Sunday, April 5, 2026
Home Blog Page 505

An kama barayin da suka saci agwagi da kare a Kano

An kama barayin da suka saci agwagi da kare a Kano
‘Yan sintirin Vigilante na garin Gurungawa dake karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano sun kama matasa hudu da ake zargi da satar wasu agwagi da wani kare.
Kwamandan kungiyar sintirin a garin Abdulhamid Dan’azumi ya ce jami’ansa sun ji motsin matasan da tsakar dare kusan misalin karfe 3 a lokacin da karnuka suka fara haushi a kansu. Bayan jami’an sun isa, suka tarar har sun hallaka kare daya.
Ya ce bayan kama matasan sun amsa laifinsu, kuma an kwace makamai da dama daga wajensu bayan da suka tabbatar da cewa sun dade su na aikata wannan assha.
Daya daga cikinsu, ya sanar cewa sun sa kudi sun sayi karen ne, amma dai agwagin ba na su bane, sun gansu ne suka kwashe suka zuba cikin buhu.

Kotu ta hana a tuhumi Hudu Yunusa-Ari

Kotu ta hana a tuhumi Hudu Yunusa-Ari
Babbar kotun tarayya dake Abuja ta hana hukumar zaben Nijeriya INEC tuhumar kwamishinan zaben da ya ayyana Sanata Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaben Gwamnan jihar Adamawa a zaben 2023.
Mai Shari’a Dotanus Okorowo ya yanke hukuncin hakan, bayan da lauyan Hudu Yunusa-Ari, wato Mr Michael Aondoaka ya bukaci hakan a gaban kotu.
Lauyan Hudu Yunusa-Ari ya shaida wa kotu cewa hukumar zaben INEC ba ta hurumin tuhumarsa har sai kotun sauraren kararrakin zaben ta sanar da makomar dakataccen kwamishina a hukumar zaben.

Amai da gudawa bai kama Alhazan Kano ba – NAHCON

Amai da gudawa bai kama Alhazan Kano ba – NAHCON
Hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON ta musanta rade-radin da ake yadawa cewa amai da gudawa ta barke a daya daga cikin masaukan Alhazan jihar Kano dake birnin Makka na Saudi Arabia.
Shugaban tawagar likitocin hukumar NAHCON Dr Usman Galadima ya sanar da hakan a Makka, Saudi Arabia, inda ya ce gurbataccen abinci ne wasu daga cikin Alhazan suka ci daga hannun ‘takaru’ ya lalata musu ciki.
Ya ce an bude wani cibiyar kula da lafiya ta wucin-gadi a wurin da lamarin ya faru inda ake kula da lafiyar kusan Alhazai 9 da abin ya shafa bayan da suka ci dambu.
Dr Usman ya ce tun daren Asabar, bayan da aka tura tawagar likitoci a wurin, sun shawo kan lamarin, har ma an sallami wadanda suka kamu.
Shugaban tawagar likitocin ya ce duk da shawarwarin da aka ba Alhazan na su guji yame-yamen abinci musamman wanda ba a tabbatar da sahihancinsa ba, amma suka yi kunnen-kashi suka ci.

Wata jarumar fim ta mutu

Wata jarumar fim ta mutu
Jaruma a masana’antar shirya fina-finan Nollywood Sidikat Odukanwi ta mutu bayan fama da rashin lafiya.
‘Yar kabilar Yoruba Sidikat ta mutu, bayan fama da rashin lafiyar da ta tilast mata daina fitowa a fim na tsawon lokaci.
Diyar mamaciyar, Bisi Aisha ce ta sanar da mutuwar mahaifiyar tata da aka fi sani da Iyako Oko.
‘Yar asalin jihar Osun, an haifi Iyako a shekarar 1960.

