DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 427

Kotu ta dage sauraron ƙarar da gwamnatin kano ta shigar kan sarautar Kano

Kotu ta dage sauraron ƙarar da gwamnatin kano ta shigar kan sarautar Kano

wata babbar kotu a jihar Kano ta dage ci gaba da zamanta har zuwa ranar 4 ga watan Yuli, inda za ta ci gaba da sauraren karar da gwamnatin Kano ta shigar tana bukatar tabbatar Sarki Sunusi na biyu a kejerar sarauta.

Babban lauyan gwamnatin jihar Kano da majalisar dokokin jihar ta bakin Lauyan su Ibrahim Isah-Wangida suka shigar da karar a ranar 27 ga watan Mayu.

Suna neman a bada umarnin hana Sarkin Kano na 15, Aminu Ado-Bayero da wasu sarakuna hudu da aka tube daga sarautar Bichi, Rano, Gaya da Karaye bayyana kansu a matsayin sarakunan gargajiya.

Sauran wadanda aka yi ƙarar su sun hada da Sufeto-Janar na ’Yan sanda, Daraktan jami’an tsaro na farin kaya a Jiha, da jami’an tsaro na Civil Defence da Sojojin Nijeriya.

Masu Tapswap sun daga ranar da zai fashe

 Masu Tapswap sun daga ranar da zai fashe

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Tapswap ta dage ranar kaddamar da shi, wanda aka shirya yi a ranar 1 ga Yuli.

Shugaban sashin sadarwa na kamfanin, John Robbin ne ya bayyana hakan a wata sadarwa da ya fitar.

Kafin wannan lokacin a baya kamfanin ya sanar da cewa ranar da zai kaddamar dashi za ta kasance ranar 1 ga Yuli bayan sun kasa gatabar dashi bisa yawan masu yin wasan.

Har Izuwa wannan lokaci kamfanin bai bayyana ranar da zai kaddamar da Tapswap din ba.

Nijeriya na bukatar tsarin shugabanci irin na su,Tafawa Balewa,Sardauna da Nmandi Azikiwe

Nijeriya na bukatar tsarin shugabanci irin na su,Tafawa Balewa,Sardauna da Nmandi Azikiwe

An bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba tsarin da Abubakar Tafawa Balewa da Dr Nnamdi Azikiwe da Cif Obafemi Awolowo da Sir Ahmadu Bello da sauran magabata suka yi domin shawo kan kalubalen tattalin arziki da siyasa da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.

Babban kodinetan kungiyar National Unity Pathfinders (NUP) na kasa Ambasada Sixtus Obinna Nwoke da sakataren kasa Saleh Alhassan Kubah injiniya ne suka yi wannan kiran a Abuja a wajen taron kaddamar da kwamitin gudanarwa na kungiyar (CWC) na kungiyar.

Sun ce kalubalen da ake fuskanta a halin yanzu ba za a iya tsallakewa ba, kuma sake duba tsare-tsare da abubuwan da suka gada na shugabannin kasar da suka kafa kasar zai taimaka wajen samar da mafita kan kalubalen.

Saboda irin namijin kokarin da tsoffin shugabannin da suka yi kokari wajen ganin an samu hadin kai da ci gaban Nijeriya.

“A yau, mun taru a matsayin masu neman hanya don tsara sabuwar hanya ga ƙasarmu domin samun mafita ga halin da kasar ke ciki

Mun hada kai wajen neman kasar Nijeriya da ta dace da muradun kasar da muke so, muna hasashen Nijeriya za ta kasance da hadin kai, sanin yanci da kuma sadaukarwar ‘yan kasar baki daya domin shawo kan duk wata matsala da ta addabi kasar baki daya.

