DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 430

Za a shafe shekaru 17 ba a yi aikin hajji cikin zafin rana ba bayan na shekarar 2025 – Hukumomin Saudiyya

Cibiyar kula da yanayi ta Saudiyya ta yi hasashen cewa aikin hajjin badi na 2025 ne zai zamo na karshe da za a gudanar cikin tsananin zafin rana.
Cibiyar ta ce za a gudanar da aikin hajjin 2026 cikin kwanakin sanyi da za a kwashe shekaru 8 jere ana aikin hajji ba tare da zafin rana ba, kamar yadda aka yi wadannan 8 ana kwala rana.
Kakakin cibiyar da ke kula da sararin samaniyar ta Saudiyya Hussein Alqahtani ya ce aikin hajjin zai shiga wani sabon aji na sauyin yanayi, wanda wataqila a iya kwashe kusan shekaru 17 kafin zafin rana ya dawo a yayin gudanar da aikin hajji.
Hakan na nufin za a gudanar da aikin hajjin badi 2025 cikin zafin rana, amma na badi waccan 2026 zai kasance lokacin ya sauya.

Hukumar NDLEA ta kama mata masu shaye-shayen miyagun kwayoyi a Katsina

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta ce a halin da ake ciki ana samu karin mata masu tu’ammali da miyagun kwayoyi a baya-bayan nan, inda ta ce har ma ta fara kamo wasu daga cikinsu domin a yi wa tufkar hanci cikin lokaci.
Shugaban hukumar na jihar Katsina Hassan Sani Abubakar ya sanar da hakan a lokacin taron manema labarai domin bikin makon yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi da majalisar dinkin duniya ta ware.
Shugaban hukumar ta NDLEA na jihar Katsina Hassan Sani Abubakar ya ce duk a cikin kokarin da suke yi na yaki da sha da fataucin kwayoyi, sun yi nasarar fasa taron wasu matasa da suke kokarin shigo da wata sabuwar hanyar shaye-shaye a fadin jihar Katsina.
Ya ce suna samun kalubale musamman daga ‘yan cikin Unguwa idan ma’aikatansu suka je aiki a lungu sa sako na jihar a kokarin da suke yi ma kawar da dabi’ar shaye-shaye a cikin al’umma.
Shugaban hukumar ya ce sun yi nasarar kama mutane 1,344, da ake zargi da sha da kuma masu sayarwa wadanda daga cikin wannan jimilla akwai mata da abin ke nema ya ta’azzara.
Sauran kayan shaye-shaye, kamar kamar yadda Hassan Sani Abubakar ya bayyana akwai tabar wiwi, maganin tari na ‘Codeine’ da aka sauya wa samfuri daga na ruwa zuwa na ‘kwaya’ wato ‘tablet’.
Shugaban hukumar ya kuma kara da cewa akwai mutane kimanin 106 da hukumar ta kai kotu da kuma wasu da yanzu haka an ma rigaya da an yanke musu hukunci suna can suna girbar abin da suka shuka.

Buhun masara ya cike N100,000 a wasu kasuwannin Nijeriya

Masara tayi tashin gwouron zabi a kasuwar Mile 12 International Market Lagos, a makon nan ana sayar da buhu mai cin tiya 40 kan kudi ₦100,000 daidai, yayin da a makon jiya aka sai da ₦87,000, a mako guda an samu karin ₦13,000 a jihar da ke kudancin Najeriya.

