Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 38

Sojin Amurka sun bayyana ƙara tallafi don inganta tsaron Nijeriya

0

Rundunar sojin Amurka ta ce ta na ƙara tura kayan aikin soja tare da faɗaɗa raba bayanan sirri da Nijeriya, a wani ɓangare na ƙoƙarin Amurka na ƙara haɗin gwiwa da rundunonin sojin Afirka domin fatattakar ’yan bindigar da ke addabar nahiyar.

 

Mataimakin kwamandan rundunar sojin Amurka a Afirka, Laftanar Janar John Brennan, wanda ya bayyana hakan yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ƙara da cewa Ma’aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) ta ci gaba da buɗe hanyoyin sadarwa da rundunonin soji a ƙasashen Sahel da ke ƙarƙashin mulkin soja, ciki har da Burkina Faso, Nijar da Mali, duk da sauye-sauyen siyasa da suka faru a yankin.

 

Wannan ya zo ne bayan harin da Amurka ta kaddamar a Nijeriya kan ‘yan ta’adda, lamarin da ya haifar da cece-kuce, duk da cewa gwamnatin Nijeriya ta kare matakin da cewa akwai sahalewar ta, kana kuma ta bayar da bayanan sirri ga Amurkan kafin kaddamar da harin.

Ba mu goyon bayan gwamnati ta rarraba mitocin lantarki kyauta – DisCos

0

Kamfanonin rarraba lantarki a Nijeriya sun nuna shakku kan umarnin da Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya bayar na cewa na’urorin auna wuta na prepaid (meters) su zama kyauta ga dukkan rukunin masu amfani da lantarki a Nijeriya.

 

Masu gudanar da kamfanonin, da suka yi magana da jaridar Punch ba tare da bayyana sunayensu ba saboda sarkakiyar batun, sun ce ministan ya yi furuci na siyasa kawai, ba tare da la’akari da ra’ayoyin sauran masu ruwa da tsaki ba — musamman kamfanonin samar da na’urorin auna lantarkin.

 

A ranar Alhamis da ta gabata ne dai gwamnatin Nijeriya ta haramta wa ma’aikatan wutar lantarki karbar kudade daga hannun ‘yan kasa domin sanya musu mitoci, lamarin da ta ce duk wanda aka samu ya karya doka zai fuskanci hukunci.

Sojoji sun mika wa Tinubu rahoton binciken zargin yunkurin juyin mulki

Rundunar sojin Nijeriya ta mika wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu rahoton binciken da ta gudanar kan abin da ta bayyana a matsayin rashin ladabi da karya dokokin aikin soja da wasu jami’an soja 16 da ke tsare suka aikata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyoyi masu ƙarfi daga ɓangaren tsaro da Fadar Shugaban Ƙasa sun tabbatar wa da jaridar cewa an miƙa rahoton ga shugaban ƙasar ne bayan fiye da watanni biyu na tsanantaccen bincike da tambayoyi, wanda Hukumar Leken Asirin Soja ta Ƙasa (Defence Intelligence Agency – DIA) ta gudanar. Rahotanni a baya sun danganta jami’an da ake tsare da zargin hannu a wani yunƙurin juyin mulki.

Wani rahoto da Sahara Reporters ta wallafa a watan Oktoban shekarar da ta gabata ya bayyana cewa an kama tare da tsare wasu jami’an soja, daga matakin Kyaftin har zuwa Birgediya Janar, a hannun Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (DIA), bisa zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

A wancan lokaci, Hedikwatar Tsaro ta kasa (Defence Headquarters) da kuma Fadar Shugaban Ƙasa sun musanta cewa an yi yunƙurin juyin mulki, duk da rahotanni da dama da suka danganta lamarin da soke bikin faretin Ranar Ƴancin Kai ta 1 ga Oktoba da Shugaba Tinubu ya yi.

