilwatda ya ce ko da yake ba a fara wata tattaunawa kai tsaye da Kwankwaso ba a halin yanzu, APC za ta karɓe shi hannu bibbiyu idan ya zaɓi shigowa jam’iyyar.