DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 426

Kotu ta tasa ƙeyar jami’ar NSCDC gidan gyaran hali

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da umarnin tsare wata babbar jami’ar Sibil difens mai suna Mrs Tosin Olagunju, a gidan yari na Suleja.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito, mai shari’a Binta Nyako ta bayar da wannan umarni ne bayan an gurfanar da Olagunju a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume hudu da suka hada da damfarar masu neman aiki da sauransu.

An zargi Mrs Tosin Olagunju da karbar Naira miliyan 12.4 daga hannun masu neman aiki, tare da alkawarin cewa tana da karfin da za ta ba su aikin na Sibil Difens.

Ba rikicin masarauta bane dalilin rashin ci gaba da zaman zauren – Majalisar Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta karyata rade-radin da ake yadawa kan batun zaman majalisar, lamarin da aka jingina da rashin tsaro, wanda ya samo asali daga rikicin masarautar jihar.

Kakakin Shugaban Majalisar, Kamaluddeen Shawai ne ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a ranar Laraba.

Yace labarin da ake yadawa ba gaskiya bane “karya ne kuma maras tushe”.

Shawai ya bukaci al’ummar jihar da su yi watsi da duk wani rahoton da ke nuni da cewa majalisar ba ta sake bude zauren majalisar saboda rashin tsaro da rikicin masarautar ya haifar.

“Majalisar za ta dawo zamanta nan ba da jimawa ba,” in ji shi.

Ban tattauna batun sakin Nnamdi Kanu da gwamnonin Kudu maso Gabas ba – Obasanjo

 

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce bai tattauna batun sakin Nnamdi Kanu ba yayin ganawarsa da gwamnonin Kudu maso Gabas a jihar Enugu .

Daily Truth ta ruwaito a ranar Talata Obasanjo tare da Cif Emeka Anyaoku da Mai Martaba Igwe Alfred Nnaemeka Achebe, sun gana da gwamnonin Kudu maso Gabas.

Bayan kammala taron an yi ta rade-radin cewa taron ya tattauna batun sakin Nnamdi Kanu, wanda shi ne shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra.

Mutane 63 sun rasa rayukansu sanadiyyar cutar Kwalara, 2,102 sun kamu a Nijeriya

Kimanin mutane 63 ne ake zargin sun rasa rayukansu yayin da 2,102 ake zargin sun kamu da cutar ta kwalara a fadin jihohi 33 tun daga farkon wannan shekarar. 

Darakta Janar na hukumar da ke yaki da cututtuka a Najeriya, Dakta Jide Idris ne ya bayyana hakan a Abuja yayin da yake karin haske kan bullar annobar.

Ya ce jihohi 10 da suka fi yawan masu cutar sun hada da Legas, Bayelsa, Abia, Zamfara, Bauchi, Katsina, Cross River, Ebonyi, Ribas da Delta.

Majalissar Dattijan Nijeriya na shirin baiwa ƴan ƙasashen ƙetare damar mallakar katin ɗan ƙasa

Majalisar dattijan Nijeriya ya gabatar da kudirin doka a ranar Talata don yi mashi karatu na biyu da nufin baiwa ƴan ƙasashen ƙetare damar mallakar katin ɗan ƙasa ta NIN.

Zaman majalissar wanda ya gudana a ranar Talata. Kudirin dokar wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya dauki nauyi, an fara karanta shi ne a ranar 5 ga watan Yuni.

Sanata Cyril Fasuyi, daga Ekiti ta Arewa ya gabatar da kudurin dokar a yayin zaman majalisar, kamar yadda Sanata Barau Jibrin ya jagoranta. 

Ma’aikacin Gidan Rediyon Faransa RFI Hausa, Malam Kabiru Yusuf ya rasu

Kamar yadda Editan Gidan Rediyon Bashir Ibrahim Idris ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce Malam Kabiru Yusuf bai dade da dawowa daga aikin hajjin wannan shekarar ba a kasar Saudiyya.

Kabiru Yusuf shi ne wakilin Gidan Rediyon Faransa na Abuja, ya rasu a Kano.

Jirgin farko na alhazan jihar Kano 554 zai taso zuwa gida Nijeriya

 Jirgin farko na alhazan jihar Kano 554 zai taso zuwa gida Nijeriya

Kimanin alhazan jihar Kano kimanin dari biyar da hamsin da hudu (554) sun kammala shirye-shiryen komawa gida a jirgin farko.

Babban Daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana haka a yau a yayin ban kwana da mahajjata a Unguwar Kudai da ke birnin Makka na kasar Saudiyya.

