Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 53

‘Yan Nijeriya 408,000 ne ke gudun hijra a Nijar, Kamaru da Chadi ta dalilin matsalolin tsaro in ji MDD

0

Fiye da ‘yan Nijeriya 408,000 ne ke ci gaba da gudun hijira a kasashen Nijar, Kamaru da Chadi, sakamakon matsalar rashin tsaro da ya addabi yankin Arewa maso Gabashin ƙasar tun shekarar 2009, a cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNHCR.

Rahoton UNHCR na shekarar 2025 ya bayyana cewa Jamhuriyar Nijar ce ke dauke da mafi yawan ‘yan Nijeriya da ke gudun hijira a can, inda ake da mutane 258,653, yawancinsu na zaune a yankin Diffa, kusa da kananan hukumomi kamar Kuluk, Gashua, Machina da Malkotan.

Kasashen Kamaru na dauke da ‘yan gudun hijira 126,892, mafi yawansu na sansanin Minawao da ke yankin Far North, yayin da Chadi ke dauke da mutane 21,636, musamman a yankin Lac Province da Baga Sola.

‘Yan Majalisar dokokin Kano sun goyi bayan shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ficewa daga NNPP zuwa APC

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bayyana goyon bayanta ga shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ficewa daga jam’iyyar NNPP, tana mai cewa rikicin shugabanci da shari’o’in kotu da ke addabar jam’iyyar na iya jefa kujerarsa cikin barazana.

Shugaban masu rinjaye na Majalisar, Hon. Lawan Hussaini, ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kano ranar Alhamis, inda ya ce ci gaba da zama a NNPP ya zama hadari ba ga gwamna kaɗai ba, har da sauran zababbun jami’an gwamnati a jihar.

Daily Trust ta rawaito Hussaini, na cewa NNPP na fama da rarrabuwar kawuna a shugabanci da kuma tarin shari’o’in kotu, lamarin da ke janyo rashin tabbas kan sahihancin tsarin jam’iyyar da tsayar da ’yan takara a zabuka masu zuwa.

Dangote ya janye korafin zarge-zargen cin hanci da ya shigar a hukumar ICPC kan Farouk Ahmed

Dangote ya janye korafin zarge-zargen cin hanci da ya shigar a hukumar ICPC kan Farouk Ahmed, tsohon shugaban hukumar NMMPRA

Jaridar Daily Trust ta ce attajirin na Afirka, Dangote, ya yi haka ne bayan da wata hukumar gwamnatin Nijeriya ta fara duba wadannan zarge-zarge na facaka da dukiyar kasa da ya yi wa wannan tsohon babban jami’in hukumar da ke da ruwa da tsaki kan sha’anin man fetur.

Sai dai ICPC ta jaddada cewa wannan mataki ba zai dakatar da binciken da take yi ba.

Nijeriya na bin kasashen Nijar, Togo da Benin tulin bashin kudin lantarkin da ya kai N25bn – NERC

Hukumar kula da lantarki ta Nijeriya NERC ta ce, kasar na bin kasashen Togo, Nijar da Benin bashin dala $17.8m — kimanin N25bn na lantarkin da aka ba su a ƙarƙashin yarjejeniyoyin kasashen waje.

A cikin rahoton rubu’i na uku na 2025, hukumar NERC ta bayyana cewa kamfanonin sayar da lantarki sun tura wa kasashen uku takardar biyan kuɗi har dala $18.69m na lantarkin da suka sha a lokacin, amma suka biya $7.125m kawai, lamarin da ya bar ragowar bashi na $11.56m.

Daga yanzu Venezuela kayan da Amurka ke samarwa za ta rika saya kadai – Donald Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ƙasar Venezuela za ta riƙa sayen kayayyakin da aka ƙera a Amurka kaɗai, ta hanyar kuɗaɗen da take samu daga yarjejeniyar man fetur da Amurka.

Trump ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social ranar Laraba, 8 ga Janairu, 2026, inda ya ce Venezuela za ta ɗauki Amurka a matsayin babban abokiyar hulɗar kasuwancinta, yana mai cewa wannan zai taimaki al’ummar Venezuela.

A cewarsa, kayayyakin da Venezuela za ta rika saye sun haɗa da amfanin gona na Amurka, da magunguna, na’urorin kiwon lafiya, da kuma kayan aikin wutar lantarki da cibiyoyin makamashi domin inganta tsarin wutar ƙasar.

Wasu ‘yan Jam’iyyar APC sun nemi Tinubu da ya sauke ministan Abuja Nyesom Wike daga mukaminsa

Wasu shugabanni a jam’iyyar APC, ƙarƙashin APC Leaders Forum da Tinubu/Shettima Solidarity Movement, sun buƙaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta cire Nyesom Wike daga muƙamin ministan Abuja, bisa zargin rashin biyayya, ayyukan da suka sabawa da kuma barazana ga haɗin kan ƙasa.

A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 7 ga Janairu, 2026, wadda aka aike wa Shugaba Tinubu ta hannun shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ƙungiyoyin sun ce halayen Wike ba su dace da ci gaba da zama a matsayin minista ba.