Farashin fetur ya kusa linkawa a kasashen Kamaru, Benin da Nijar bayan cire tallafin man a Nijeriya

Farashin fetur ya kusa linkawa a kasashen Kamaru, Benin da Nijar bayan cire tallafin man a Nijeriya

Bayanan da majiyar DCL Hausa ta Daily Trust ta samo sun nuna cewa farashin litar man fetur ya kusa linkawa a kasashen Kamaru, Benin da Jamhuriyar Nijar bayan da Nijeriya ta sanar da cire tallafin man fetur din.
Bayanan sun ce samun fetur din cikin rahusa, ya sa ‘yan kasuwa na ‘sumogal’ dinsa zuwa kasashe makwabta daga Nijeriya har a wuce da shi Sudan wadansu lokutta.
Hakan dai na ba ‘yan Nijeriya wahala wajen samun isasshen man da za su yi amfani da shi, da wasu lokuttan akan shiga matsalar karancinsa. Bayanai dai sun tabbatar da cewa cire tallafin man fetur din ya haddasa barazana ga tattalin arzikin kasashen makwabta da yanzu haka harkokin ‘bumburutu’ suka yi kasa.
Binciken jaridar ya gano cewa ana farashin ya koma CFA700 ko CFA800 a kasar Benin sabanin CFA450 da ake sayarwa kafin a cire tallafin man a Nijeriya.
A baya, ana sayar da litar fetur a Nijeriya kan kudi N195, a kasashe makwabta kuwa ana sayar da litar man kan kudi CFA508 kwantankwacin Naira 381. A haka ne ‘yan ‘sumogal’ ke amfani da damar domin fitar da shi, don a samu kazamar riba.

Majalisar Kano ta musanta yunkurin dawo da Sarki Sanusi

Majalisar dDkokin jihar Kano ta musanta shirin tsige sarakunan jihar biyar tare da mayar da Khalifa Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano.

Wasu daga cikin kafafen yada labarai na shafukan sada zumunta sun ruwaito a ranar Larabar makon nan cewa Majalisar jihar za ta sake duba batun masarautun da kudirin gyaransu na shekarar 2023 wanda shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini, memba mai wakiltar mazabar Dala ya karanta ranar Alhamis.

Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba jim kadan bayan kammala zaman majalisar, dan majalisa Lawan Hussaini, ya bayyana labarin a matsayin labarin bogi.

Rashin lantarki ya sa daliban jami’ar ABU daina karatu

Harkokin karatu sun samu tangarda a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya yayin da dalibai suka shafe kusan wata daya zaune a gida sakamakon matsalar wutar lantarki da jami’ar ta shiga.
A ranar 15 ga watan Mayun da ya gabata ne hukumar da ke dakon hasken lantarki ta yanke hanyar lantarki ta jami’ar sakamakon bashin da suke bin jami’ar.
Jaridar Daily trust ta gano cewa hukumar gudanarwar jami’ar ta biya kamfanin Kaduna Electric Naira miliyan 40 daga cikin kudin wutar lantarki da ake bin su.
Sai dai duk da haka kamfanin na Kaduna Electric bai mayar da lanyin lantarkin makarantar ba.

Gwamnatin APC ta janyo cece-kuce a Sokoto

 

Ta leko ta koma shi ne abin da wasu ma’aikata suka shaida
sakamakon sauyin gwamnati da aka samu jihar Sokoto. A cikin kasa da sa’o’I 24
da tsohon gwamna Tambuwal na jam’iyyar PDP ya mika mulki ne dai, sabuwar
gwamnatin jihar  ƙarƙashin jãgorancin
gwamna Ahmad Sule na jam’iyyar APC ta ɗauki matakin  sõke daukar ma’aikata da ƙãrin girma da
gwamnatin Aminu Waziri Tambawal ta yi, lamarin da ya sanya da dãma daga cikin
waɗanda aka ɗauka aikin cikin halin ni ƴãsu. Daya daga cikin mutanen da tsohon
gwamna Tambuwal ya dauka aiki a jihar ya shaida wa DCL Hausa yadda suka ji da
kamun ludayin sabuwar gwamnmatinwacce ya zarga da jefa rayuwarsa cikin kunci.         

