Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 51

Dalilin da ya sa Buhari ya ba ni minista a gwamnatinsa – Lai Mohammed

0

Tsohon ministan yada labarai da al’adu na Nijeriya Lai Mohammed ya bayyana cewa shafe tsawon lokaci cikin rikon amana, biyayya da kuma hidima ne suka sanya tsohon shugaba Muhammadu Buhari ya ba shi mukamin minista a gwamnatinsa.

 

Lai Mohammed ya bayyana haka ne a cikin sabon littafin da ya kaddamar mai taken ‘Headlines and Soundbites: Media Moments that Defined an Administration’.

 

A cikin littafin da aka kaddamar a ranar 17 ga watan Disambar 2025 a Abuja, Lai Mohammed ya ce marigayi Muhammadu Buhari ya yi jinkiri kafin ya zabo mambobin kunshin gwamnatinsa.

 

Sai dai sakamakon yardar da tsohon shugaban ya masa, ya amince masa da kasancewa cikin kwamitin karbar mulki bayan samun nasara a zaben 2015.

Nijeriya na cikin hadari – Aminu Waziri Tambuwal

0

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya nuna damuwa kan halin da Nijeriya ke ciki, yana mai cewa kasar na cikin hadari.

Tambuwal ya bayyana haka ne yayin taron bikin cikar sa shekaru 60 da haihuwa, inda ya bayyana cewa Nijeriya na bukatar samun hadin kai wajen ceto ta daga halin da ta fada.

Kazalika ya ce a halin yanzu Nijeriya ta sauka daga kan tsarin da shugabannin da suka gabata suka dora ta, lamarin da ya bayyana a matsayin abin damuwa, kamar yadda Channels TV ya wallafa.

Trump ya dauki matakin hana kwace kudaden Venezuela daga asusun Amurka

0

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wani umarni na musamman ‘Executice Order’ da ke nufin hana kotuna ko masu bin bashi kwace kudaden shiga daga sayar da man fetur na Venezuela da ke cikin asusun Ma’aikatar Kuɗi ta Amurka, in ji Fadar White House.

 

Umarnin dai ya yi nuni da cewa matakin zai taimaka wa kasar Venezuela wajen samar da tsaro, zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

 

Wannan ya zo ne kasa da mako guda bayan da sojojin Amurka suka kutsa birnin Caracas tare da yin awon gaba da shugaban Venezuela Nicolas Maduro.

Harin Amurka a Sokoto ya hallaka barayin daji – Jaridar Punch

0

Wani faifan bidiyon da jaridar Punch ta samu ya tabbatar mata da hallaka barayin daji a harin da Amurka ta kai a jihar Sokoto.

 

An yi ajalin da dama daga cikin barayin daji, tare da lalata mafakar su da motocinsu, a wani luguden wuta da rundunar sojin saman Amurka ta kai a Jihar Sokoto a ranar 25 ga watan Disamba, 2025, kamar yadda jaridar ta ruwaito.

 

Bidiyon yadda aikin ya gudana, wanda har yanzu ba a fitar da shi a hukumance ba, amma jaridar ta ce ta kalla a ranar Asabar, ya nuna hare-hare uku dabam-dabam da aka kai kan mafakar barayin daji tsakanin 24 da 25 ga Disamba, 2025.

 

Harin dai ya kasance karkashin wani shirin aikin tsaro na hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Nijeriya da ta Amurka, a yunkurin kawo karshen ayyukan ta’addanci a sassan kasar.

Gwamnatin Nijar ta rushe kungiyoyin agaji na NGO sama da dubu 1 na ciki da wajen kasar

0

A cikin wani kudurin doka ne da ministan cikin gidan Nijar Janar Mohamed Toumba ya dauka na ranar 7 ga watan Janairun nan ya sanar da matakin na rushe sama da kungiyoyi masu zaman kansu dubu daya sakamakon rashin mika takardunsu na bayanan inda suke samun kudadensu da yadda suka kashe su.

A cikin kudurin, ministan ya ce, cikin sama da kungiyoyi 3,000 da aka kididdige a kasar baki daya, 1,809 ne kawai aka amince da su cigaba da ayyukansu a hukumance. Cikin su, 1,684 na cikin gida ne yayin da 125 na ketare ne.

A baya, ministan cikin gidan ya ja hankalin kungiyoyin tare da ba su wa’adin ajiye takardun nasu a ofishinsa

Jam’iyyun siyasa na yankin Greenland sun gargadi Trump cewa ba su son zama Amurkawa

0

Jam’iyyun siyasa a Greenland sun bayyana cewa ba sa son zama ‘yan Amurka, bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya sake nuna yiwuwar amfani da karfi domin kwace yankin Greenland mai arzikin ma’adanai.

A wata sanarwa da suka fitar a daren Juma’a, shugabannin jam’iyyun biyar na majalisar Greenland sun ce makomar yankin dole ta kasance a hannun ‘yan Greenland kadai. Wannan na zuwa ne bayan Trump ya ce Amurka za ta dauki mataki kan Greenland ko suna so ko ba sa so.

Jam’iyyun sun ce, ba sa son zama Amurkawa, ba sa son zama ‘yan Denmark, sun fi son zama ‘yan Greenland, suna masu jaddada cewa su ne kadai ke da hakkin yanke shawarar makomar yankin kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kasashen Denmark da sauran kawayen Turai sun nuna damuwa kan kalaman Trump, duk da cewa Amurka na da sansanin soja a Greenland. Trump dai ya ce mallakar yankin na da matukar muhimmanci ga tsaron Amurka, musamman ganin karuwar ayyukan sojojin Rasha da China a yankin.

