Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 49

‘Yan sandan sun dakile harin ‘yan bindiga a wani kauyen jihar Gombe

0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta ce ta dakile yunkurin harin ’yan bindiga a kauyen Guda Lamido, da ke garin Kashere a karamar hukumar Akko kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:00 na safiyar Talata, 13 ga Janairu, inda aka samu rahoton cewa wasu ’yan bindiga sun yi yunkurin kutsawa cikin kauyen.

Ya ce jami’an ’yan sanda tare da ’yan banga da mafarauta sun gaggauta kai dauki, inda suka fafata da ’yan bindigar tare da tilasta musu guduwa zuwa daji.

DSP Abdullahi ya ce babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin. Ya kara da cewa an tsaurara sintiri da sa ido domin hana sake aukuwar barazana, tare da yin kira ga jama’a da su cigaba da bai wa hukumomin tsaro hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai kan duk wani motsi na barazana.

WHO ta bukaci gwamnatoci su kara haraji kan lemuka da giya

0

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi kira ga gwamnatocin duniya da su kara haraji sosai kan lemun zaki da kuma barasa, tana mai cewa hakan na da muhimmanci wajen rage mace-mace da cututtuka. WHO ta ce wadannan abubuwan sha suna saukin samu kuma farashinsu ya yi kasa a kasashe da dama, lamarin da ke kara yawaitar kiba, ciwon sukari, cutar daji da raunuka.

Daraktan Janar na WHO, Dr. Tedros Ghebreyesus, ya bayyana hakan yayin wani taro ta yanar gizo a ranar Talata, inda ya ce harajin lafiya na taimakawa wajen rage amfani da kayayyakin da ke cutar da lafiya, tare da rage nauyi a kan tsarin kiwon lafiya. Ya kara da cewa kudin da ake samu daga harajin na ba gwamnatoci damar saka hannun jari a fannin lafiya, ilimi da walwalar jama’a.

Rahoton WHO ya nuna cewa a kalla kasashe 116 sun riga sun kakaba haraji kan lemun zaki, amma wasu kayayyaki kamar ruwan ‘ya’yan itatuwa kashi 100 cikin 100, madarar da aka zuba sukari, da shayin kofi da ake sayarwa a shirye, na tsallake harajin. Haka kuma, rahoton ya ce kasashe 167 na karbar haraji kan barasa, amma farashinsa ya cigaba da sauki tun daga 2022 saboda rashin daidaita haraji da hauhawar farashi da kudin shiga kamar yadda Punch ta ruwaito.

WHO ta jaddada cewa yawan shan lemun zaki na da alaka da kiba, ciwon sukari na nau’i na biyu, cututtukan zuciya da matsalolin hakora, yayin da barasa ke kara hadarin cututtuka ga uwa da jariri, lalacewar lafiyar kwakwalwa da yawaitar hatsari. Hukumar ta kawo misalin Birtaniya, inda aka kakaba haraji kan lemun zaki a 2018, lamarin da ya rage yawan sukari da ake sha, ya samar da fam miliyan 338 a 2024, tare da rage kiba a tsakanin ‘yan mata masu shekaru 10 zuwa 11, musamman a yankunan talakawa.

‘Yan sanda a Katsina sun cafke mutum 3 da abubuwan fashewa

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama mutum uku tare da kwace wasu kayayyakin fashewa a wani samame da ta gudanar bisa umarnin IGP Kayode Egbetokun na ƙara sintiri da aikin leken asiri a manyan hanyoyi.

An kama motar kirar Golf dauke da detonators 6,975 a Koza, karamar hukumar Daura, wadda Jamilu Musa Mai shekaru 40 ke tukawa.

Bincike ya gano cewa ya ɗauko kayan ne daga Kano zuwa Kwangolam, da ke karamar hukumar Mai’adua ta jihar.