Ita dai sabuwar gwamnatin ta ce irin wadannan ayyuka da
tsohon gwamnan PDP Tambuwal ya rarraba wa mutanen da ta kira “shafaffu da mai”
abu ne da aka yi cikin kuskure wanda ba za ta lamunta ba, a don haka ne ta ce
duk wani karin girma ko daukar aiki da Tambuwal ya yi bayan zaben gwamnan jihar
daga ranar 19 ga watan Maris zuwa na ranar da aka mika mata mulki to ta warware
shi. Sai dai kakakin PDP a jihar ta Sakkwato Hassan Sahabi Sanyinnawal yace
abin da sabuwar gwamnatin jihar ta yi bīta da ƙulli na siyasa ne kawai.                                   

Duk ƙoƙarin da nayi, har tsawon kwanaki biyu, dan jin ta
bakin ɓangaren sabuwar gwamnatin ta jihar Sakkwato, dan jin dalilin soke daukar
aiki da kuma ƙarin girma ga wasu ma’aikata yaci tura.

Wani mai sharhi kan lamurran siyasa, Dakta Umar Adamu na
jami’ar jihar Gombe yace, irin wannan mataki kan iya haddasa gãba a tsakaninin
alumma.

 Da alama dai irin
wannan fashin baki da tirjiyar da sabbin am’aikatan da aka dauka ke nunawa ba
za su sanya sabuwar gwamnatin ta jam’iyyar APC dawo da ma’aiaktan na Sokoto
bakin aiki ba, inda baya ga korar wadannan malamai, sabon gwamna Ahmed Sule ya
umurci a soke sababbin sunayen da tsohon gwamna Tambuwal ya rada wa wasu manyan
makarantun jihar.

DCL Hausa, Umar Ibrahim

Mulki da mace mataimakiyar gwamma na tayar da kura a Adamawa

Fintiri da Binani

 

A karon farko mutanen jihar Adamawa sun fara sanin muhimmanci ko akasin haka na samun mace mataikiyar gwamna. Nasarar Gwamna Ahamdu Umaru Fintiri wadanda ya dauki mataimakiya Farfesa Kaletapwa Farauta ta biyo bayan rudanin siyasa da ya tilasta gudanar da zaben har sau biyu tare da jinkiri wajen bayyana wanda ya yi nasara a sakamakon zargin wuce gona da iri da kwamishinan zabe na wancan lokacin Hudu Yunusa Ari  ya yi.

Duk da cewa a karshe wannan cece-kuc,  an samu zababben gwamna da kuma mataimakiya, a yanzu wata dambarwa siyasa da ta kunno kai ita ce yadda wasu ‘yan jihar suka zura ido suga yadda za ta kaya a wa’adi na biyu na Gwamna Fintiri sakamakon macen da ya dauka a matsayin mataimakiya. … Na cikin manyan ‘yan’yan jam’iyyar APC a jihar Adamawa da suka yi kokarin ganin Aishatu Ahmad Binani ta yi nasara, ya shaida wa DCL Hausa cewa a yanzu dai za a iya mutanen jihar sun ki cin biri sun ci dila.

Wannan zargi da fargaba da APC ke nunawa kan kamun ludayin mulkin namjij da mace, bai hana jam’iyarr PDP mai mulki a Adamawa ba, ganin alfanun zabin da suka. Jam’iyyar ta PDP ta ce samun wannan hadaka ta jinsi zai ba gwamnatin jihar damar sanin yadda za ta mulki jihar cikin sauki ganin yadda yanzu mace take a matsayin mataimakiyar gwamna.

Duk dai wannan musayar yawu da ‘yan siyasa ke  yi suna yi ne don al’ummar jihar, sai dai kuma mutane sun kasa kunne tare da zuba idon ganin yadda za ta kaya a wannan mulki “samfurin shinkafa da wake” karon farko a tarihin jihar.

