Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 55

Ramaphosa ya yi Allah-wadai da kama Maduro da Amurka ta yi

0

Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta ɗauka na kama Shugaban ƙasar Venezuela, Nicolas Maduro.

Ramaphosa ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, inda ya ce Afirka ta Kudu na tare da al’ummar Venezuela kan abin da ya faru.

Ramaphosa ya kuma yi kira ga kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya UNSC da ya ɗauki mataki cikin gaggawa domin cika aikinsa na samar da zaman lafiya da tsaro a duniya.

Sojoji sun ceto mutane shida da aka sace a Kaduna

Dakarun rundunar Operation Fansar Yamma sun samu nasarar ceto mutane shida da aka sace a wani sumame da suka gudanar a yankunan Kajuru da Kujama na jihar Kaduna.

Mukaddashin Mataimakin Daraktan yada labarai da huldaa da jama’a na rundunar sojin Nijeriya, sashe na 1, Laftanar Kanal Shuaib Umar, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X a ranar Talata.

Ya ce an gudanar da aikin ceton ne a ranar 5 ga Janairu, 2026, a wani bangare na hare haren da aka kai a ƙananan hukumomin Chikun, Kajuru, Kachia, Kagarko, da kuma yankunan kan iyaka da Kauru.

Bayan fafatawar, sojojin sun ci gaba da binciken yankin tare da samun nasarar ceto mutane shida da aka sace.

‘Yan bindiga sun sace mutane da dama a wasu hare hare da suka kai a Katsina

Wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hare-hare kan wasu al’ummomi a jihar Katsina, inda suka sace mutane da dama.

Shaidun gani da ido sun shaida wa gidan talabijin na Channels ta wayar tarho a ranar Talata cewa harin ya faru ne a daren Litinin, bayan da ’yan bindigar suka mamaye yankunan, suka kwashe tsawon lokaci suna aikata ta’asa da firgita mazauna wuraren.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa ’yan bindigar sun fara kai hari a Unguwar Alhaji Barau, daga bisani suka wuce Gidan Dan Mai-gizo da Gidan Hazo, duk a Unguwar Na’alma da ke karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Duk da haka, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba, yayin da har yanzu ba a tantance adadin mutanen da aka kashe ko waɗanda aka sace ba.

Abba ne jagoranmu na kasa ba Kwankwaso ba, in ji mataimakin shugaban jam’iyyar NNPP na kasa

Mataimakin Shugaban NNPP na shiyyar Arewa maso Yamma,Sani Danmasani, ya bayyana cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, shi ne jagoran jam’iyyar NNPP, ba Rabiu Musa Kwankwaso ba.

Danmasani ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, inda ya ce bisa tanadin kundin tsarin jam’iyyar NNPP, Gwamna Abba Kabir ne jagoran jam’iyyar kasancewar shi kaɗai ne gwamnan da jam’iyyar ke da shi a halin yanzu.

Jaridar Daily Nigeriyan ta rawaitk Dan Masani ya ce Sanata Rabiu Kwankwaso ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaɓen 2023 ne kawai, bisa wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin jam’iyyar da kungiyar Kwankwasiyya, wadda ta ƙare bayan kammala zaɓen.

Danmasani ya ƙara da cewa wasu manyan mambobin Kwankwasiyya, ciki har da Kwankwaso, an kore su daga jam’iyyar NNPP bisa zargin aikata ayyukan da suka saɓa wa manufofin jam’iyya.

Liam Rosenior ya zama sabon mai horas da kungiyar Chelsea

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta cimma yarjejeniya da Liam Rosenior a matsayin sabon kocin kungiyar.

Rosenior ya tabbatar da hakan da kansa inda ya ce yana dab da karɓar ragamar horaswa a ɗaya daga cikin manyan kungiyoyin ƙwallon ƙafa a duniya, yana mai bayyana farin cikinsa da wannan dama.

Hakan ya zo ne bayan da Chelsea ta raba gari da mai horaswa Enzo Maresca, bayan fuskantar matsin lamba kan irin tafiyar da kungiyar ke yi karkashin jagorancin sa.

Muna da ƙarfin soji da za mu yaƙi Amurka idan faɗan ƙasa ne – Shugaban ƙasar Uganda

0

Shugaban ƙasar Uganda, Yoweri Museveni, ya ce ƙasarsa na da ƙarfin soja, masu ƙwarewa da gogewa da za su iya kareta idan aka yi yaƙi ta ƙasa, har ma da manyan ƙasashe kamar Amurka.

