Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 50

Ƴan APC a Arewa ta Tsakiya sun caccaki masu neman a sauke Wike daga Ministan Abuja

0

Kungiyar magoya bayan jam’iyyar APC a yankin Arewa ta Tsakiyar Nijeriya ta yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi wa Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, na yin murabus ko kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauke shi daga muƙaminsa.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a martani ga kalaman Sakataren Jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, inda ya buƙaci Wike ya ajiye aikinsa na minista domin ya mayar da hankali kan rikicin siyasar jihar Rivers.

DCL Hausa ta ruwaito cewa wannan cece-kuce na zuwa ne bayan gargaɗin da Wike ya yi wa Ajibola Basiru kan tsoma baki a rikicin siyasar Rivers, inda ministan ke cikin takaddama da Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara.

A cikin wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar, Saleh Zazzaga, ya fitar, kungiyar ta ce babu dalilin da zai sa a sauke Wike, tana mai jaddada cewa Birnin Tarayya Abuja na cikin yankin Arewa ta Tsakiya, kuma Wike yana aiwatar da aikinsa yadda ya dace.

Aljeriya ta shigar ƙorafi tana ƙalubalantar wasanta da Nijeriya ta yi nasara

0

Hukumar kwallon kafa ta kasar Aljeriya FAF, ta tabbatar da cewa ta miƙa ƙorafi ga hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) da kuma hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) dangane da hukuncin alkalan wasa a wasan da ta buga da Nijeriya.

A wata sanarwa da suka wallafa shafin X na tawagar ƙwallon ƙafar Aljeriya, FAF ta ce ta nemi a fara bincike na musamman domin a fayyace hukuncin da aka ce sun tayar da rigima, tare da ɗaukar matakin da ya dace bisa ƙa’ida.

A cewar FAF, ba ta gamsu da wasu hukunce-hukuncen alkalai a wasan ba, sabkda shakku da rashin gamsuwa da hakan ke haifarwa ga alkalancin wasanni a Afirka.

Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da cibiyar kula da CCTV da ta laƙume Naira biliyan 40 a Lagos

0

Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da cibiyar kula da na’urorin CCTV da ta lakume biliyan 40 a kan gadar Third Mainland da ke birnin Legas, domin ƙarfafa tsaro da kuma rage yawan haɗurra a gadar.

An ƙaddamar da cibiyar ne a ranar Lahadi, inda ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa aikin ya biyo bayan gyare-gyaren manyan gine-gine da aka yi wa gadar tun bayan da gwamnatin Tinubu ta hau mulki a 2023.

Ya ce an fara sanar da shirin ne tun 2025, kuma za a rika sa ido kai tsaye daga cibiyar tare da tilasta bin ƙa’idar gudun wuce sa a ga masu ababen hawa.

CAF na binciken rashin ɗa’a a wasannin kwata-fainal na AFCON 2025 da suka shafi Nijeriya, Aljeriya, Kamaru da Maroko

0

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) ta ƙaddamar da bincike kan zargin rashin ɗa’a daga wasu ’yan wasa da jami’ai a wasannin kwata-fainal na Kofin Ƙasashen Afirka AFCON 2025 tsakanin Kamaru da Maroko, da kuma Aljeriya da Nijeriya.

CAF ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan samun rahotannin rikici da alkalai da kuma cikas da aka samu a wuraren bayan kammala wasanni, kamar yadda sanarwa a shafin yanar gizon CAF ta bayyana a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce hukumar ta tattara rahotannin wasanni da faifan bidiyo da ke nuna yiwuwar halaye da ba su dace ba, tare da tura batun gaban Kwamitin Ladabtarwa domin ci gaba da bincike da ɗaukar mataki idan an samu laifi.

Iran ta shiga rana ta huɗu da katse intanet yayin da ake ci gaba da zanga-zanga

0

An shiga rana ta huɗu da gwamnatin ƙasar Iran ke ci gaba da katse intanet a faɗin ƙasar, a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da ake cewa ita ce mafi girma a Iran cikin sama da shekaru uku.

Kamar yadda gidan talabijin na Channels TV ya ruwaito, ƙungiyar sa ido kan harkokin intanet ta NetBlocks ta bayyana cewa zuwa safiyar Litinin, katsewar intanet ɗin ta kai sama da sa’o’i 84 ba tare da yankewa ba.

Rahotanni sun nuna cewa katsewar na zuwa ne a lokacin da dubban ’yan ƙasar ke ci gaba da fitowa kan tituna domin nuna adawa da manufofin gwamnati, duk da ƙoƙarin da hukumomi ke yi na takaita sadarwa da yada labarai.

Masu sa ido na kasa da kasa na bayyana damuwa cewa katse intanet na iya ƙara ta’azzara take haƙƙin bil’adama, tare da hana duniya samun cikakken bayani kan abin da ke faruwa a Iran a halin yanzu.