Sanarwar ta ce bayan zurfafa bincike, rundunar ta cafke wasu karin mutum biyu Ibrahim Murtala dan shekaru 22 da Sulaiman Muhammad mai shekaru 35, inda aka ƙara kwato detonators 7,500 da jakunkunan gelatine 30½ masu nauyin 2,273.65 kg.

Dukkansu sun amsa laifinsu, kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike, yayin da ake ci gaba da neman sauran waɗanda suka tsere, in ji jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ta Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu.

Tinubu yana nan kalau bai sangauta ba, martanin APC kenan ga Peter Obi

Jam’iyyar APC ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai ɓace ba, kuma bai ki halartar aikinsa ba, duk da maganganun da dan takarar shugaban kasa na Labour Party a 2023, Peter Obi, ya yi kan rashinsa bayyanar shugaban a idon jama’a.

A wata sanarwa da mai magana da yawun APC na Legas, Seye Oladejo, ya fitar, jam’iyyar ta ce Tinubu yana ci gaba da gudanar da manyan al’amuran gwamnati – daga tsare-tsare, tsaro, harkokin diflomasiyya zuwa gyaran tattalin arziki.

Oladejo ya ce shugabanci ba a auna shi da fitowa kullum a kafafen watsa labarai ba, sai dai ingancin matakai da sakamakon ayyukan gwamnati.

A baya bayan nan, Peter Obi ya yi tambaya kan inda Tinubu ys shiga, yana cewa shugaban ya shafe kwanaki 196 a waje a 2025, kuma bai yi jawabi ga ‘yan kasa ba tun December 2025.

Tinubu dai ya isa Abu Dhabi domin halartar gangamin Abu Dhabi Sustainability Week 2026, bayan kammala hutun ƙarshen shekararsa a Turai.

Tinubu ba zai watsar da Wike ya dauki Fubara ba – in ji Fayose

Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba zai yanke alaƙa da Nyesom Wike, Ministan Abuja, saboda rikicin siyasar da ke tsakanin Wike da Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ba.

Fayose ya faɗi haka ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a Arise TV, yana mai cewa Wike ya fi Fubara muhimmanci ga gwamnatin Tinubu, duba da rawar da yake takawa a siyasa da kuma aikinsa a matsayin Ministan Abuja.

A cewarsa, Tinubu ba shi da wani dalili da zai sa ya bar Wike, wanda ya goyi bayan zabensa a Rivers kuma yake taka muhimmiyar rawa wajen ba da nasarori ga jam’iyyar APC.

Maganganun Fayose sun zo ne a daidai lokacin da Majalisar Dokokin Rivers ta fara shirin tsige Gwamna Fubara bisa zargin aikata manyan laifuka, ciki har da rusa majalisar, kashe kuɗi ba bisa ka’ida ba da kin amincewa da ikon majalisar kamar yadda kotu ta umarta.

Rikicin siyasar Rivers ya samo asali tun ƙarshen 2023 sakamakon takaddama tsakanin Wike da Fubara kan ikon jagorantar tsarin siyasar jihar da kuma ikon PDP a tsakaninsu.

Hukumar Hisbah a Yobe ta haramta cudanyar maza da mata a taruka

Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta fitar da sabbin dokoki da suka haramta maza da mata zama kusa da juna a taruka da kuma a cikin motocin haya a fadin jihar.

A cikin sanarwar da aka fitar ranar 6 ga Janairu 2026, wacce shugaban hukumar, Muhammad Yahudi, ya sanya wa hannu, Hisbah ta ce yin “hirarraki tsakanin mace da namiji ta hanyar da ta saba koyarwar addinin Musulunci” ya sabawa doka a jihar.

Mujallar Peoples Gazzete ta ce sababbin matakan sun kuma hada da hana tukin ganganci da cashewa da wasa da motoci a bukukuwan sallah da bikin aure.

Hukumar ta bukaci jama’a da baki da su kiyaye wadannan ka’idoji domin tabbatar da zaman lafiya da kare dabi’un addinin Musulunci a jihar Yobe.