Ita ma dai kasuwar Mai’adua jihar Katsina buhun masarar ya kusa cika ₦100,000, inda aka sayar da buhunta kan kudi ₦95,000 a satin nan da ke mana ban kwana, bayan da a makon da ya gabata aka saya ₦84,000, karin ₦11,000 kenan aka samu.
To a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano ₦85,000 aka sayi buhun masarar a makon nan, inda a makon da ya gabata aka saya ₦82,000, ita ma dai karin dubu 3 kenan aka samu a satin nan.
A kasuwannin jihohin Adamawa da Kaduna an sai da Buhunta ₦87,000 a wannan makon, amma farashin na makon jiya ya sha banban a kasuwannin, inda aka sayi buhun masara ₦85,000 a kasuwar Giwa jihar Kaduna a satin da ya shude, sai kuma kasuwar Karamar Hukumar Gombi a jihar Adamawa da aka saya ₦79-80,000.
Shinkafar Hausa kuwa ta fi sauki a kasuwar Mai’adua jihar Katsina da aka saya ₦145,000 a satin nan, amma a makon jiya ₦150,000 aka sayi buhunta, an samu ragin ₦5000 kan farashin makon da ya wuce.
Su kuwa Jihohin Adamawa da Kano da jihar Kaduna da ma Lagos, kuɗin buhun Shinkafa ‘yar gida ₦150,000 cif ne wannan makon, hakan kuwa batun yake a makon da ya shude.
Ita kuwa Shinkafar waje ta fi tsada a kasuwar Giwa jihar Kaduna da ke arewacin kasar da ake saidawa ₦86,000,bayan da a makon da ya gabata aka saya ₦80,000
Sai dai farashin Shinkafar wajen bai sauya tufafi ba da na makon jiya wanda aka saya ₦85,000 a kasuwar Dawanau jihar Kano.
An sayi buhun Shinkafar waje ₦78-80,000 daidai a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa a satin nan da ke dab da ƙarewa, inda a makon jiya aka sai da kan kuɗi ₦75,000.
A Mai’adua jihar Katsina ₦81,000 ne kuɗin buhun Shinkafar waje a satin nan, bayan a satin da ya gabata aka sayar ₦78,000.
Bari mu kammala Farashin Shinkafar waje da kasuwar Mile 12 International Market Lagos, da aka saya ₦83,000.
Kwalin taliyar Spaghetti ma dai ya fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market Lagos da aka saya ₦17,000 a satin nan, yayin da a makon jiya aka sai da ₦16,000 karin ₦2000 a mako guda.
Sai kasuwar Mai’adua jihar Katsina da aka saya ₦15,000 a makon nan, bayan da a makon jiya aka saya ₦15,500
An samu ragin ₦500 kenan a makon nan.
A kasuwar Dawanau jihar Kano ₦13,500 ake sayar da kwalin taliyar a wannan makon,haka farashin yake a makon jiya.
Sai kasuwar Zamani da ke nan jihar Adamawa da aka sayi kwalin ₦14,000,inda a makon jiya aka saya ₦13,000 daidai.
To a kasuwar Giwa jihar Kaduna ma dai farashin bai sauya dana makon daya gabata da ake saidawa ₦14,000 cif.
Ga ma’abota cin kosai da alala kuwa Farashin farin wake ₦2200,000 ne a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas a wannan satin,amma satin daya gabata ₦200,000 daidai a kasuwar.
Sai dai a kasuwannin jihohin Kano da Kaduna kuwa ₦175,000 aka sayar da buhunta a makon nan,yayinda a makon jiya aka sai da buhun kan kuɗi ₦170,000 cif.
₦160-170,000 ake sayar da buhun farin wake a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa a sati na, yayin da a satin da ya kare aka saya ₦160,000 daidai.
Da muka leka kasuwar Mai’adua jihar Katsina ma mun taras cewa ana sayar da buhun waken N170,000 a satin Nan, yayin da makon da ya gabata aka saya N165,000.
DCL Hausa A’isha Usman Gebi

Nnamdi Kanu na neman sulhu da gwamnatin Nijeriya

Jagoran masu fafutikar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu ya ce ai nemi zaman sasanci da sulhu tsakaninsa da gwamnatin Nijeriya bisa tuhumarsa da ake yi.
Kanu na magana ne ta hannun lauyansa Alloy Ejimakor, inda ya fada wa kotun tarayya a Abuja cewa zai nemi wannan sasanci ne karkashin doka ta 17 ta kotun tarayya.
Lauyan gwamnati, Adegboyega Awomolo ya ce tuni ya sanar da bangaren Kanu cewa ba ya da hurumin jagorantar wannan zaman sasanci a madadin gwamnatin tarayya.

Na bar Nijeriya fiye da yadda na same ta – Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Nijeriya Chief Olusegun Obasanjo ya ce ya bar kasar da cigaba fiye da yadda ya same ta a lokacin da ya karbi ragamar tafiyar da ita a shekarar 1999.
Obasanjo, wanda tsohon shugaban kasar mulkin soji ne, an zabe shi a matsayin shugaban kasa na farar hula a shekarar 1999, inda ya yi wa’adi biyu na mulki, ya sauka a shekarar 2007.

