Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 42

NNPP ta ce za ta ci zaben Kano a 2027 ko da Gwamna Abba ya koma APC

0

Wani jigo a jam’iyyar NNPP Ladipo Johnson, ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta lashe zaben Kano a 2027 ko da Gwamna Abba Kabir Yusuf fice daga cikinta tare da komawa APC.

 

Kalaman nasa sun zo ne a daidai gabar da Gwamnan ya gana da shugaban Nijeriya a fadarsa da ke Abuja a ranar Litinin 19 ga watan Janairun 2025.

 

A cewar Ladipo, ko kadan batun shirin ficewar Gwamnan daga NNPP ba ta girgiza su ba, kasancewar sun gina tubali mai kwari da zai taimaka musu wajen lashe zabe a jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, kamar yadda Channels TV ya wallafa.

 

Duk da cewa ganawar Gwamna Abba da shugaba Tinubu ta ruruta batun komawar sa jam’iyyar APC, mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce ganawar tasu ta ta’allaka ne kan abubuwan da suka shafi kalubale, ayyuka da kuma ci-gaban jihar Kano.

Jami’an tsaro sun sake kama Malami bayan belinsa daga gidan yarin Kuje

0

Rahotanni sun bayyana cewa wasu jami’an tsaro da ake kyautata zaton na hukumar DSS ne sun sake cafke tsohon ministan shari’ar Nijeriya Abubakar Malami SAN.

 

Jaridar Punch ta ruwaito cewa sake kama shi ya zo ne bayan fitarsa daga gidan yarin Kuje sakamakon belinsa da aka bayar.

 

Sai dai har zuwa lokacin da aka tuntubi hukumar tsaron ta DSS, ba a samu wani karin bayani ba.

CAF ta dakatar da kocin Senegal Pape Thiaw

0

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka (CAF) ta sanar da dakatar da kocin tawagar ƙasar Senegal, Pape Thiaw, daga aikinsa na ɗan lokaci.

 

A cikin wata sanarwa da CAF ta fitar, hukumar ta tabbatar da matakin dakatarwar, sai dai ba ta bayyana dalilan dakatarwar ba a wannan lokaci.

 

Pape Thiaw dai shi ne kocin da ke jagorantar tawagar Teranga Lions, kuma dakatarwar na zuwa ne a lokacin da Senegal ke shirin buga wasu wasannin ƙasa da ƙasa.

Sarkin Musulmi ya ayyana Talata 20 ga Janairu a matsayin 1 ga watan Sha’aban 1447AH

0

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya (NSCIA), ya ayyana Talata 20 ga watan Janairu, 2026, a matsayin rana ta farko ta watan Sha’aban, 1447 bayan Hijira.

 

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa ga manema labarai da aka fitar a ranar 19 ga Janairu, 2026, daga fadar Sarkin Musulmi da ke Sokoto.

 

Sanarwar, wadda Farfesa Sambo Wali Junaidu, Waziri na Sokoto kuma Shugaban Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Addini na Majalisar Sarkin Musulmi ya rattaba hannu a kai, ta ce an yanke wannan hukunci ne bayan cikakken bincike da rahotannin ganin jinjirin watan da aka tattara daga sassa daban-daban na ƙasar.

Shugaban majalisar dokokin jihar Borno ya soki rashin sanya hoton Kashim Shettima a taron jam’iyyar APC

0

Shugaban majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkarim Lawan, ya nuna rashin jin daɗinsa kan rashin sanya hoton mataimakin shugaban Nijeriya, Sanata Kashim Shettima a hotunan da aka yi amfani da su wajen wani taron jam’iyyar APC da ake gudanarwa a Maiduguri, babban birnin jihar.

Abdulkarim Lawan ya bayyana hakan ne a yayin taron, inda ya ce abin bai dace ba a ki saka hoton mataimakin shugaban kasa ba, musamman ganin cewa taron na gudana ne a mahaifarsa, kuma shi ne wakilin Arewa maso Gabas a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.

Ya ƙara da cewa irin wannan rashin sanya hoton Shettima ne ya jawo rikici a taron APC na Gombe a bara, yana mai gargadin cewa ya kamata a kauce wa maimaita kuskuren.

Babban limamin Ilorin, jihar Kwara ya rasu yana da shekaru 75

Babban Limamin Ilorin, Sheikh Muhammad Bashir Saliu, ya rasu a Litinin din nan yana da shekaru 75, bayan fama da gajeriyar jinya a Abuja.

