DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 429

Sabuwar kungiyar tawaye a Nijar tace ta ita ce ta yi garkuwa da kantoman Bilma

Sabuwar kungiyar tawaye a Nijar ta FPJ ta yi ikirarin cewa ita ce ta yi garkuwa da Kantoman Bilma nan da mukarabbansa

A cikin wani sako ta shafukan sada zumunta, sabuwar kungiyar tawaye ta Front Patriotique pour la Justice ko FPJ a takaice ta ce ita ce ke da alhakin kame shugaban karamar hukumar Bilma da ke cikin jihar Agadez Commandant Amadou TORDA tare da mukarabban sa 4 ciki har da babban jami’in tsaron Gendarmerie na yankin Bilma

Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Mahamat Tori ta zargi hukumomin mulkin sojan Nijar na CNSP da jefa kasar cikin yanayin kama karya da rashin adalci

A ranar Juma’ar da ta gabata ne 15 ga watan Yunin nan tawagar Kantoman na Bilma a yayin da take kan hanyar ta ta dawowa daga Dirkou bayan halartar wani taron adda’o’in zaman lafiya da kungiyar farar hula ta M62 ta shirya ta fuskanci harin kwantan baunar ‘yan tawayen inda suka budewa tawagar huta nan take lamarin da ya kai ga yin garkuwa da su

Rundunar ‘yan sandan kano sun tura karin jami’ai zuwa manyan fadojin jihar biyu

 Rundunar ‘yan sandan kano sun tura karin jami’ai zuwa manyan fadoji 2 a Kano

Rundunar ‘yan sandan ta tura karin jami’an tsaro zuwa manyan fadadoji guda biyu da ke dauke da sarakunan da ke bangarorin biyu

Tsohon kwamishinan ‘yan sandan Kano, AIG Usaini Gumel ne ya tabbatar da hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ta wayar tarho.

Gumel ya ce, “An tura jami’ai da kayan aiki domin tunkarar duk wani abin da ba a yi tsammani ba a yankunan da aka gano a cikin garin, don haka hukumar .’yan sanda za ta cigaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Ya bayyana cewa tura sojojin na da nufin hana barazanar tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiya har sai an samu sakamakon rikicin na masarautar.

AIG Gumel ya ce rundunar ta kara karfafa shirinta na tura jami’anta domin tabbatar da ingantaccen tsaro da zaman lafiya a jihar.

“An baza jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro a fadar Kofar Kudu, gidan sarki Malam Mohammadu Sunusi, da kuma fadar Nasarawa Mimi, gidan sarki Aminu Bayero,” inji shi.

Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan Nijeriya da su guji shan da ake hadawa a gida kamar, Kunu da Zobo

Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan Nijeriya da su guji shan da ake hadawa a gida kamar, Kunu da Zobo

Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan Nijeriya da su guji shan abin sha da ake hadawa a cikin gida irin su kunu, zobo da fura domin gujewa yaduwar cutar kwalera.

Karamin Ministan Muhalli, Iziaq Salako ne ya bayar da wannan shawarar a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Salako ya ce matakan kariya ga kamuwa da cutar shine tsaftace muhallinsu a ko da yaushe da dena zubar da shara musamman a wuraren ba a kebe ba.

Yace amfani da ruwa mai tsafta na da matukar muhimmanci ga lafiyar al’umma musamman idan ansamu masu tafasa ruwan kafin amfani dashi

A guji shan abubuwan da aka shirya a gida kamar su kunu, zobo, fura da nono, koko, ruwan ‘ya’yan itace da sauransu sai dai an tabbatar anyi cikin tsafta da aminci.

Ya kuma yi kira ga Jihohi da Kananan Hukumomi da su kara sanya ido kan lafiyar muhalli a wuraren da ake sayar da abinci da abin sha a fadin kasar nan.

Waɗannan wuraren sun haɗa da kasuwanni, gareji, makarantu, gidajen abinci, filin wasa, wuraren ibada da na wasanni.

Dole ne mu kare sarkin musulmi- Kashim Shettima

Dole ne mu kare sarkin musulmi- Kashim Shettima.

Mataimakin Shugaban ƙasar ya faɗi hakan ne a jihar Katsina a wajen kaddamar da taron inganta tsaro da kungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma tare da hadin gwiwar hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP ta shirya.

Taron ya samu halartar Gwamnonin shiyyar guda 7 da sarakunan Katsina, Daura, Zazzau, Kazaure da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammd Sa’ad Abubakar III.

Shettima yace cikin dukkan al’amuran ci gaba a kasar nan, mai martaba sarkin musulmi, anayin komi dashi don haka yazama wajibi muyi godiya ga dukan iyayenmu na sarakuna a kasar nan.

Ya kuma mika sako ga mataimakin gwamnan Sakkwato wanda ya wakilci gwamnan, inda yace sarkin musulmi bawai sarkin musulmi ne kawai ba, ya fi wannan matsayin a wajen mu domin yana wakiltar al’umma ne gaba daya a kasar nan don haka yana bukatar kariya,  don ci gaban al’ummarmu,

Ya bayyana haka ne bayan babban daraktan kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), Farfesa Isiaq Akintola, ya koka da cewa gwamnatin Sokoto na shirin tsige sarkin musulmin.

A baya dai gwamna Ahmed Aliyu ya kori sarakunan gargajiya 15 bisa wasu laifuka.

Peter Obi yayi kira da al’umma su hada hannu wajen kawo gyara a Nijeriya

Peter Obi yayi kira da al’umma su hada hannu wajen kawo gyara a Nijeriya

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi,ya yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su hada kai domin kawo sauyi ga al’umma.