An mika wasiƙar ne a ranar Laraba, yayin da mambobin ƙungiyoyin suka gudanar da zanga-zangar lumana a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja, inda suka ce manufarsu ita ce kare martabar jam’iyya, dimokuraɗiyya da kuma ajandar gwamnatin Tinubu.

Gwamnatin Nijeriya za ta bai wa ‘yan wasan Super Eagles alawus-alawus na AFCON

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa an kammala dukkan matakai tsaruka domin biyan alawus-alawus na wasannin Super Eagles a gasar AFCON 2025, inda ta ce ‘yan wasan za su fara ganin kuɗaɗen a asusunsu kafin ranar Juma’a.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, 8 ga Janairu, 2026, karamar Ministar kuɗi,Doris Uzoka-Anite, ta ce za a biya kuɗaɗen zai a asusun ‘yan wasa na ƙasashen waje tun daga Alhamis din nan zuwa Juma’a.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa ‘yan wasan Super Eagles sun yi barazanar ƙin tafiya zuwa birnin da za a buga wasan daf da na kusa da na ƙarshe,sakamakon rashin biyan alawus-alawus ɗin da suke bi.

Majalisar dokokin Rivers na shirin tsige Gwamnan jihar

Majalisar Dokokin jihar Rivers ta fara shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara tare da mataimakiyarsa Ngozi Oduh, bisa zargin aikata manyan laifuka da saba wa kundin tsarin mulkin ƙasa.

Rahotanni sun nuna cewa a zaman majalisar da aka yi ranar Alhamis, 8 ga Janairu, 2026, wanda aka watsa kai tsaye ta gidan talabiji na Channels,wanda Shugaban Majalisa Martins Amaewhule, ya jagoranta, Shugaban masu rinjaye, Hon. Major Jack, ya karanta takardar zarge-zarge da manyan laifuka da ake yi wa Gwamna Fubara.

‘Yan majalisa 26 ne suka sanya hannu kan takardar, inda suka ce zarge-zargen sun shafi saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Shugaban majalisar, Amaewhule, ya ce za a miƙa wa Gwamna Fubara takardar sanarwar zarge-zargen cikin kwanaki bakwai masu zuwa, kamar yadda doka ta tanada.

Ministan yada labarai ya nesanta kansa da wani rubutu mai taken “Malagi 2027”

0

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Nijeriya, Mohammed Idris, ya nesanta kansa daga wani rubutu na siyasa mai taken “Malagi 2027”, wanda ke hasashe kan zaben gwamnan Jihar Neja na 2027. Ma’aikatar ta ce an wallafa rubutun ne ba tare da sanin ministan ko amincewarsa ba, lamarin da ya kai ga dakatar da mataimakin da ya rubuta shi.

A wata sanarwa da Mataimakin Ministan kan Harkokin Watsa Labarai, Rabiu Ibrahim, ya fitar a ranar Laraba, an ce ministan ya bukaci jama’a su yi watsi da rubutun gaba daya. Sanarwar ta jaddada cewa ministan na mayar da hankali ne kacokan kan aikinsa na gwamnati, ba tare da tsoma kansa cikin maganganun siyasa ba.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an fara bincike kan lamarin tare da dakatar da mataimakin da ya rubuta rubutun nan take. Haka kuma, ta jaddada cewa Ministan da Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, na da kyakkyawar alaka ta fahimtar juna, inda ta ce duk wata jita-jita kan siyasar 2027 na iya lalata wannan hadin kai.

Wasu tsoffin ‘yan sanda sun roki Tinubu da ya sa a mayar da su aiki bayan tilasta yi musu ritaya

0

Wasu tsoffin jami’an rundunar ’yan sandan Nijeriya sun sake kira ga rundunar da ta bi hukuncin Kotun Kwadago ta Kasa, wadda ta bayar da umarnin a mayar da su bakin aiki bayan an yi musu ritaya ba bisa ka’ida ba. Jami’an, da ke cikin rukuni na kwasa-kwasan horaswa na 33, 34 da 35, sun ce an yi musu ritaya ne tun kafin su cika wa’adin shekaru 35 da doka ta tanada.

Kotun, karkashin Mai shari’a Oyewumi Oyebiola, ta umurci Sufeton Janar na ’Yan Sanda, Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda da Sakataren Rundunar su mayar da jami’an bakin aiki, tare da hana tilasta musu ritaya. Sai dai duk da hukuncin da aka yanke tun ranar 19 ga Afrilun 2022, har yanzu ba a aiwatar da umarnin kotun ba.

A wata wasika da lauyansu, Adetoye Adejola, ya rubuta wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, jami’an sun roki shugaban Nijeriya ya shiga tsakani domin tabbatar da bin hukuncin kotu. Sun ce kin aiwatar da hukuncin na ci gaba da tauye hakkinsu tare da barazana ga tsarin shari’a da kuma tsaron cikin gida na ƙasa.