‘Yan bindiga sun kakaba wa manoma harajin dubu 50 ga kowace gona a jihohin Kano da Katsina kafin su girbe gonarsu

0

’Yan bindiga da ke tsakanin jihohin Kano da Katsina sun kakaba haraji ga manoma har ₦50,000 a kowace eka ga manoma, musamman masu noman rake, kafin su girbe amfanin gonarsu.

Jaridar The Guardian ta bayyana cewa ’yan bindigar sun kafa sansanoni a Dajin Rugu da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina da kuma Dajin Falgore a karamar hukumar Doguwa a jihar Kano, inda suke karɓar haraji da yi wa manoman barazana.

Rahoton ya nuna cewa manoman da suka ƙi biyan harajin na fuskantar barazana, lalata amfanin gona, da yiwuwar kai musu hari, lamarin da ya tilasta wa da dama barin gonakinsu,kuma yawanci manoman rake ne suka fi fuskantar wannan matsala.

“Amurka za ta kwace Greenland ko ta wane hali” — Trump

0

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka za ta mallaki yankin Greenland ta kowace hanya, yana mai gargaɗin cewa Rasha ko China na iya karɓar iko da yankin idan Amurka ba ta ɗauki mataki ba.

Trump ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, yana cewa Greenland — wacce ke da arzikin ma’adanai — na da muhimmanci ga tsaron Amurka, musamman yadda ayyukan soji na Rasha da China ke ƙaruwa a yankin Arctic.

Shugaban Amurka ya ce zai iya buɗe kofar tattaunawa kan Greenland, yankin da ke da ikon cin gashin kansa a ƙarƙashin Denmark, amma ya jaddada cewa “ko ta wace hanya, Amurka za ta mallaki Greenland.”

Atiku ya zargi Tinubu da tsoratar da masu faɗar ra’ayi kan gwamnatinsa

0

Madugun adawa a Nijeriya Alhaji Atiku Abubakar, ya buƙaci gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta sakin Abubakar Salim Musa (@AM_Saleeeem), wani matashi da aka tsare bisa sukar tabarbarewar tsaro a ƙasar.

Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, bayan kungiyar Amnesty International Nigeria ta sanar cewa an kama Musa ba tare da dalili ba a daren 11 ga Janairu, 2026, kuma ana tsare da shi a gidan yarin Keffi.

A cewar Amnesty International, lamarin na nuni da yadda ’yancin faɗar albarkacin baki ke ƙara fuskantar barazana, musamman ga matasa, inda mutane ke fuskantar barazanar kamawa da tsarewa ba bisa ka’ida ba saboda bayyana ra’ayoyinsu a kafafen sada zumunta.

Atiku ya ce tsare Abubakar Salim Musa abin damuwa ne da ke nuna takurawa ga masu adawa, yana mai cewa laifinsa kawai shi ne sukar tabarbarewar tsaro a Arewacin Nijeriya da ma ƙasar baki ɗaya, yana jaddada cewa maimakon gwamnati ta magance matsalolin tsaro da ake nunawa, ta koma tsoratar da masu sukarta—musamman a fili.

Sabuwar dokar haraji a jamhuriyar Nijar ta haifar da cece-kuce

0

Sabuwar dokar haraji a Nijar ta fara yamutsa hazo tare da barin baya da kura.

Batun cire harajin da ya kama daga kaso daya zuwa 35 cikin 100 na albashin ‘yan kasar shi ne ya fi haifar da cece-kuce.

Dokarr ta tanadi cire CFA 350,000 na haraji ga ma’aikacin da ke daukar milyan guda na CFA a matsayin albashi yayin da za a cire CFA 75,000 ga mai daukan albashin CFA 300,000.

Matsin tattalin arziki da Nijar ke fama da shi ya sa kasar kara tsaurara matakan samun kudaden shiga daga ‘yan kasar, wadanda su ma sun jima suna kukan matsalar rashin kudade kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Jonah Jang ya bukaci Gwamnan Plateau Mutfwang ya sauka daga kujerarsa

0

Tsohon gwamnan Plateau kuma jigo a jam’iyyar PDPn jihar Jonah Jang ya bukaci Gwamna Caleb Mutfwang da ya sauka daga kujerarsa a kuma sake gudanar da zabe.

 

Wadannan kalamai sun biyo bayan ficewar Gwamna Caleb daga jam’iyyar PDP tare da komawa APC mai mulkin Nijeriya.

 

Tsohon gwamnan ya fadi haka ne a wani taron jam’iyyar PDP ta jihar Plateau, inda ya ce tunda gwamnan ya fice daga jam’iyyar da ta ba shi damar samun kujerar, to kamata yayi ya sauka.

 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi na nuna damuwa da tsarin Nijeriya da ya bai wa ‘yan siyasa damar sauya sheka a cikin jam’iyyu, yana mai bayyana hakan a matsayin tarnaki ga tsarin dimukuradiyya.