 

Museveni ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan abubuwan da suka faru a ƙasar Venezuela, inda ya ce har yanzu bai fahimci ainihin abin da Shugaban Amurka, Donald Trump, da Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, ke faɗa a kai ba.

 

Da yake jawabi a wani taron matasa a birnin Kampala a ranar Lahadi, Museveni ya ce yana ci gaba da nazari kan lamarin domin fahimtar abubuwan da ke faruwa,ya kuma ce sojojin Amurka sun fi ƙarfi wajen yaƙi ta sama da ruwa, amma ba su da karfi wajen yaƙi ta ƙasa.

Shugaban na Uganda ya kara da cewa yaƙin ƙasa na da haɗari ga Amurka, domin a irin wannan yaƙi, na fuskantar juna kai tsaye na basu matukar wahala.

Matatar mai ta Dangote ta musanta rufe aikinta

Matatar man Dangote ta karyata jita-jitar da ke yawo cewa ta dakatar da aiki, tana mai cewa aiki na ci gaba da gudana yadda ya kamata ba tare da tsaiko ba.

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar 5 ga Janairu, 2026, ya bayyana cewa matatar na samar da lita miliyan 40 zuwa 50 na man fetur (PMS) a kullum, gwargwadon bukatar kasuwa.

Sanarwar ta kara da cewa, a ranar 4 ga Janairu, matatar ta samar da lita miliyan 50 na PMS, inda aka fitar da lita miliyan 48, tare da adadin ajiyar da ke iya wadatar Nijeriya na sama da kwanaki 20.

Kamfanin ya ce ayyukan gyaran na yau da kullum da ake yi a wasu sassa ba sa shafar yawan man da ake samarwa, kuma ana ci gaba da tace man PMS, Dizal da Jet A-1 a dukkan sassan da ke aiki.

Dangote Petroleum Refinery ta ce farashin man fetur daga matatar (ex-gantry) na nan daram a ₦699 kan kowace lita, kuma ana sayarwa ga ‘yan kasuwa da masu sayen kaya masu yawa ba tare da nuna wariya ba.

Kamfanin ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da labaran karya, su kuma dogara da ingantattun bayanai, yana mai jaddada kudurinsa na tabbatar da wadataccen man fetur, daidaiton farashi.

Hauhawar farashi ta sa ’yan Nijeriya rage kashe kudi da Naira tiriliyan 14 – CBN

0

Wasu bayanai da babban bankin Nijeriya CBN ya fitar, sun nuna cewa yawan kudaden da ‘yan Nijeriya ke kashewa wajen gudanar da gidajensu ya ragu da akalla Naira tiriliyan 14.

 

Bayanan da bankin ya fitar a shekarar 2024, sun nuna cewa an samu wannan sauyi ne sakamakon hauhawar farashin kayayyakin amfanin yau da kullum.

 

Jaridar Punch ta ruwaito cewa hauhawar farashin a shekarar ta 2024 na da alaka ta kai tsaye da cire tallafin man fetur, sai kuma rashin samun tsayayyen farashi a kasuwar canjin kudade.

 

Hakan dai ya tilastawa ‘yan Nijeriya da dama mayar da hankali kan gabatar da bukatun da suka zama wajibi gare su, bayan hakura da wasu abubuwan, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Shugaba Trumph na Amurka ya yi barazanar daukar matakin soji kan Columbia

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar kaddamar harin soji kan kasar Colombia, bayan wani farmakin soji da ya kai a Venezuela.

Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce yiwuwar kai farmakin soji kan Colombia tunani ne mai kyau,yana zargin gwamnatin kasar da hannu wajen safarar hodar iblis zuwa Amurka.

Trump ya yi wannan furuci ne bayan wani farmaki da sojojin Amurka suka kai a Venezuela, wanda ya janyo cece kuce a duniya tare da tayar da hankula.

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a hatsarin Kwale – kwale a Yobe ya karu zuwa 29

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya faru a karamar hukumar Nguru ta jihar Yobe ya ƙaru daga 25 zuwa 29, kamar yadda hukumomin jihar suka sanar.

Sakatare a hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Yobe (YOSEMA), Dakta Mohammad Goje, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Damaturu a ranar Litinin.

Ya ce an ƙara gano gawawwaki huɗu daga cikin kogin, yayin da mutane tsakanin 8 zuwa 10 har yanzu ake neman su, ya ƙara da cewa fasinjoji 13 da suka jikkata a hatsarin an ba su magani kuma an sallame su daga asibiti.