Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 41

Ma’aikatan KEDCO sun tsunduma yajin aiki

0

Ƙungiyar manyan ma’aikatan wutar lantarki da ma’aikatan kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

 

Yajin aikin da suka faro shi a ranar Laraba 21 ga watan Janairun 2026, ya biyo bayan zargin da suka yi na rashin kyakkyawan tsarin aiki, baya ga rashin biya musu bukatunsu cikin wa’adin da suka diba.

 

Yajin aikin ya yi sanadiyyar jefa wasu yankuna a jihar Kano cikin duhun rashin lantarki, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

 

Jaridar Punch ta ambato wasu daga cikin jagororin ma’aikatan na jaddada bukatunsu na inganta yanayin aiki, da kuma biyan su tarin basuka da suke bi tun daga shekarar 2014.

Ba zan yi amfani da karfin soji wajen kwace Greenland ba – Donald Trump

0

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ba zai yi amfani da karfin soja domin karbe ikon Greenland ba, yankin da ke karkashin Denmark, sai dai ya jaddada cewa Amurka na bukatar mallakar yankin.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, Trump ya fadi hakan ne a ranar Laraba, 21 ga Janairu, 2026, yayin da yake jawabi ga shugabannin duniya a wani taro da aka gudanar a Davos, Switzerland.

Trump ya ce ko da yake Amurka na da karfin da za ta iya amfani da shi, ba ya so kuma ba zai yi amfani da karfi ba, yana mai cewa kalamansa sun kwantar da hankalin wadanda ke zargin zai dauki matakin soja kan Greenland.

Kotu ta bayar da belin Kwamishinan kuɗi na jihar Bauchi wanda ake zargi da tallafa wa ta’addanci

0

Kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da beli na Kwamishinan kuɗi na jihar Bauchi, Yakubu Adamu, da sauran wadanda ake tuhuma tare da shi, kan zargin tallafa wa ta’addanci da kudi dala miliyan 9.7.

Gidan talajibin TVC ya rawaito Mai shari’a Muhammad Umar ya amince da bukatar bayarda belin a Larabar nan, 21 ga Janairu, 2026, inda ya gindaya sharuddan da dole wadanda ake tuhuma su cika kafin su fita.

Kotu ta umurci kowane daga cikin wadanda ake tuhuma da ya gabatar da masu tsaya masa biyu, wadanda dole ne su kasance Babban Sakataren Ma’aikatar gwamnatin tarayya ko kuma matsayin Darakta a aikin gwamnati.

Haka kuma, an umurce su da su mika fasfo dinsu na kasa da kasa ga rajistaran kotu.

‘Yan sandan Nijeriya sun tabbatar da sace Kiristoci sama da 100 a Kaduna

0

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da cewa an sace fiye da Kiristoci 100 daga Coci uku a jihar Kaduna, bayan da a baya ta musanta faruwar lamarin.

DW Afrika ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a yankin Kurmin Wali, inda mazauna yankin suka ce adadin wadanda aka sace ya kai 177, sai dai mutane 11 sun samu damar tserewa daga hannun masu garkuwa da mutanen.

A cewar rundunar ‘yan sanda, musantawar da ta yi tun da farko ta faru ne sakamakon rashin samun bayanai, inda binciken da aka gudanar daga baya ya tabbatar da cewa an yi garkuwa da masu ibadar.

Atiku ya shiga tsakani yayin da magoya bayansa da na Peter Obi ke takun saka kan tikitin takara a ADC

0

Tsohon dan takarar shugabancin Nijeriya, Atiku Abubakar, ya shiga tsakani domin kwantar da tarzoma bayan takaddama ta kaure tsakanin magoya bayansa da na tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi, kan tikitin shugaban kasa na jam’iyyar ADC gabanin zaben 2027.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa rikicin ya karu ne bayan Peter Obi ya fice daga jam’iyyar Labour Party zuwa ADC a watan Disambar 2025, inda ya bayyana cewa ya dauki matakin ne domin gina hadakar adawa mai karfi da za ta iya fuskantar matsalolin tattalin arzikin Nijeriya da kuma kayar da jam’iyyar APC mai mulki.

Tun bayan shigar Obi cikin hadakar, magoya bayansa musamman ‘yan Obidient Movement suka kara matsin lamba ga Atiku da ya goyi bayan takarar Obi a ADC.