Firaministan Denmark, Mette Frederiksen, ta gargadi cewa duk wani hari kan Greenland zai kawo karshen tsarin tsaron NATO. Sai dai, Trump bai dauki ikirarin Denmark da muhimmanci ba kan yankin, yana mai cewa kasancewar Danes sun taba sauka a can shekaru daruruwa da suka wuce ba yana nufin mallakar kasar ba.

‘Yan sanda sun kama wani matashi kan zargin lalata yarinya ‘yar shekara 6 a Bauchi

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani matashi dan shekara 20 bisa zargin lalata da wata yarinya ‘yar shekara shida a karamar hukumar Alkaleri. Rundunar ta ce an kama Bilal Ya’u ne bayan mahaifin yarinyar ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda.

Mai magana da yawun rundunar, SP Nafiu Habib, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 5 ga Janairu, 2026, inda ake zargin matashin ya yaudari yarinyar zuwa wani gini da ba a kammala ba, sannan ya aikata mata fyade. An garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Gwamnati da ke Alkaleri domin duba lafiyarta da kula da ita.

‘Yan sanda sun ce matashin ya amsa laifinsa yayin bincike, tare da bayyana cewa ya taba aikata irin wannan laifi ga yarinyar tun a shekarar 2024, inda a wancan lokacin aka gargade shi kawai. Rundunar ta tabbatar da cewa bincike na ci gaba, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu bayan kammala bincike.

Rundunar Civil Defence ta Jihar Kano ta cire Kwamandanta na Fagge bayan mutuwar wanda ake tsare da shi a ofishin

0

Hukumar tsaro ta Civil Defence a jihar Kano ta sanar da cire Kwamandan ofishin Fagge bayan mutuwar wani mutum da ake tsare da shi a ofishin. Hukumar ta ce an mika jami’in da aka cire tare da dukkan jami’an da ke bakin aiki a lokacin faruwar lamarin ga rundunar ‘yan sanda domin gudanar da bincike.

Mai magana da yawun NSCDC a Kano, Ibrahim Abdullahi, ya ce Kwamandan jihar, Mohammed Hassan Agalama, ya amince da cire SC Amina Musa Kolawale daga mukaminta, tare da nada CSC Bashir Isa Abubakar a matsayin sabon Kwamandan Fagge.

NSCDC ta bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, tana mai jaddada kudirinta na kare mutuncin rayuwa, hakkin dan Adam da bin doka da ka’idojin aiki, yayin da bincike ke ci gaba kan mutuwar wanda aka tsare.

Shugaba Tinubu da Shettima za su kashe sama da Naira Biliyan 9 a tafiye-tafiye da abinci a 2026

0

Kasafin kudin shekarar 2026 ya nuna cewa Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, da Mataimakinsa, Kashim Shettima, za su kashe jimillar naira biliyan 9.36 kan tafiye-tafiye na cikin gida da waje, da kuma abinci da abubuwan liyafa. Wannan na kunshe ne a cikin kundin kasafin kudi na 2026 da Ofishin Kasafin Kasa ya fitar.

Bisa bayanan kasafin, Shugaba Tinubu zai kashe sama da naira biliyan 7 kan tafiye-tafiyensa, ciki har da kusan naira biliyan 6.1 na tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, yayin da aka ware sama da naira miliyan 431 don abinci da kayan liyafa. Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima, kuma zai kashe kusan naira biliyan 1.7 kan tafiye-tafiye da kuma naira miliyan 186 kan abinci da abubuwan liyafa.

Kasafin ya kuma nuna manyan rabon kudi ga sassa daban-daban, inda aka ware naira tiriliyan 3.2 ga tsaro, naira tiriliyan 2.3 ga ilimi, da naira tiriliyan 2.1 ga lafiya da jin dadin jama’a. Majalisar Dattawa ta riga ta amince da kudirin kasafin a karatu na biyu, yayin da ake sa ran ci-gaba da tantancewa kafin amincewa ta karshe.

Shugaba Tinubu ya shiga tsakani a rikicin Wike da Fubara

0

Alamu na nuna cewa Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga tsakani a rikicin siyasa da ke gudana tsakanin Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike. Wata babbar majiyar fadar shugaban kasa ta ce Tinubu ya kira Wike domin tattaunawa kan rikicin, inda ake sa ran za a yi ganawar a wajen Nijeriya.

Rahotanni sun kuma ce Gwamna Fubara ya bar Nijeriya a ranar Alhamis da nufin ganawa da Tinubu a kasar Faransa. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan majalisar dokokin Jihar Rivers, da ake dangantawa da Wike, suka kaddamar da sabon yunkurin tsige Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, bisa zargin aikata manyan laifuka.

Majiyar ta shaida ma jaridar Punch cewa shugaba Tinubu ba zai lamunci rikicin ya kara dagulewa ba, musamman ganin barazanar tabarbarewar tsaro da tasirinsa ga arzikin kasa. Ta ce Tinubu na ganin matakin tsige Fubara a wannan lokaci na iya haddasa rikici a yankin Neja Delta, lamarin da ya sa ya dauki matakin shiga tsakani domin dawo da zaman lafiya.