Da take magana da jaridar Daily Trust, wata majiya da ke da masaniya kan binciken ta ce tuni an miƙa rahoton ga shugaban ƙasa. Majiyar ta ƙara da cewa matakin da shugaban ƙasa zai ɗauka kan rahoton ne zai buɗe ƙofofin ɗaukar ƙarin matakai na gaba.

Gwamnan Kano, Abba Kabir zai koma jam’iyyar APC a ranar Litinin – Sanusi Bature Dawakin Tofa

0

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, zai koma jam’iyyar APC a hukumance ranar Litinin, 26 ga Janairu 2026, bayan murabus dinsa daga NNPP da ya sanar a ranar Juma’a, kamar yadda mai magana da yawunsa Sunusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana.

Sanarwar ta ce Gwamna Yusuf ya taba shiga APC tun 2014, inda ya lashe zaben fitar da gwani na Sanatan Kano ta Tsakiya kafin daga bisani ya janye wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Ta kara da cewa dawowarsa APC ta biyo bayan bukatar karfafa shugabanci, hadin kan kasa da kuma ci gaban Kano ta hanyar dandali mai tsari.

A ranar Litinin, Gwamna Yusuf zai yi rijista da APC tare da ’yan Majalisar Dokokin Jiha 22, ’yan Majalisar Wakilai 8 da shugabannin kananan hukumomi 44, tare da kaddamar da rijistar e-registration ta APC a jihar Kano.

‘Yan sanda sun hallaka ‘yan bindiga 3 tare da ceto wasu a wasu kauyukan iyakokin jihar Gombe

0

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe ta tabbatar da hallaka wasu ‘yan bindiga uku tare da kwato makamai da harsasai, sannan ta ceto wasu daga cikin mutanen da aka sace a wani samame da aka gudanar a yankunan kan iyakar jihar.

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce jami’an tsaro sun dakile yunkurin hari a yankunan Pindiga, Billiri da Shongom ranar Juma’a, amma ‘yan bindigar sun kai hari Garin Galadima da ke yankin Lambo da misalin karfe 3 na asubahin Asabar, inda suka yi ajalin mutum daya tare da sace biyar.

Ya ce biyo bayan farmakin, ‘yan sanda da mafarauta sun fafata da ‘yan bindigar, lamarin da ya yi sanadin hallak uku lahira daga cikinsu, kwato bindigogin AK-47 guda biyu, harsasai 120, babura hudu, da kuma ceto mutane uku, yayin da rundunar ta ce tana ci gaba da farautar sauran da suka tsere.

Gwamnatin jihar Lagos za ta fara cire harajin da ba a biya ba kai tsaye daga asusun bankunan wadanda ake bi

0

Hukumar tattara haraji ta Jihar Legas (LIRS) ta sanar da cewa za ta fara amfani da ikon doka wajen karɓar harajin da ba a biya ba ta hannun bankuna, ma’aikata, masu haya da abokan kasuwanci na masu biyan haraji.

LIRS ta ce dokar Haraji ta Ƙasa ta 2025 ta ba ta damar umartar duk wanda ke riƙe da kuɗin mai bashi ko ke binsa kuɗi, ya tura kuɗin kai tsaye domin biyan bashin haraji.

Hukumar ta bayyana cewa wannan mataki ya shafi harajin mutum ɗaya, harajin ribar kadarori, stamp duty da wasu, tana mai gargaɗin jama’a su biya harajinsu domin kauce wa wannan tsari.

Kwamishina a gwamnatin Abba a Kano ya ajiye mukaminsa

0

Kwamishinan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire na Jihar Kano, Yusuf Ibrahim Kofarmata, ya yi murabus daga mukaminsa nan take, yana danganta matakin da yanayin rikicin siyasa da ke gudana a jihar.

A cikin wasikar murabus dinsa, Kofarmata ya ce yanayin siyasar da ke cike da matsin lamba da tsammanin biyayya na iya kawo shakku kan ‘yancin yanke hukunci da tsarkin aikinsa a matsayin kwamishina, abin da ya ce bai dace da ka’idojin aiki na gwamnati ba.

