Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 39

Atiku ba zai iya kayar da Tinubu ba a zaben 2027 – Hannatu Musa Musawa

0

Ministar Al’adu, Fasaha da Kirkira, Hannatu Musawa, ta ce tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ba zai iya doke Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 ba, ko da ya haɗu da Peter Obi a tikitin zaɓe ɗaya. Ta bayyana hakan ne a wata hira da aka wallafa a shafin Instagram na TheMicon Podcast.

Musawa ta ce duk da cewa Atiku mutum ne mai ƙarfi a siyasa, ba ta ganin zai iya kayar da jam’iyya mai mulki. Ta ƙara da cewa haɗin Atiku da Peter Obi zai janyo rarrabuwar kai a cikin magoya bayan Obi, inda da dama ba za su amince Obi ya tsaya matsayin mataimaki ba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ta kuma yi gargaɗin cewa idan har Peter Obi ne zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa a irin wannan haɗin gwiwa, hakan zai ƙara raunana damar adawa. Kalaman nata sun haifar da muhawara a kafafen sada zumunta yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

‘Yan sanda sun kama sabuwar amarya kan zargin ajalin mijinta da guba a jihar Jigawa

0

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wani sabon ango a ƙauyen Gauza da ke ƙaramar hukumar Jahun, bayan da ake zargin ya rasu ne sakamakon cin abincin da amaryarsa ta dafa masa wanda aka saka masa guba.

Lamarin ya faru ne a ranar 23 ga Janairu, 2026, inda bayan cin abincin rana, ango ya kamu da rashin lafiya mai tsanani kuma aka garzaya da shi asibiti, inda daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.

Binciken farko ya nuna cewa ‘yan sanda sun kama matar marigayin a matsayin babbar wadda ake zargi, bayan da ta amsa laifin zuba gubar bera a cikin abincin mijinta. Ta kuma bayyana cewa ta tura ‘yar uwarta domin sayo gubar, tare da cewa an tilasta mata auren ne daga iyayenta, abin da ta ce ya janyo aikata wannan mummunan lamari.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar ya bayar da umarnin mika lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) a Dutse domin zurfafa bincike, kafin gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu.

Rundunar ta bukaci al’umma su guji daukar doka a hannunsu, tare da amfani da hanyoyin doka wajen warware matsalolin aure da na iyali, tana kuma tabbatar da jajircewarta wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.

Kasar Australia ta soke lasisin aikin wata ma’aikaciyar jinya ‘yar Nijeriya saboda an same ta tana bacci a bakin aiki

0

Hukumar shari’a a Australia ta soke lasisin aikin jinya na wata ‘yar asalin Nijeriya, Chimzuruoke Okembunachi, bayan an same ta da laifin yin barci sau da dama a bakin aiki yayin aikin dare a wata cibiyar kula da tsofaffi, lamarin da ya jefa lafiyar marasa lafiya cikin hatsari.

Rahoton Daily Mail ya ce kotun NSW Civil and Administrative Tribunal ta yanke hukunci a ranar 20 ga Janairu, 2026, cewa abin da Okembunachi ta aikata a watan Maris 2024 ya kai matsayin laifin saba dokar kwarewar aiki, wanda ya sa aka cire sunanta daga rajistar ma’aikatan jinya.

Okembunachi, mai shekaru 25, ta fara aiki a Hardi Aged Care da ke Guildford a Yammacin Sydney a watan Fabrairu 2024. Kasa da wata guda bayan haka aka dakatar da ita, daga bisani kuma ta yi murabus. A zaman kotu, an bayyana cewa tsakanin 13 zuwa 27 ga Maris, ita ce kaɗai babbar ma’aikaciyar jinya a aikin dare, tana kula da mataimakan jinya uku ko hudu da kuma kusan tsofaffi 100.

An tabbatar da cewa a akalla darare shida ta kasa gudanar da aikinta saboda barci, yayin da marasa lafiya uku suka rasa shan magungunan morphine a kan lokaci. A wani lokaci, an ce ta umarci wata mataimakiyar jinya da ba ta da izini ta ba mara lafiya Panadol.

Kotun ta ce duk da ta nuna nadama, abin da ta aikata na da barazanar jefa rayukan marasa lafiya cikin hatsari, don haka dole ne a soke lasisinta. An hana ta neman sake dubawa na tsawon akalla watanni tara. Duk da haka, tana ci gaba da karatun likitanci a Jami’ar Western Sydney, tana samun tallafi daga mahaifinta da kuma taimakon dalibai na Centrelink.