Ya kuma yi kira da  shugabanni su dauki mataki domin magance halin da kamfanoni da dama ke ficewa daga Nijeriya, inda ya bayyana cewa hakan yana jawo asarar da aka yi kiyasin Naira tiriliyan 95 cikin shekaru biyar da suka gabata.

Obi, a cikin wata sanarwa daya fitar a shafin sa na X, ya bayyana ficewar manyan kamfanoni goma a cikin shekarar da ta gabata kadai, wadanda suka hada da GlaxoSmithKline, Equinor, Sanofi-Aventis, Bolt Food, Procter & Gamble, Jumia Food, PZ Cussons, Kimberly-Clark, da Diageo.

Yace ya zama dole a magance ficewar da wasu kamfanoni daga Nijeriya ke yi a wannan lokacin domin yana janyo asara ga al’ummar kasar baki daya.

Mahaifiyar matar mataimakin shugaban kasa ta rasu

Mahaifiyar matar mataimakin shugaban kasa ta rasu 

Mahaifiyar matar mataimakin shugaban kasa kashim shettima Maryam Albishir mai shekaru 69, ta rasu a Kano da yammacin ranar Lahadi bayan doguwar jinya da tayi fama da ita.

A wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar, Mista Stanley Nkwocha ya sanyawa hannu ta bayyana rasuwar tata.

Za a yi jana’izar Hajiya Maryam, mahaifiyar matar mataimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Shettima da yammacin ranar Litinin a Kano, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kungiyar kare hakkin Musulmi a Nijeriya ta zargi Gwamna Aliyu na jihar Sokoto da shirin tsige Sarkin Musulmi

Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta koka kan shirin da Gwamnan jihar sakkwato Ahmed Aliyu keyi na tsige sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.

Babban daraktan kungiyar Farfesa Isiaq Akintola ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce da takun saka a kan tsige wasu sarakuna a jihar Kano.

A baya dai Gwamna Aliyu ya kori sarakunan gargajiya 15 bisa zargin su da wasu laifuka.

A cikin sanarwar, Akintola ya ce musulmin Nijeriya sun ki amincewa da duk wani tunanin na yunkurin tsige sarkin musulmin.

‘Yan bindiga sun yi mummunan ta’adi a kauyen Katsina

Wasu ‘yan bindiga da ba a san adadinsu ba, sun kai hari kauyen Mai Dabino na karamar hukumar Danmusa jihar Katsina, inda suka hallaka kusan mutane 9.
Majiyar DCL Hausa ta ce da yawa daga cikin wadanda aka kashe din kone su aka yi da wuta.
Majiyar ta ce maharan sun shiga garin da yammacin Asabar har zuwa karfe 2 na daren wayewar Lahadi, inda suke harbin kan mai uwa da wabi.
Kazalika, bayanan da DCL Hausa ta tattara sun ce maharan sun kuma kone duk wasu manyan shaguna da ke garin, da gidaje da motoci a lokacin wannan harin.
Bugu da kari, ‘yan ta’addar sun kuma sace mata da kananan yara da ya zuwa yanzu ba a san adadinsu ba.
Majiyar DCL Hausa ta ce yanzu haka da sanyin safiyar Lahadi, an fara jana’iza wadanda aka kashe a kauyen.
Mazabar Mai Dabino na daga cikin mazabu 11 na karamar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina da ke fama da matsalar tsaro.

Sojoji sun hallaka ‘yan bindiga masu tarin yawa a Giwa jihar Kaduna

Rahotanni daga karamar hukumar Giwa jihar Kaduna na cewa sojoji sun yi nasarar hallaka ‘yan bindiga masu tarin yawa a wani harin da suka kai a yankin.
Wannan harin da sojoji suka kai ta sama da kasa ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan bindigar, ciki kuwa hada wasu daga cikin jagororinsu a yankin Bula a cikin Dajin Yadi na karamar hukumar ta Giwa a jihar Kaduna.
Kamar yadda sako ya isa ga gwamnatin jihar Kaduna, an kai wannan harin ne biyo bayan wasu bayanan sirri da aka samu bayan kashe wasu jiga-jigan ‘yan bindiga a kan iyakar Kaduna-Katsina.
Bayanan sirrin dai sun ce ‘yan bindigar sun hadu a Dajin Yadi ne domin su kitsa yadda za su farmaki al’ummomi daban-daban na jihar. Bayan samun wannan bayani, jami’an tsaro suka kimtsa suka tunkare su yadda ya kamata, kuma suka yi nasarar yin fata-fata da su.
Bayanin hakan dai na cikin wata sanarwa daga kwamishinan tsaro da lamurran cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan da DCL Hausa ta samu kwafi.

Alhazan kasar India sun koka da halin rashin kula a Saudiyya

Alhazan kasar India sun koka cewa ba a samar musu da abubuwan da suka kamata ba a aikin hajjin wannan shekarar na 2024.

Daga cikin abubuwan da suka rasa hada rashin tsafta a sansanonin Alhazai, karancin abinci, cunkoso musamman a Mina a lokacin gudanar da aikin hajjin bana.
Alhazan kasar ta India da suke cikin jerin kasashen Musulmin duniya da suka halarci wannan aikin hajji, sun zargi hukumar kula da aikin hajji na kasar da watsar da su.
Da yawa daga cikin alhazan dai sun saka a kafafen sadarwar zamani suna korafin yadda suka ce an ba a samar musu da wurare masu tsafta ba.