Sauya taken kasa na daga cikin nasarorin da muka cimmawa a majalisar dokokin Nijeriya – Akpabio

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya Sanata Godswill Akpabio ya ce da ba a sauya taken kasa a shekarar 1978 ba watakila, kasar ba ta san wani abu ta’addanci ba a halin yanzu.
A shekarar 1978 ne dai Gwamnatin soji ya wancan lokacin karkashin Olusegun Obasanjo ta daina amfani da wancan taken kasar.
Lilian Jean Williams dai ne ya rubuta wancan taken kasar da ake cewa “Nigeria We Hail Thee’ a shekarar 1959.
Arise O compatriots da Pa Ben Odiasse ya rubuta ce aka cigaba da amfani da ita har sai da shugaba Tinubu ya ajiye ta ya maido da wancan tsohon taken kasar da aka ajiye a zamanin mulkin soji.
Ba tare da bata lokaci ne ba dai kudirin sauya taken kasar ya tsallake karatu na daya da na biyu a zaurukan majalisar dattawa da ta wakilan Nijeriya kuma shugaban kasa ya rattaba masa hannu.
Sanata Akpabio ya ce dawo da wancan tsohon taken kasar na daga cikin nasarorin da ya samu a jagorancin majalisa da yake yi.

Jam’iyyar APC na neman gwamnatin tarayya ta kafa dokar ta-baci a jihar Rivers

Shugabancin jam’iyyar APC a jihar Rivers ya roki gwamnatin tarayya da ta kafa dokar ta-baci a jihar.
Shugaban rikon jam’iyyar a jihar Mr Tony Okocha ne ya yi wannan rokon a lokacin wani taron manema labarai a Fatakwal babban birnin jihar.
Ya ce jihar Rivers na cikin halin yakin da ya lakume rayukan mutanen da ba a san adadinsu ba ya zuwa yanzu.
Gwamnatin tarayya dai na da hurumin kakaba dokar ta-baci a duk jihar da aka samu barkewar wata annoba, rikicin da ya ki ci, ya ki cinyewa, zazzafan fadan da ya ki karewa a tsakanin bangarori, barkewar wata cuta ko wasu abubuwan da ke kawo barazana ga tsaro.

Gwamna Rivers Fubara ya umurci a binciki asusun ajiyar kananan hukumomin jihar

Gwamnan jihar Rivers Similaye Fubara ya umurci babban mai binciken kudi na jihar da ya gaggauta binciken asusun ajiyar kananan hukumomin jihar 23.
Umurnin Gwamnan na a binciki asusun ajiyar kananan hukumomin ya takaita ne a shekaru uku da suka gabata.
Wannan umurni dai na zuwa ne a lokacin da gabar siyasa ke kara zafafa tsakanin Gwamnan sa tsohon ubangidansa, ministan Abuja Nyeson Wike.
A lokacin da yake rantsar da sabbin kantomomin kananan hukumomin jihar, Fubara ya ce dalilin hakan shi ne don ya zama izna ga sabbin wadanda za su kama madafun iko.

Ba ‘yan Nijeriya kadai ne ke fama da talauci ba, in ji Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya ce ba ‘yan kasar kadai ne ke fama da talauci ba a duniya.
Sai dai shugaban kasar ya aminta cewa ‘yan kasar na cikin halin matsin rayuwa da talauci.
Amma a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawunsa Mr Ajuri Ngelale, ta ce shugaban kasar ya sha alwashin shawo kan wadannan matsalolin da ‘yan kasa ke ciki na talauci.
Daga cikin hanyoyin da ya yi alkawarin zai bi don shawo kan matsalolin hada kakkabe ayyukan ta’addanci don manoma su koma gona don noma abin da za su ci, su sayar.
Shugaban kasar na magana ne a Lagos a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Sanata Godswill Akpabio da sauran tawaga a lokacin sa suka je yi masa barka da sallah.

Buhun shinkafar bature ya zarta N85,000 a sassan Nijeriya

Kayan abinci na kara tsada a yayin da bikin Babbar Sallah ke ƙara karatowa a sassan kasar nan, inda a satin da ke shirin karewa aka sayi buhun Masara ₦87,000 a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Lagos a kudancin Najeriya, bayan da makon da ya shude aka saya ₦84,000.