Idan Gwamna Abba ya koma APC, shi ne mutum na farko da za mu fara yankar wa katin jam’iyyar – APC a jihar Kano

0

Jam’iyyar APC a jihar Kano ta bayyana cewa tana maraba da Gwamna Abba Kabir Yusuf bayan ficewarsa daga NNPP, tana mai nuna fatan zai sanar da shigarsa jam’iyyar nan ba da jimawa ba. Sakataren APC na jihar, Ibrahim Zakari Sarina, ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyi kan matakin da gwamnan zai ɗauka na gaba.

Sarina ya ce kodayake gwamnan bai sanar da shigarsa APC a hukumance ba, jam’iyyar na sa ran hakan zai faru, inda ya jaddada cewa ƙofofin APC a buɗe suke gare shi da magoya bayansa. Ya ƙara da cewa wannan ci gaban na ƙara ƙarfi ga jam’iyyar, ganin yadda ake tsammanin gwamnan zai zo tare da zaɓaɓɓun jami’ai da masu riƙe da muƙamai.

Ya kuma bayyana cewa APC ta riga ta ɗauki matakai na musamman domin karɓar gwamnan, inda ta tanadi lambar rajistar e-registration ta musamman mai lamba 001 a mazabarsa ta Chiranci-Diso. A cewarsa, shirin karɓar ba gwamnan kaɗai ya shafa ba, har da mambobin majalisarsa, masu goyon bayansa da dukkan abokan tafiyarsa na siyasa.

Dole ne Nijeriya ta daina shigo da abubuwan da za ta iya samarwa – Gwamnatin Nijeriya

0

Karamin Ministan Harkokin Masana’antu, Sanata John Owan, ya ce Nijeriya dole ta rage dogaro da shigo da kaya daga waje tare da mayar da jama’a cikin ayyukan samarwa. Ya ce yawan jama’a kaɗai ba ya kawo bunƙasar tattalin arziki sai an samar da ayyukan yi.

Owan ya bayyana haka ne a taron tattalin arziki na RCCG a Legas, inda ya ce nasarar manufar Nigeria-First da Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar a 2025 za ta dogara da tsayayyen tsari da amfani da sayen kayan gwamnati wajen ƙarfafa masana’antun cikin gida.

Ministan ya jaddada cewa idan ba a faɗaɗa masana’antu ba, yawan matasan Nijeriya na iya zama barazana. Ya ce haɗa manufofin gwamnati da gyaran tsarin sayayya zai rage shigo da kaya, ya ƙarfafa masana’antu, tare da samar da ayyukan yi masu ɗorewa.

‘Yan Nijeriya sama da dubu 13 da suka makale aka dawo da su gida daga kasashen waje a cikin shekaru 3 – Rahoton jaridar Punch

0

Akalla ‘yan Nijeriya 13,635 da suka makale a kasashen waje aka dawo da su gida daga kasashe 10 cikin shekaru uku da suka gabata, kamar yadda bayanai daga Hukumar IOM, NEMA da NiDCOM suka nuna.

An dawo da mutanen ne daga Libya, Sudan, Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Ghana, Jamhuriyar Nijar, Aljeriya, Chadi, Côte d’Ivoire da Mali.

A shekarar 2025 kadai, an dawo da ‘yan Nijeriya 3,358 daga kasashe biyar, inda aka fi dawo da su daga Libya (1,773) da Jamhuriyar Nijar (1,188). A 2024 kuma, an kwaso mutane 4,261 daga kasashe bakwai, ciki har da Libya, Nijar, Chadi, Mali da UAE, yayin da a 2023 aka dawo da 5,753 galibi daga Sudan, Libya da Nijar.

Gwamnatin Nijeriya ta sake gargadin matasa da su guji yin hijira ba bisa ka’ida ba, musamman bin tayin ayyukan bogi a kasashen waje. Ma’aikatar Harkokin Waje da Ma’aikatar Matasa sun ce hijira bisa doka tana da amfani, amma wadda ba ta bi ka’ida ba na jefa rayuka cikin hadari tare da illata ci gaban kasa.