Gwamnatin Nijeriya ta kafa kwamitoci biyu da zasu yi yaki da ciwon zazzabin cizon sauro

Gwamnatin Nijeriya ta kafa kwamitoci biyu da zasu yi yaki da ciwon zazzabin cizon sauro

Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin bada shawara kan kawar da zazzabin cizon sauro a Nijeriya (AMEN) da kuma kwamitin ministoci na yaki da zazzabin cizon sauro a yunkurinta na kara kaimi wajen kawar da cutar zazzabin cizon sauro.

Ministan lafiya, Farfesa Ali Pate a lokacin da yake kaddamar da kwamitin ba da shawara da kwamitin ministocin, ya ce matakin ya zama wajibi bisa la’akari da gagarumar matsalar da cutar ke da shi a Nijeriya ta fuskar mace-mace, yada wasu cutukan tsakanin al’umma.

A cikin wata sanarwa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da kasashen waje Tashikalmah Hallah, ministan ya jaddada cewa, duk da cewa ana iya yin rigakafi da kuma magance cutar,amma zazzabin cizon sauro na ci gaba da zama babban kalubale ga kasar.

Don haka, akwai bukatar cigaba da nemo hanyoyi tare da shawarwarin masana da zasu taimaka wajen kawo karshen sa.

Hukumar kwastam ta kama bindigu 844 da alburusai 112,500 aka shigo dasu Nijeriya

Hukumar kwastam ta kama bindigu 844 da alburusai 112,500 aka shigo dasu Nijeriya

Babban Kwanturolan Hukumar hana fasa kwauri ta Nijeriya (NCS) Kwastam, Bashir Adeniyi, ya bayyana yadda aka kama bindigogi guda 844, alburusai 112,500 da sauran haramtattun kayayyaki da aka kama a tashar jirgin ruwa ta Onne da ke jihar Ribas a kudu maso kudancin Nijeriya.

Adeniyi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wani taron manema labarai da aka gudanar a garin Onne,wanda aka shirya domin bayyana kayayyakin da aka kama tare da mika su ga hukumar da ta dace.

Yace bisa bayanan sirri da suka samu, kwantena mai lamba 165396 wadda ta zo daga kasar Turkiyya an samu bayanan akwai gurbatattun abubuwa a ciki da aka shigo dasu

Kwantenar da ke dauke da bindigun da alburusai da aka boye a cikin abubuwa daban-daban kamar su ’yar tsana, kayan daki da kayan aikin famfo an kama ta ne a tashar tashar Onne ranar 21 ga Yuni, 2024 wanda kudin su yakai kusan sama da biliyan hudu.

A dangane da wannan,akwai mutum uku da ake tuhuma suna hannu da zarar an kammala bincike za a kaisu kotun da ta dace domin gurfanar dasu.

‘Yan bindiga sun sake shiga garin Dutsinma jihar Katsina, sun aike da malamin jami’ar FUDMA lahira

Wasu ‘yan bindiga da ba a kai ga tantance adadinsu ba ya zuwa wannan lokaci sun kutsa kai cikin garin Dutsinma na jihar Katsina, inda suka harbe wani malamin jami’ar tarayya ta FUDMA da aka bayyana sunansa da Dr Tiri.
Majiyar DCL Hausa ta kuma ce maharan sun kuma yi awon-gaba da ‘ya’yansa biyu da ba a sanar da jinsinsu ba, wato maza ne ko mata, ko kuma mace da namiji.
Lamarin ya faru a daren Litinin wayewar Talata da misalin karfe 1am.
Majiyar ta ce yanzu haka gawar Dr Tiri da ke koyarwa a sashen tattalin arziki na fannin noma na can a babban asibitin garin Dutsinma jihar Katsina.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ASP Aliyu Abubakar Sadiq bai kai ga amsa kiran wayar da DCL Hausa ta yi masa ba kan lamarin.

Faransa ta doke Belgium da ci 1-0 a gasar cin kofin Nahiyar Turai na 2024

Faransa ta doke Belgium da ci 1-0 a gasar cin kofin Nahiyar Turai na 2024

Faransa ta doke Belgium da ci 1-0, inda ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2024

A ranar Litinin ne Faransa ta doke Belgium da ci daya mai ban haushi, inda ta tsallake zuwa zagayen gab da na kusa da na karshe na gasar cin kofin nahiyar Turai na 2024.