Sai dai hakan ya janyo martani daga magoya bayan Atiku, lamarin da ya kara rarraba kawuna a cikin hadakar tare da tayar da shakku kan dunkulewar adawa gabanin zaben 2027.

Bankin Duniya zai ba da rancen dala miliyan 12 ga jihohin Nijeriya da ke da sansanonin ‘yan gudun hijira

0

Bankin Duniya ya zai bayar da rancen dala miliyan 12 ga wasu jihohin Nijeriya da ke da sansanonin ‘yan gudun hijira, domin inganta tattara bayanai da cike gibin bayanan da suka shafi matsalolin gudun hijira.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, an amince da bayar da kudin ne a karkashin wani sabon shiri wanda Bankin Duniya ya amince da shi a ranar 7 ga Agusta, 2025.

Rahoton ya bayyana cewa, kudin na daga cikin rancen dala miliyan 300 da International Development Association (IDA) ta amince da shi, wanda aka sanya hannu tsakanin Gwamnatin Nijeriya da Bankin Duniya,amma jihohi za su samu kudin ne kawai idan sun cika sharuɗɗan da aka shimfiɗa.

Cyril Ramaphosa ya amince da karin albashi ga ‘yan siyasar Afirka ta Kudu

0

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya amince da karin albashi ga ‘yan siyasa da masu rike da madafun ikon kasar

 

Karin albashin nasu zai fara aiki ne a ranar 1 ga watan Afrilun 2026, kamar yadda fadar gwamnatin ƙasar ta bayyana.

 

DW Africa ta ruwaito cewa karkashin sabon tsarin albashin, mataimakin shugaban kasa zai rika karbar akalla Dala 177,000 a shekara, yayin da ministoci za su rika samun kusan Dala 151,000, sai kuma mataimakansu Dala 124,000.

 

Sai dai wannan mataki na gwamnatin Afirka ta Kudu ya bar baya da kura, inda wasu kungiyoyin ma’aikata da jam’iyyun siyasa ke sukar lamarin.

An kama fiye da mutane 77,000 masu tu’ammali da kwaya a Nijeriya cikin shekaru 5

0

Shugaban hukumar NDLEA mai yaki da tu’ammali da miyagun ƙwayoyi a Nijeriya Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya bayyana cewa cikin shekaru biyar, an kama mutane akalla 77,792 masu tu’ammali da miyagun ƙwayoyi a Nijeriya.

 

Buba ya bayyana haka ne a Abuja, tare da cewa an kama miyagun ƙwayoyi na kilogram 14, 847 a tsawon shekarun.

 

A cewar sa, kamen ya taimaka wajen lalata tsarin masu safarar miyagun ƙwayoyi a ciki da wajen Nijeriya, wanda hakan ke isar musu da sakon cewa ta’adar ba ta da waje a kasar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ana ci gaba da shari’ar Diezani a Birtaniya kan zargin cin hanci

0

Ana ci gaba da shari’ar tsohuwar ministar man fetur ta Nijeriya Diezani Alison-Madueke a kotun London, kan zargin ta da karbar cin hancin Yuro dubu 100

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa Diezani ta gurfana ne a gaban kotun Southwark Crown da ke Landan a kasar Birtaniya, domin fara sauraren shari’ar tuhumar da ake mata kan cin hanci.

Tun bayan kama tsohuwar ministar mai shekaru 65 a shekarar 2015 kafin bayar da belinta, ta musanta tuhume-tuhume shida da ake mata.

Za a fara cikakken zaman shari’ar ne a ranar 26 ga watan Janairun 2026.

Obasanjo ya kai wai Babangida ziyara gidansa da ke jihar Neja

0

Tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya kai wa tsohon shugaban kasar a mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida ziyara a gidansa da ke Minna, babban birnin jihar Neja.

 

Wasu majiyoyi sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa dattawan biyu sun tattauna cikin sirri na tsawon mintuna 30, kafin daga bisani Obasanjo ya koma filin sauka da tashin jiragen sama na Ahmed Bola da ke Minna.

 

Kazalika guda daga cikin majioyin, ya bayyana cewa ganawar tasu na iya kasancewa mai alaka ta kai tsaye da zaben 2027 da ke karatowa.