Wannan ya biyo bayan jadawalin da hukumar jin dadin alhazan da Max Air suka tsara, kamar yadda aka gani a makon da ya gabata. Lamin Rabi’u ya bayyana cewa wadanda suka zo na farko su ne za su fara komawa gida.

Kananan hukumomin da aka tantance sun hada da Gwale, Dala, Ungogo, da Fagge. Ya bukaci daukacin alhazai da su ci gaba da zaman lafiya da hakuri. Yace dukkanin mahajjata za su ci gaba da samun abinci, magunguna, da duk wata kulawar da ta dace har zuwa har zuwa lokacin da zasu dawo.

Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa wanda daraktan ayyukan hajji Alhaji Kabiru Muhd Panda ya wakilta ya yi kira ga wadanda suka dawo da su kula da kyawawan dabi’u kamar yadda suke yi a da da kuma ci gaba da addu’ar samun nasara a wannan aikin.

Jirgin zai taso ne daga filin jirgin sama na Sarki Abdul-Aziz a Jidda a yau zuwa filin jirgin Malam Aminu Kano tare da alhazan jihar Kano.

Kudaina muzgunawa ma’aikatanmu yayin da suke kan aiki- FRSC

Kudaina muzgunawa ma’aikatanmu yayin da suke kan aiki- FRSC

Hukumar kiyaye afkuwar haddura ta kasa (FRSC) ta gargadi masu ababen hawa da su daina muzgunawa jami’anta a yayin gudanar da ayyukansu a fadin kasar nan.

Shugaban hukumar FRSC, Malam Shehu Mohammed ya yi wannan gargadin ne a lokacin da yake mayar da martani kan hukuncin da wata kotun majistare ta yanke na daurin shekaru uku a gidan yari bisa laifin cin zarafin jami’an hukumar.

Shugaban ya nuna jin dadinsa da hukuncin da aka yanke tare da jinjina wa bangaren shari’a kan yadda ake gudanar da adalci cikin gaggawa.

Ya kuma nanata kudurin rundunar na hada kai da bangaren shari’a wajen gaggauta hukunta masu laifi musamman wadanda ke cin zarafin jami’an ta a kan hanyoyi da ke fadin kasar.

Babu wani abu tsakanin sarkin musulmi da gwamnan Sokoto:Fadar sarkin musulmi

Babu wani abu tsakanin sarkin musulmi da gwamnan Sokoto:Fadar sarkin musulmi

Babu wani abu tsakanin sarkin musulmi da gwamnan jihar sokoto Ahmad Aliyu,Dokta Muhammad Jabbi kilgori ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi a wajen bude taron jin ra’ayin jama’a kan gyaran dokar, Sa’in Kilgori, Dokta Muhammad Jabbi Kilgori, ya ce gyaran ba zai tube Sarkin Musulmi daga mulki ko ayyukansa ba.

Ya ce sabanin hasashe, babu wani batu tsakanin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar da gwamna, Alhaji Ahmed Aliyu.

Kilgori, wanda ya zama hakimin Kilgori kuma dan majalisar masarautar, ya ce masarautar tana sane da wasu makiya da ke son haifar da matsala tsakanin masarautar da gwamnatin jihar.

Babu wani batu tsakanin Sarkin Musulmi da Gwamna Ahmed Aliyu ko kadan. Sarkin Musulmi a shirye yake ya yi aiki a karkashin kowace doka da aka zaba ta hanyar da ta dace. Mun yi aiki a ƙarƙashin dokoki daban-daban a baya kuma a shirye muke mu yi aiki a ƙarƙashin sabuwar doka.

Yace sarkin ya yi aiki a karkashin dokar da aka gabatar don gyara na tsawon shekaru 16. Sarkin Musulmi a shirye yake ya yi aiki kafada da kafada da gwamnati,

Aminiya ta ruwaito cewa gyaran da ake shirin yi a Sakkwato ta shekarar 2008 ya tayar da kura daga ciki da wajen jihar biyo bayan rade-radin da ake yi cewa gyaran ana shirin tsige sarkin musulmi ne

Matar mataimakin gwamnan Neja ta rasu

 Matar mataimakin gwamnan Neja ta rasu

Hajiya Zainab, mai-ɗakin mataimakin gwamnan Neja, Yakubu Garba, ta rasu a wannan Rana ta Talata da safe.

Hadimin mataimakin gwamnan, Salis Sabo ne ya bayyana labarin rasuwar a shafinsa na facebook.

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, mun yi rashin mai-ɗakin Mai gida na mataimakin gwamnan Neja. Allah Ya gafarta mata Ya sa aljannar Firdaus ce makomar ta,

” in ji shi.