Dan wasan kasar Belgium Jan Vertonghen,ne yaci gida a minti na 85 ana daf da tashi daga wasan wanda ya baiwa kasar Faransa damar shigewa gaba zagaye na gaba.

Gwamnatin Nijeriya za ta dakatar da kwangilar aikin hanyar Lokoja da Benin

Gwamnatin Nijeriya za ta dakatar da kwangilar aikin hanyar Lokoja da Benin 

Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin dakatar da ayyukan da ‘yan kwangilar ke gudanarwa na gyaran hanyar Lokoja zuwa Benin saboda jinkirin aikin da rashin nuna damuwa da halin da al’ummar yankin ke ciki ga ‘yan kwangilar dake aikin.

Ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki a Uyo,inda ya koka da yadda aikin gyaran hanyar baya sauri.

Ministan kuma ya yi gargadin cewa duk dan kwangilar da ya ci gaba da jan kafa game da aikin da gwamnati ta bashi za’a soke kwangilar sa.

Haka kuma akwai shawarwarin da gwamnatin tarayya ta yi na tallafa wa ‘yan kwangilar dake cikin gida Nijeriya, wanda zai yi  tasiri kai tsaye ga tattalin arzikin masu aikin gaba daya

INEC ta gabatar da shawarwari 142 don inganta harkokin zabe a Nijeriya

INEC ta gabatar da shawarwari 142 don inganta harkokin zabe a Nijeriya

Shugaban hukumar zabe ta mai zaman kanta ta kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu,ya ce hukumar tana shirin gabatar da shawarwari 142 domin inganta harkokin zabe a nan gaba.
Yakubu ya bayyana haka ne a wajen bude taron karramawa na kwanaki biyu ga kwamishinonin zabe,a ranar Litinin a Legas.
Ya ce hukumar ta wallafa rahoton sake duba zaben shekarar 2023, inda ya ce tuni aka samu a shafinta na intanet.
Zan iya gaya muku cewa hukumar zabe ta bayar da shawarwari 142 kan inganta harkokin zabe a Nijeriya da ake shirin gabatar dasu.
Da zaran an shirya rahoton, za mu fito fili mu tattauna da ‘yan Nijeriya kan wannan batu domin yana da muhimmancin gaske garesu.
Sauye-sauyen akasari ana aiwatar da su ne ta hanyar gudanar da aikin hukumar ta INEC, amma wasu jami’an tsaro ne za su aiwatar da su a lokacin zabe da zarar an tabbatar dasu.

Mutane 25 ne suka rasa rayukansu, yayinda da 53 suka jikkata a wani hadarin mota a Kano

Mutane 25 ne suka rasa rayukansu, yayinda da 53 suka jikkata a wani hadarin mota a Kano

Hukumar kiyaye afkuwar haddura ta kasa reshen jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar matafiya 25, yayin da wasu 53 suka samu raunuka a wani hatsarin mota.

Hatsarin ya afku ne da sanyin safiyar Litinin a kusa da Kasuwar Dangwaro, dake hanyar zariya a Kano.

Matafiyan sun yi lodi ne a cikin wata tirela wadda take dauke da shanu ta da zata tafi yankin kudancin Nijeriya daga Maiduguri.

A cewar kwamandan hukumar FRSC a jihar, Ibrahim Abdullahi, hatsarin ya afku ne da wata tirela (IVECO) mai lamba XA 311 ZB.

Yace an kira su ne da misalin karfe 03:15 na daren ranar 1 ga Yuli, 2024. Da samun labarin, suka yi gaggawar aika jami’ai da motar  zuwa inda lamarin ya faru domin ceto wadanda lamarin ya shafa da karfe 03:30.

Kwamandan sashin ya ce hatsarin ya afku ne sakamakon gudun wuce gona da iri da motocin keyi.