Ya ce ya dauki matakin ne domin kare martabar mukamin da kuma amincewar jama’a, inda ya gode wa Gwamnatin Jihar Kano bisa damar da aka ba shi, yana fatan murabus dinsa zai taimaka wa ma’aikatar ta cigaba da aiki ba tare da tangarda ba.

Wasu tsoffin ‘yan majalisar tarayya sun ki amincewa da goyon bayan sake zaben Tinubu a 2027

1

Akalla tsoffin ‘yan Majalisar Tarayya 17 sun nesanta kansu daga wani taro da aka shirya a karkashin kungiyar tsofaffin ‘yan majalisar tarayya (NFFL) domin goyon bayan wa’adin mulki na biyu ga Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu. Sun ce ba su halarci wani taro ba kuma ba su amince da duk wata sanarwa da aka fitar da sunansu ba, suna kiran taron da “shirin siyasa na yaudara.”

A wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar, sun zargi masu shirya taron da yin amfani da kudi da rarrashi domin kirkirar sahihanci na bogi. Sun ce ba za a iya wakiltar daruruwan tsoffin ‘yan majalisa da ‘yan tsiraru da aka tara a boye ba, tare da jaddada cewa tsoffin ‘yan majalisa ba kaya ba ne da za a saya ko a sayar.

Sun kara da cewa ya kamata gwamnati ta dogara da aiki da sakamako maimakon neman goyon baya ta taruka. A cewarsu, idan gwamnatin na ganin ta cancanci wa’adi na biyu, to ta gabatar da hujjojin tsaro, rage tsadar rayuwa, samar da ayyukan yi da daidaita tattalin arziki, domin “goyon baya ba shi ke tafiyar da kasa ba, aiki ne.”

Cire Musulmi dan Arewa a tikitin takarar Tinubu na iya cutar da APC a 2027 – Hannatu Musa Musawa

0

Ministar Al’adu, Hannatu Musawa, ta ce APC na iya fuskantar matsala a zaben 2027 idan ta cire Musulmi dan Arewa daga tikitin Shugaba Bola Tinubu. Ta ce hakan zai jawo cikas musamman a jihohin Arewa masu rinjaye.

Musawa ta bayyana cewa siyasar Arewa na da zurfi, inda jama’a ke daukar zabe da muhimmanci. Ta ce cire Sanata Kashim Shettima ko sauya tsarin tikitin Musulmi da Musulmi na iya fusata masu zabe.

Ta kuma ce hadin gwiwar jam’iyyun adawa ba ta da karfi a halin yanzu, tana mai jaddada cewa APC na da yakinin za ta ci gaba da rike mulki a 2027.

SERAP ta maka ministan hasken wutar lantarkin Nijeriya kotu kan zargin badakalar N128bn na ma’aikatar

0

Kungiyar SERAP ta shigar da kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, da kamfanin NBET, bisa zargin kasa bayyana yadda aka kashe N128bn na kudin jama’a. SERAP ta ce karar ta biyo bayan rahoton Babban Akanta Janar na Tarayya da aka wallafa a ranar 9 ga Satumba, 2025.

A cikin karar, SERAP na neman kotu ta tilasta wa Adelabu da NBET su yi bayani kan abin da ta kira “batan ko karkatar da N128bn,” tare da bayyana ranar fitar da kudaden da kuma wadanda suka amfana. Kungiyar ta kuma bukaci a bayyana sunayen jami’an gwamnati da suka amince ko suka taka rawa wajen sakin kudaden.

SERAP ta ce cin hanci da rashawa a bangaren wutar lantarki na ci gaba da jefa ‘yan Nijeriya cikin duhu, tare da matsalar rugujewar babban layi da hauhawar kudin lantarki. Kungiyar ta ce amincewar kotu da bukatunta zai taimaka wajen inganta gaskiya, da magance matsalolin wutar lantarki a Nijeriya.