Kungiyoyin mata na ganin shigar da mata a harkar shugabanci abu ne da zai kawo wa jihar Adamawa ci gaba ta bangarori dabam-dabam. Asma’u Suleiman Surko dake Rajin kare hakkin mata ta  Shaidawa DLC HAUSA cewa samun mace a wannan muƙamin babban Nasara ce ga al’umma.

Kawo yanzu dai jama’a a jihar Adamawa cike suke da zumudin ganin sauyin da gwamnatin Gwamna Ahmadu Fintiri za ta nuna wa jihar da ya banbanta da wa’adinsa na farko wanda ya yi mulki da namiji a matsayin mataimaki.

 

DLC HAUSA,  A’isha Usman Gebi daga Yola

Mutanen Kaduna na fargabar rusau daga Uba Sani

Ayyuka na farko-farko da Uba Sani ya fara yi a matsayin sabon gwamnan jihar Kaduna a ranar 29 ga watan Mayu, sa’o’I kadan bayan da aka rantsar da shi, su ne sanar da sauya sunan sanannen titin nan na Rabbah Road zuwa Malam Nasir El-Rufa’i road, abin da ya razana wasu da suka yi fatan sabon gwamnan ya kauce wa manufofin tsohon gwamnan da aka yi wa lakabi da “mai rusau”. An zargi El-Rufai dai da bijirowa mutanen jihar da manufofi masu tsauri a zamanin mulkinsa. To sai dai kuma wasu na ganin hakan ba wani abu ba ne illa godiya da girmamawa ga tsohon gwamnan, ganin irin tsayin dakar da Elrfufai ya yi wajen ganin Uba Sanin ya zama gwamna.

Cikin manyan alkawurran da gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi wa jama’ar akwai tabbatar da tsaro, alkinta tattalin arziki da janyo masu zuba jari sai kuma hada kai tare da tafiya da kowa ba tare da nuna banbancin bangaranci addini, kabila ko kuma siyasa ba.

Batun siyasa na ci gaba da dumama a jihar ta Kaduna, musamman la’akari da yadda kotun sauraren kararrakin zabe ta fara zaman sauraren karar da jam’iyyar PDP ta shigar, tana Kalubalantar sakamakon zaben, wanda ta ce an yi aringizo, da kuma amfani da kudade wajen wannan zabe, baya ga tafka magudi.

Da bambancin kuri’u kasa da dubu 12 ne dai APC ta lashe zaben gwamna, abin da watakila ke ba PDP kwarin gwiwar samun nasara a kotu. 

To ko me ‚yan adawa a jihar zasu ce a game da wannan zaman shari’a da aka fara da kuma kamun ludayin gwamnatin da Uba Sani a Kaduna, Muhammad Dan Auta mai bai wa shugaban jam’iyyar PDP a jihar a Kaduna shawara ta fannin yada labarai, ya ce da alamu gwamnatin bata shigo da kafar dama ba, kasancewar ta shiga a cewarsa ta hanya mai cike da kazanta.

Da alama wadannan kalamai basu yiwa gwamnatin da magoya bayanta wani tasiri ba, don kuwa a cewar su basu da ko dar cewa sune zasu yi nasara a kotun,Muhammad Sani Akilu Idris shi ne mataimakin tsohon gwamna El-Rufa’I kan harkokin siyasa, yace akwai alamun haske idan aka lura da kamun ludayin gwamnan jihar cikin mako guda.

A yayin da jam’iyyu APC da PDP ke ci gaba da tabka zazzafar siyasa bisa kamun ludayin gwamnatin APC, mutanen jihar sun shaida wa DCL Hausa abubuwan da suka fata da kuma zullumi daga gwamnatin gwamna Uba Sani

Jihar Kaduna da ake yiwa kallo da cibiyar arewacin Nijeriya na da matukar tasiri wannan ta sa siyasarta ke daukar hankali, duk da dai jama’ar jihar na ganin akwai jan aiki gaban sabon shugaba Uba Sani.

 

DCL Hausa, Yacouba Umaru Maigizawa