Muna maraba da Gwamna Abba a APC kuma za mu warware batun tikitin takara na ba hamayya kafin zabe – Abdullahi Abbas

0

Shugaban jam’iyyar APC a Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas Sanusi, ya ce jam’iyyar na maraba da murabus din Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP da kuma shirin shigarsa APC, yana mai cewa siyasa wasa ne na adadi, kuma kowane kari yana ƙara wa jam’iyya ƙarfi a zaɓe. Ya bayyana hakan ne a wata hira, inda ya jaddada cewa APC a shirye take ta karɓi duk wanda ya ga alherin jam’iyyar ya yanke shawarar shigowa.

Dangane da rade-radin tikitin kai-tsaye ga gwamnan, Abbas Sanusi ya ce ba batun da jam’iyyar ke duba a yanzu ba ne. Ya bayyana cewa Gwamna Yusuf ba shi kaɗai zai shigo APC ba, akwai shugabannin ƙananan hukumomi, kansiloli da sauran masu riƙe da muƙamai da za su biyo shi. Ya ce bayan kammala dukkan matakan sauya sheƙa ne jam’iyyar za ta zauna ta tsara yadda za a tafiyar da al’amura domin cin nasara a zaɓen 2027, tare da guje wa rikici tsakanin tsofaffin mambobi da sababbi.

Kan jinkirin shigowar gwamnan, shugaban APC na Kano ya ce duk labaran da ake yadawa tun baya jita-jita ne kawai, domin sauya sheƙar gwamna na buƙatar manyan shawarwari da bin tsari. Ya shawarci mambobin APC da masu shigowa su fifita nasarar jam’iyya, tare da zaman lafiya da haɗin kai, yana mai cewa iko daga Allah yake, kuma APC na da kudirin gyara kura-kuran da ke addabar ƙasa domin ‘yan Nijeriya su samu sauƙi.

Ba zan cefanar da akidar siyasata kan wata bukatar kashin kai ba – Dr Rab’iu Musa Kwankwaso

0

Madugun darikar Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ba zai taba yin sulhu da akidunsa domin wata riba ta kansa ba, yana mai jaddada cewa gwagwarmayarsa ta siyasa ta dade tana wakiltar talakawan Nijeriya.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a Kano ranar Juma’a, jim kadan bayan Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da wasu shugabanni, sun fice daga NNPP.

Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a gidansa da ke Kano, inda ya ce tafiyar Kwankwasiyya ta ginu ne kan akida da manufa, ba kan kudi ko anfani na kai ba. Ya ce da a ce neman riba ce manufarsa, da tuni ya dauki wata hanya mai sauki ya bar tafiyar, amma ya tsaya tsayin daka saboda kishin talakawa da adalci.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya kuma bukaci magoya bayansa da su fara shiri tun yanzu domin zaben 2027, yana mai gargadin cewa akwai wasu da ke kokarin rusa abin da aka gina tsawon lokaci a Kano.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, madugun ya jaddada cewa ba zai ja da baya ba wajen kare muradun jama’a, yana mai cewa burinsa shi ne yakar duk wani tsari da ke danniya ko zaluntar talakawa.

Babban layin lantarki na ‘National Grid’ ya fadi a Nijeriya

0

Babban layin wutar lantarki na ƙasa ya sake faɗuwa a Juma’ar nan, lamarin da ya jefa sassa da dama na Nijeriya cikin duhu.

Jaridar Punch ta rawaito cewa adadin wutar da ake samarwa ya sauka daga megawatt 4,500 zuwa megawatt 24.

Rahotanni sun ce dukkan tashoshin samar da wutar lantarki 23 da ke haɗe da grid ɗin ba sa iya bayar da wuta a yayin faruwar lamarin.

An yi ajalin magoya bayan ‘yan adawa 30, tare da kama mutum 2,000 bayan zaɓen Uganda – Babban hafsan sojin kasar

0

Babban hafsan sojin Uganda, wanda ɗan Shugaba Yoweri Museveni ne da aka sake zaɓa, ya bayyana cewa mutane 30 daga magoya bayan ‘yan adawa sun mutu, yayin da sama da mutum 2,000 aka kama, biyo bayan zaɓen ƙasar.

Shugaban sojin, Muhoozi Kainerugaba, ya bayyana hakan ne a ranar Jumma’a, bayan zaɓen da aka gudanar a 15 ga Janairu.

Jaridar Punch ta rawaito cewa a halin yanzu, jagoran ‘yan adawa Bobi Wine na ɓoye, bayan da ya zargi jami’an tsaro da kai hari gidansa bayan kammala zaɓen,bayan ya bayyana kin amincewarsa da sakamakon zaben.