Sunday, April 5, 2026
Home Blog Page 507

Za mu dawo mulkin Kano ba dadewa – Ganduje

Gwamnan Kano mai barin gado Abdullahi Ganduje, PhD
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ce za su bar Gwamnati a jihar na dan wani lokaci amma za su dawo su amshi mulki ba da jimawa ba.
Ganduje ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi lokacin bikin bude aikin sabo titin kwanar Dala a karamar hukumar ta Dala.
“Tabbaas tarihi zai sake maimaita kansa na Dawo-dawo dama wancan Dawo-dawon din ma mu muka sa aka yi ta, Kuma mu muka san dawo-dawo, don haka a wannna lokacin ma kada mu manta da wakar nan ta Dawo-dawo” Inji Gwamna Ganduje.

Daraktan sufuri a Nijar ya halaka kanshi


Daraktan sufuri a jihar Tillaberi ta Jamhuriyar Nijar Adamou Halidou ya halaka kansa, inda ya mutu ta hanyar rataye kansa a saman bishiya.

Adamou Halidou wanda dan asalin garin Dogon Doutchi ne na jihar Dosso ta kasar ya rataye kansa a wata bishiya a ranar Larabar nan.
Daraktan sufuri a Nijar dai, kwantankwacin kwamishina ne a mukaman da ake rabawa a jihohin Nijeriya.