Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 54

Sabbin dokokin haraji karin nauyi ne ga ma’aikata da talakawa – Shugaban NLC

0

Shugaban Kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), Comrade Joe Ajaero, ya bayyana damuwa kan sabuwar dokar haraji, yana mai cewa an yi watsi da bukatar ma’aikata yayin tsara dokar, lamarin da ya kara nauyi ga masu karamin karfi. Ya ce harajin da ya shafi albashin mafi karanci ba adalci ba ne kuma yana tilasta wa talakawa karin nauyi.

Ajaero ya gargadi gwamnati da kada ta cigaba da aiwatar da dokar ba tare da gyara ba, yana mai cewa ci-gaba da hakan zai iya rage amincewar jama’a da kawo barazana ga tsarin dimokuradiyya. Ya ce dokar tana nuna cewa ma’aikata da talakawa sun kasance a waje yayin yanke hukunci mai tasiri a rayuwarsu.

Ajaero ya jaddada cewa dimokuradiyya ba ta tsaya ga zabe kawai ba; tana bukatar mutunta doka, inganta hukumomi, da gwamnati mai hidima ga al’umma baki daya. Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake duba dokar domin tabbatar da adalci ga kowa.

Datti Baba- Ahmed ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban Nijeriya a 2027

0

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, Sanata Datti Baba-Ahmed, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2027. Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wani taro da jam’iyyar ta gudanar a sakatariyarta ta kasa da ke Abuja.

Baba-Ahmed ya ce burinsa na tsayawa takara ba ya da alaka da ficewar tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi, zuwa jam’iyyar ADC. Ya jaddada cewa tun kafin zaben 2023 yake da burin tsayawa takarar shugaban kasa, yana mai cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba shi dama duk da addininsa da kabilarsa.

Hakazalika ya ce zai bi doka da ka’idojin jam’iyya da na INEC kafin fara kamfen. Shugaban jam’iyyar Labour Party na kasa, Julius Abure, ya yaba masa bisa ci-gaba da kasancewa cikin jam’iyyar duk da rade-radin sauya sheka bayan ficewar Peter Obi.

Babu wani gwamna da ke da ikon juya akalar APC – Farfesa Yilwatda

1

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce babu wani gwamna ko mutum guda da ke da iko da jam’iyyar APC. Ya bayyana cewa dukkan manyan matakai da ake dauka a jihohi ana tsara su ne daga matakin kasa, ba a bar su a hannun jihohi ba.

Yilwatda ya fadi hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin Sunset na gidan rediyon Jay FM a Jos, Jihar Filato. Ya ce APC jam’iyya ce da ke aiki da tsari, ba da son rai ko motsin zuciya ba, yana mai jaddada cewa gwamna, sanata, shugaban karamar hukuma ko shi kansa shugaban jam’iyya ba su da cikakken iko a kanta.

Shugaban ya kara da cewa APC ta guji kafa majalisar amintattu domin kauce wa rikici, yana mai cewa jam’iyyar mallakin al’umma ce kuma mutane su ne amintattun APC, sabanin wasu jam’iyyun da wasu tsirarun mutane ke rike da dukkanin tsarinsu.

An yi yunkurin juyin mulki a kasar Burkina Faso

0

Gwamnatin soja ta Burkina Faso ta ce ta dakile wani sabon yunkurin juyin mulki da aka shirya domin hambarar da shugaban kasar na rikon kwarya, Kanal Ibrahim Traoré. Ministan tsaro, Mahamadou Sana, ya bayyana cewa an dakile shirin ne a daren Asabar sakamakon aikin kwararrun jami’an leken asiri.

Gwamnatin ta zargi tsohon shugaban rikon kwarya, Paul-Henri Damiba, da shirya yunkurin, inda ta ce an tsara hallaka shugaban kasar da wasu manyan jami’an soja da fararen hula, ta hanyar harbi ko dasa bam a gidansa. Damiba dai shi ne Traoré ya kifar da shi a juyin mulkin watan Satumban 2022.