An tabbatar da rasuwarsa ne ta bakin mai magana da yawun mai Martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Abdulazeez Arowona, a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce nan gaba kadan za a sanar da lokacin jana’izarsa.

Marigayi Sheikh Muhammad Bashir Saliu, haifaffen Ilorin, jihar Kwara, ya shafe rayuwarsa wajen koyarwa da hidimar addinin Musulunci, ya zama babban Limamin Ilorin ne a Oktoba 1983, yana da shekara 33, kuma ya yi sama da shekaru 40 yana rike da mukamin.

Kwankwaso ya jinjina wa rikon amana da hakurin magoya bayan darikar Kwankwasiyya

Tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yaba wa magoya bayansa bisa haƙuri, juriya da biyayya da suka nuna duk da ƙalubalen da tafiyar ke fuskanta, yana mai cewa hakan ne ke gina kyakkyawar makomar Kwankwasiyya akidar.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya fitar a ranar Litinin, inda ya nuna jin daɗinsa ga magoya baya da masoya tafiyar bisa ci gaba da tsayawa tsayin daka kan manufofin Kwankwasiyya a lokutan da suke fuskantar ƙalubale.

Kwankwaso ya jaddada cewa ƙarfin Kwankwasiyya na ta’allaka ne kan tsantsar biyayyar mabiyanta, gaskiya da ci gaban al’umma, ko da a lokacin matsin lamba.

Birtaniya da Faransa na duba yiwuwar haramta wa yara amfani da kafafen sada zumunta

Kasashen Faransa da Birtaniya na duba yiwuwar bin sahun Australia wajen hana yara da matasan da suka gaza shekaru 20 da haihuwa amfani da kafafen sada zumunta, sakamakon damuwa kan tabarbarewar lafiyar kwakwalwa a tsakanin matasa.

Rahoton ya nuna cewa Australia ita ce ƙasa ta farko da ta haramta wa ’yan ƙasa da shekaru 16 amfani da kafafen sada zumunta kamar Instagram, Facebook, TikTok da YouTube, matakin da ya janyo muhawara a duniya.

A Faransa kuwa, ana muhawara kan kudurori da ke neman hana ’yan ƙasa da shekaru 15 amfani da kafafen sada zumunta, ciki har da wanda Shugaba Emmanuel Macron ke goyon baya.

Kazalika a Birtaniya ma, masana da jami’an gwamnati na tattaunawa kan irin wannan mataki, inda aka gayyaci Jonathan Haidt, fitaccen masanin ilimin halayyar ɗan Adam daga Amurka, domin tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar kan lamarin.

Bobi Wine ya yi watsi da sakamakon zaben Uganda

Hukumar zaɓe ta ƙasar Uganda ta ayyana Yoweri Museveni a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa, inda samun nasarar ta kai shi ga yin wa’adi na 7 a kan mulki.

A bayanan da hukumar zaɓen ta fitar, Museveni ya yi nasara ne bayan kammala ƙirga ƙuri’u a faɗin ƙasar, lamarin da ya tabbatar da ci gaba da zamansa shugaban ƙasa.

Sai dai jagoran adawa Bobi Wine, ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen, inda ya yi zargin an tafka magudi da karya dokokin zaɓe, tare da cewa sakamakon ba shi al’umma suka tsammaci ji ba.

Rikicin siyasa na iya ƙara tsananta yayin da ‘yan adawa ke neman matakan shari’a da na kasa da kasa domin kalubalantar sakamakon zaɓen, a daidai lokacin da gwamnati ke kira ga kwanciyar hankali da zaman lafiya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Tinubu ya umarci a tsananta bincike kan batun hallaka mata da yaranta a Kano

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike kan kisan wata mata, Fatima Abubakar, da ’ya’yanta shida da aka yi a Unguwar Dorayi Chiranci da ke jihar Kano.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban shawara kan harkokin yaɗa Labarai Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin, inda Shugaban ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai kiran lamarin da mummunan ta’addanci, tare da ta’aziyya ga iyalan mamatan.

Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa ’yan sanda bisa saurin cafke waɗanda ake zargi, tare da umartar hukumomin tsaro su tabbatar da ingantaccen bincike da gurfanar da su gaban shari’a.