Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 40

Fubara ne jagoran APC a jihar Rivers, ba Wike ba — Daniel Bwala

0

Mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin yada labarai Daniel Bwala, ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara shi ne jagoran jam’iyyar APC a jihar Rivers, yana mai jaddada cewa tsohon gwamna Nyesom Wike ba ɗan APC ba ne.

Bwala ya bayyana hakan ne a gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, yayin da ake fama da rikicin siyasa a Rivers, wanda ya kai ga Majalisar Dokokin jihar ta fara yunkurin tsige Gwamna Fubara.

Ya ce matsayin shugaban APC a bayyane yake cewa Fubara ne jagoran APC a Rivers, ba Wike ba, Wike ba memba ne na APC ba, don haka ba shi da ikon magana a madadin APC.

An fara shari’ar magoya bayan Senegal 18 da ake zargi da tayar da hargitsi a wasan ƙarshe na AFCON

0

An fara shari’ar magoya bayan Senegal 18 da ake zargi da tayar da hargitsi a lokacin wasan ƙarshe na gasar AFCON 2025 da Senegal ta doke Moroko da ci 1–0 a wata kotun Moroko, kamar yadda lauyoyin da ke kare su suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Lamarin ya faru ne a Rabat, inda aka gudanar da wasan ƙarshe, bayan samun hargitsi a filin wasan.

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 29 ga Janairu, domin bai wa ɓangarorin sharya wa, ance magoya bayan na ci gaba da kasancewa a tsare kafin shari’ar yayin da ake ci gaba da bincike kan abin da ya faru a ranar wasan.

Na yi kokarin kare ‘yan wasana ne daga zalunci a wasan karshe na AFCON – Pepe Thiaw

0

Kocin kasar Senegal, Pape Bouna Thiaw, ya ce zafin zuciya ne ya sa ya umarci ’yan wasansa su fice daga fili a wasan ƙarshe na kofin nahiyar Afirka AFCON da aka fafata da Moroko.

Thiaw ya bayyana hakan ne a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, kamar yadda Premium Times ta ruwaito, bayan cece-kucen da ya biyo bayan hukuncin bugun fenariti da aka bai wa Moroko sakamakon duba VAR a ƙarshen wasan.

Lamarin ya faru ne lokacin da Senegal ta nuna rashin amincewa da hukuncin alkalin wasa, lamarin da ya sa ’yan wasan suka fice daga fili na ɗan lokaci kafin daga bisani su dawo su kammala wasan.

Kotun kolin Nijeriya ta yi watsi da karar da ake zargin Manjo Al Mustapha da hannu wajen halaka matar Abiola

0

Kotun Kolin Nijeriya ta yi watsi da shari’ar da aka shigar da Manjo Hamza Al Mustapha, kan zarginsa da hannu wajen halaka Kudirat Abiola, matar marigayi Cif MKO Abiola.

Gidan talabijin na NTA ya bayyana cewa rahoton shari’ar ya nuna kwamitin alkalai biyar na kotun kolin karkashin jagorancin mai Shari’a Uwani Aba-Aji, ta yanke hukunci a kan shari’ar da Gwamnatin jihar Legas ta shigar tun da fari.

Kotun ta ce Gwamnatin jihar Legas ta nuna rashin kulawa kan shari’ar da aka dauki shekara da shekaru ana gudanar da ita.

Kotun Koli ta kuma nuna takaicinta kan yadda Gwamnatin Legas ta kasa tura wakilci ko lauyanta, duk da cewa an aika mata da sanarwar zaman shari’a tun shekarar 2020, kuma ba a gabatar da wani bayani ga kotu ko bangaren da ake kara ba, saboda haka, kotun ta yanke hukuncin korar shari’ar gaba daya.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea Bissau sun saka ƙarshen shekarar 2026 don gudanar da zaɓe a ƙasar

0

Sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea-Bissau sun ce za a gudanar shugaban ƙasa a ranar 6 ga Disambar 2026, bayan da suka kifar da tsohon shugaban ƙasar, Umaro Sissoco Embalo, a ƙarshen 2025.

Kafar yada labarai ta Al Jazeera ta rawaito cewa shugaban mulkin sojin ƙasar, Manjo-Janar Horta Inta-a, ya sanar da hakan ne a wata doka da aka sanar a ranar Laraba, inda ya ce an cika dukkan sharuddan gudanar da zaɓen cikin ‘yanci, adalci da gaskiya.