Ministan ya kara da cewa an gano shirin ne bayan samun wani bidiyo da ke nuna masu kitsa yunkurin suna tattauna shirin, yana mai zargin cewa an samu tallafin kudi daga kasar Ivory Coast, tare da shirin kai hari kan sansanin tashi da jiragen drone kafin kasashen waje su iya shiga tsakani kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

PDP za ta gana da Atiku da Peter Obi gabanin zaben 2027 – Emmanuel Ogidi

0

Jam’iyyar PDP ta bayyana shirin ganawa da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, da wasu manyan jiga-jigan siyasa a Nijeriya domin farfado da jam’iyyar.

Shugaban PDP na Kudu maso Kudu, Emmanuel Ogidi ya ce, jam’iyyar ta riga ta ziyarci tsofaffin shugabanni, Olusegun Obasanjo da Ibrahim Babangida, yayin da tana shirin tattaunawa da sauran masu ruwa da tsaki a fagen siyasa, ciki har da Obi da Atiku kamar yadda Channels TV ta ruwaito

A baya-bayan nan, kwamitin gudanarwa na PDP ya gana da tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, wanda ya tabbatar da kasancewarsa mai cikakken goyon bayan jam’iyyar yayin da PDP ke shirin fuskantar zabuka a Ekiti da Osun, har zuwa zaben 2027.

‘Yan sanda sun ceto yara 76 tare da kawar da yunkurin kai hari a jihar Kaduna

0

Rundunar ‘yan sanda a Nijeriya ta kawar da yunkurin kai hari da sace yara a Kasuwan Magani, Jihar Kaduna, inda suka ceto yara maza da mata guda 76 ba tare da wani rauni ba.

A cikin sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Kakakin yada labarai na ‘Yan Sanda, CSP Benjamin Hundeyin, ya ce an samu sahihin bayanan sirri a ranar 5 ga Janairu 2026 cewa wasu yan bindiga na shirin kai hari da sace yara daga motocin da ke wucewa a yankin.

A yayin aikin, an kama mutane uku da suka hada da Jonathan John mai shekaru 25; Oliver Magaji, 27; da Bitrus Sawaba, 23.

Binciken farko ya nuna cewa, an kama su ne suna shirin kai yaran wasu sassa na kasar domin aikin yara da sauran ayyukan gida. Yaran da aka ceto suna cikin koshin lafiya a hedkwatar rundunar har sai a same iyayensu ko masu kula da su.

Rundunar ta tabbatar da fara cikakken bincike don gano cikakken abin da ya faru da kuma gano duk wani mai hannu a ciki kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

‘Yan sandan sun sake jaddada kudurinsu na kare rayuka da dukiyoyi, tare da rokon jama’a su bayar da sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa wajen dakile aikata laifuka.

Trump ya gargadi Republican da su yi nasara a zaben tsakiyar wa’adi gudun kar a tsige shi

0

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce dole ne jam’iyyar Republican ta lashe zaɓen tsakiyar wa’adin Majalisar Dokoki a 2026, in ba haka ba, jam’iyyar Democrat na iya neman tsige shi kan shugabancin.

Trump ya yi wannan gargadin ne yayin jawabi ga ‘yan majalisar Republican a wani taro a Washington inda ya ce rashin samun rinjaye a majalisar zai iya hana manufofin gwamnati gudana kuma ya fallasa hukumarsa ga bincike, inda ya bukaci ‘yan Republican su daina rikice-rikicen ciki.

Shugaban na Amurka ya kuma yi kira ga jam’iyyarsa su wayar da kan masu zaɓe kan manufofin Republican da suka shafi jinsin maza da mata, kiwon lafiya da ingancin zaɓe, musamman ga masu fama da hauhawar farashin rayuwa.