Amurka ta soke fiye da visa 100,000 tun bayan dawowar trump kan mulki

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce an soke sama da visa 100,000 tun bayan dawowar Donald Trump kan mulki, ciki har da kusan visa 8,000 na ɗalibai da visa 2,500 na ƙwararrun ma’aikata.

Gwamnatin ta ce matakan suna cikin sabon tsarin ƙarfafa tsaro da aiwatar da dokokin shige da fice.

Rahoton da DW Afrika ta ruwaito ya ce an fi soke visar ne saboda kuskurensu na tsawaita zama a kasar fiye da izini, tuƙi a yayin maye, kai wa jama’a hari, da kuma sata.

Hukumomin sun ce gwamnatin ta jagoranci korar mutane fiye da miliyan 2.5, abin da suke kallo a matsayin bajinta a tarihin kasar ta Amurka.

Sai dai rahotanni sun ce akwai wasu daga cikin waɗanda aka kora da suna da visa mai inganci, lamarin da ya tayar da ce-ce-ku-ce kan hakkokin ɗan adam da tauye tsarin doka wajen kamewa da korar baki.

Man United na daf da nada Michael Carrick a matsayin mai horaswa na wucin gadi

Manchester United ta cimma matsaya da tsohon ɗan wasanta kuma kocin ta a baya, Michael Carrick, domin ya zama mai horar da tawagar na rikon kwarya har zuwa ƙarshen kakar bana, a cewar rahoton Sky Sports ranar Talata.

Carrick, wanda ya taɓa riƙe United a matsayin mai horaswa na wucin gadi a baya, zai koma Old Trafford domin taimaka wa kulob ɗin ya daidaita wasanni bayan rikice-rikicen da suka addabi ƙungiyar a cikin gida da wajen fili.

Kulob ɗin na fatan sabon rikon kwaryar zai dawo da kwanciyar hankali yayin da ake neman sabuwar mafita ga dogon lokacin da aka kwashe ana tababa a cikinta.

Kudin shigo da man fetur a Nijeriya ya ragu da kashi 54 – CBN

Kudin da Nijeriya ke kashewa wajen shigo da man fetur da aka tace ya ragu matuƙa da kashi 54 cikin 100 cikin shekara biyu, inda ya fadi daga dala biliyan $14.58 a watanni tara na shekarar 2023 zuwa dala biliyan $6.71 a irin wannan lokaci na shekarar 2025.

Rahoton Babban Bankin Nijeriya (CBN), kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, ya nuna cewa kudin shigo da man ya ragu zuwa dala biliyan $11.38 a watanni tara na 2024, kafin ya kara faduwa zuwa dala biliyan $6.71 a cikin watanni tara na 2025.

Binciken kwatance tsakanin cikakken rahoton shekarun 2023 da 2024, da kuma rahoton zangon kashi uku na 2025, ya nuna cewa raguwar kudin na da alaka da karuwar ayyukan tace man fetur a cikin gida, lamarin da ya rage dogaro da shigo da man daga kasashen waje.

Rundunar sojin Nijeriya za ta murƙushe duk wata barazanar tsaro — CDS Oluyede

Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Olufemi Oluyede, ya tabbatar da cewa rundunar sojin Nijeriya za ta murƙushe duk wata barazana ga tsaron ƙasa a ko’ina take, yana mai cewa ba za a yi rangwame ga masu tayar da zaune-tsaye ba.

Janar Oluyede ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin bikin Ranar Tunawa da Sojoji ta 2026, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

Janar Oluyede ya jaddada cewa tsaro shi ne ginshiƙin martabar kowace ƙasa, kuma rundunar sojin Nijeriya za ta ci gaba da aiki ba dare ba rana domin kakkabe ‘yan tada ƙayar baya da sauran barazanar tsaro.

Babban Hafsan Tsaron ya kuma nuna godiya ta musamman ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa abin da ya kira jajircewa da kuma samar da sabbin dabaru da goyon bayan da gwamnatin ke bai wa rundunar sojin ƙasa.