Rahoton ya bayyana cewa juyin mulkin da ya faru a watan Nuwamba ya kawar da Embalo, tare da naɗa Horta Inta-a don jagorantar gwamnatin na tsawon shekara guda.

Majalisar dattawan Burtaniya ta amince da dokar hana matasa ƴan ƙasa da 16 amfani da shafukan sada zumunta

0

Majalisar dattawan Birtaniya ta amince da wani kudiri da ke neman haramta amfani da kafofin sada zumunta ga yara ‘yan ƙasa da shekaru 16, bayan an kada kuri’ar goyon baya tsakanin mambobin majalisar.

Rahoton BBC ya bayyana cewa gyaran dokar ya samu goyon bayan ‘yan majalisar daga jam’iyyun Conservative, Liberal Democrat da Crossbench, yayin da gwamnati ta ce za ta gudanar da nata shawarar jin ra’ayoyin jama’a kan yiwuwar haramcin.

A karkashin dokar, gwamnati za ta tilasta wa kamfanonin sada zumunta samar da hanyoyin tantance shekarun mutum kafin ya fara amfani da kafafensu.

Sanata Adams Oshiomhole ya buƙaci gwamnatin Tinubu ta garƙame duk wanda ya ƙi biyan haraji

0

Sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea-Bissau sun ce za a gudanar shugaban ƙasa a ranar 6 ga Disambar 2026, bayan da suka kifar da tsohon shugaban ƙasar, Umaro Sissoco Embalo, a ƙarshen 2025.

Kafar yada labarai ta Al Jazeera ta rawaito cewa shugaban mulkin sojin ƙasar, Manjo-Janar Horta Inta-a, ya sanar da hakan ne a wata doka da aka sanar a ranar Laraba, inda ya ce an cika dukkan sharuddan gudanar da zaɓen cikin ‘yanci, adalci da gaskiya.

Rahoton ya bayyana cewa juyin mulkin da ya faru a watan Nuwamba ya kawar da Embalo, tare da naɗa Horta Inta-a don jagorantar gwamnatin na tsawon shekara guda.

‘Yan APC kawai jam’iyyar za ta ba mukamai bayan zaben 2027 – Nentawe Yilwatda

0

Shugaban jam’iyyar APC na Nijeriya Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa ba za su bai wa duk wanda ba dan jam’iyya mukami ba bayan zaben 2027.

Farfesa Nentawe ya fadi haka ne a Abuja, inda ya jaddada cewa wajibi ne kowane mai mukami ya zama mai biyayya ko kuma aiki da jam’iyyar da ta ba shi matsayin.

A cewar sa, babu maganar bai wa kwararru ko wasu masana mukamai a jam’iyyar, yana mai dogaro da cewa a bisa tsarin siyasa ake tafiya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

‘Yan Nijeriya sun sha fetur din N1.58trn a bukuwan Kirsimeti – Punch

0

Wani rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya sun sha fetur din Naira tiriliyan 1.58 a bukuwan Kirsimeti.

Kamar yadda bayanai daga hukumar kula da albarkatun man fetur ta Nijeriya suka nuna, a kowace rana cikin watan Disambar 2025, ana amfani man fetur da ya haura lita miliyan 63 a kasar, wanda hakan ya sanya aka sha lita biliyan 1.97 cikin kwanaki 31.

Kamar yadda masana suka yi hasashe, yawan shan man fetur a karshen shekara na da nasaba da bukukuwa, baya ga tafiye-tafiye don kai ziyara wurare da kuma karuwar bukatar amfani da shi.

‘Yan bindigar da suka sace Kiristoci 166 a Kaduna sun nemi kafin alkalamin N29m

0

Barayin dajin da suka sace Kiristoci 166 a jihar Kaduna sun nemi N29m matsayin ‘kafin-alkalami’ kafin su fadi adadin kudin fansar da za a biya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a ranar Lahadi 18 ga watan Janairun 2026, ‘yan bindiga sun kutsa cikin majami’u uku a yankin Kurmi Wali da ke kudancin Kaduna tare da sace masu ibadar.

Tun da fari dai gwamnatin jihar Kaduna ta musanta batun, kafin daga bisani ta tabbatar da faruwar lamarin.

A halin yanzu al’ummar yankin da aka sace mutanen sun tsinci kawunan su cikin firgici, inda da dama suka tsere daga muhallansu tare da dakatar da sauran harkoki, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.