Hakazalika, ya yi hasashen cewa jam’iyyar Republican za ta samu nasara mai girma a zaɓen tsakiyar wa’adi mai zuwa, duk da zargin da ake masa na wasu batutuwa da suka shafi gaskiya a Washington.

Babu haraji ga kudin da ke ajiye a asusun banki- Shugaban cibiyar kwararrun haraji ta Nijeriya

0

Shugaban Cibiyar Kwararrun Haraji ta Nijeriya reshen Abuja, Ben Enamudu, ya bayyana cewa babu wani haraji da ake karɓa kan kuɗin da ke cikin asusun banki a ƙarƙashin sabon tsarin haraji. Ya ce abin da ake samu kawai shi ne kuɗin hatimi na naira 50 idan an tura kudi, ba harajin ajiyar kuɗi ba.

Ya ce kuɗin hatimin yana shafar tura kuɗi daga asusu zuwa wani asusu, inda mai aikawa kaɗai ke biyan kuɗin. Albashi da tura kudi ƙasa da Naira 10,000 ba sa biyan kuɗin, haka kuma canja-wuri tsakanin asusu a banki ɗaya ba ya janyo cajin hatimi. Sai dai idan canja-wurin ya ratsa banki zuwa wani, ko da asusun mutum ɗaya ne, za a biya kuɗin.

Enamudu ya ƙara da cewa sabon tsarin harajin ya tanadi kariya ga masu ƙaramin ƙarfi, inda muhimman kayayyaki da ayyuka kamar abinci na yau da kullum, magunguna, kiwon lafiya da ilimi ke nan a keɓe daga harajin VAT, tare da wasu sauƙi a fannin gidaje.

Ganga Miliyan 30 zuwa 50 na man kasar Venezuela za a sayar domin amfanin Amurka – Donald Trump

0

Farashin danyen mai ya kara faduwa a ranar Laraba bayan shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Venezuela za ta mika wa Amurka ganguna miliyan 30 zuwa 50 na man fetur, lamarin da ya girgiza kasuwannin makamashi na duniya.

Trump ya ce man za a sayar da shi a farashin kasuwa, kuma kudin za su kasance karkashin kulawar Amurka, abin da masana ke ganin ya rage fargabar karancin mai da kuma yiwuwar takaita samarwa daga Venezuela kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Masu sharhi sun ce kasuwar mai tuni tana da wadatar kaya, musamman bayan yarjejeniyar OPEC na kara yawan samar da mai, wanda hakan ke kara matsin lamba ga farashin.

Nijeriya na biyan tallafin lantarki kusan tiriliyan 2 a duk shekara

0

Rahotannin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) sun nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta kashe naira tiriliyan 1.98 a matsayin tallafin wutar lantarki cikin watanni 12, daga Oktoba 2024 zuwa Satumba 2025.

A cewar rahoton, an kashe Naira biliyan 471.69 a zangon karshe na 2024, Naira biliyan 536.4 a zangon farko na 2025, Naira biliyan 514.35 a zangon na biyu, sannan Naira biliyan 458.75 a zango na uku na 2025 kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

NERC ta bayyana cewa wannan tallafi na biyo bayan kasancewar kudin wutar lantarki a kasa da kudin da ake kashewa wajen samar da ita, wanda ya tilasta wa gwamnati rufe gibin ta hanyar tallafi. Rahoton ya ce ana aiwatar da tallafin ne kai tsaye ta hanyar rage kudin da kamfanonin rarraba wuta ke biya wa Hukumar Sayen Wuta ta Kasa (NBET).

Duk da karin kudin wuta ga masu amfani da Band A tun Afrilun 2024, nauyin tallafin bai ragu ba. Hakan ya sa Ministan Wuta, Adebayo Adelabu, da masana ke jaddada cewa tsarin tallafin wuta ba mai dorewa ba ne, tare da kiran a mayar da tallafin ne ga talakawa kadai.