Sai kasuwar Dandume jihar Katsina da aka sayar da Buhunta kan kuɗi ₦83-88,000 a wannan makon.
Ita kuwa kasuwar Mai’adua a jihar Katsina ₦84,000 ake sayar da buhun masara a wannan makon, haka batun yake a satin da ya gabata.
To a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna an sayi buhun Masara ₦85,000 a satin nan, yayin da a makon jiya aka saya ₦80,000, karin ₦5000 kenan cikin mako guda.
Da DCL Hausa ta yi tattaki zuwa kasuwar Dawanau da ke jihar Kano ta taras da masarar ta kara ₦2000 kan kuɗinta na makon jiya da aka saya ₦80,000 daidai, amma a satin nan ₦82,000 ne kuɗin buhun ya ke a kasuwar.
An sayi buhun Masara ₦79-80,000 cif a Kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa a wannan makon, hakan kuwa aka sai da makon jiya.
To bangaren Shinkafar Hausa kuwa, ta fi sauki a makon nan a kasuwar Mai’adua jihar Katsina wanda aka sai da buhunta ₦140-145,000, haka kuɗin ya ke a makon jiya.
Sai dai shinkafar ta fi tsada a kasuwar Dandume jihar Katsina da aka saya ₦130-155,000.
A Mai’adua jihar Katsina an sayi buhun ₦150,000 cif a satin nan, bayan da a makon da ya gabata aka sai da buhun shinkafar Hausar ₦145,000, an samu karin ₦5000 kenan a makon nan.
Sai dai kuma kuɗin buhun Shinkafar ₦150,000 daidai ne a kasuwannin jihohin Adamawa, Kano, Kaduna da Lagos a makon nan da ke mana ban kwana, amma farashin na makon jiya ya sha banban a kasuwannin, an sayi buhun ₦160,000 a kasuwar Mile 12 International Market Legos a satin da ya gabata, amma a makon nan ₦150,000 ne kuɗin buhunta, an samu sauƙin ₦10,000 kenan, haka nan batun yake a kasuwar Karamar Hukumar Girie a jihar Adamawa.
Ita kuwa Shinkafar Bature mai cin tiya 50 ta fi sauki a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, an sayi buhun ₦75,000 a makon nan, amma a makon da ya wuce ₦67,500 ake sai da buhun shinkafa ‘yar Gwamnati.
₦76,-77,000 ake sayar da buhun shinkafar waje a kasuwar Dandume jihar Katsina a satin nan.
Sai kuma kasuwar Mai’adua a jihar Katsina aka saya ₦78,000 a makon nan da ke dab da ƙarewa, amma a makon jiya ₦78-79,000 ake sayar da buhunta.
Shinkafar waje ta fi tsada a kasuwar Dawanau jihar Kano da aka saya ₦85,000 a makon nan, amma a makon jiya ₦87,000 ne kuɗin buhun Shinkafar.
Ita ma dai kasuwar Mile 12 International Market Legos ₦85,000 kuɗin yake a wannan makon, farashin dai bai sauya Tufafi ba da na makon jiya.
₦80,000 daidai ake sayar da buhun shinkafar waje a satin nan a kasuwar Giwa jihar Kaduna.
Farin wake ya fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market Legos da aka saya ₦200,000 daidai a makon nan, amma a makon jiya an sayi buhun ₦185,000 a kasuwar.
A kasuwannin jihohin Kano da Kaduna an sayi buhun farin wake ₦170,000 daidai a makon nan,amma farashin wake a jihohin ya bambanta a makon jiya,₦165,000 aka sai da buhun a kasuwar Giwa jihar Kaduna a makon jiya, yayin da aka sayi buhun ₦155,000 a kasuwar Dawanau Kano a makon jiyan.
A kasuwar karamar hukumar Gombi an sai da buhun farin wake ₦160,000 a makon da ya shude, yayin da a wannan makon aka saya ₦150-160,000.
To a kasuwar Dandume jihar Katsina ₦160,000 har zuwa ₦180,000 ake sai da buhun farin wake a satin nan da ke dab da ƙarewa.
Sai kuma kasuwar Mai’adua jihar Katsina da aka saya ₦165,000 a wannan makon, inda a makon da ya gabata aka sayar kan kuɗi ₦164,000, an samu sassaucin dubu guda kenan a makon nan.
To bari kammala farashin kayan abincin na wannan satin da kuɗin kwalin taliya.
Kwalin taliyar dai ta fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market Legos da ake saidawa ₦16,000 cif a makon nan, yayin da a makon jiya aka sayar da kwalin ₦18,000 daidai, an samu canjin dubu 2 kenan a sati guda.
To a kasuwar Mai’adua jihar Katsina an sayi kwalin taliyar ₦15,500 a makon nan,amma a makon jiya ₦15,300 kuɗin ya ke a kasuwar.
Sai kasuwar Dandume jihar Katsina da aka saya ₦14,000 cif a satin nan.
To a kasuwar Giwa jihar Kaduna ma dai farashin kwalin taliyar ₦14,000 a wannan makon, haka farashin ya ke a makon jiya.
₦13,500 ne ake sayar da kwalin taliya a kasuwar Dawanau jihar Kano a makon nan,bayan da a makon daya shude aka sayar kan kuɗi ₦13,000 cif.
Ita ma dai kasuwar Zamani dake jihar Adamawa ₦13,000 daidai ake sayar da Taliyar Spaghetti a makon nan,haka batun yake a makon daya gabata.
DCL HAUSA A’isha Usman Gebi.