Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 58

An takaita amfani da kafafen sada zumunta a Guinea

0

Guinea ta takaita amfani da TikTok, YouTube da Facebook yayin jiran sakamakon zaben shugaban kasa.

Gwamnatin Guinea ta takaita shiga shafukan sada zumunta na TikTok, YouTube da Facebook, yayin da kasar ke jiran sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a Lahadin da ta gabata.

Kungiyar sa ido kan harkokin intanet ta NetBlocks ta bayyana cewa an samu tsaiko da katsewa wajen shiga wadannan shafuka ta manyan kamfanonin sadarwa na Orange da MTN, lamarin da ya shafi miliyoyin masu amfani da intanet a kasar.

Hukumomi a Ghana sun kama masu zambar yanar gizo

0

DW Afrika ta rawaito cewa a wani sumame na hadin gwiwa da aka kai a yankin Accra na kasar, jami’an hukumar tsaron yanar gizo ta Ghana, ’yan sanda da hukumar shige da ficen kasar suka gudanar aka yi wannan kame.

Hukumomin sun bayyana cewa ana zargin mutanen da aikata laifuka da suka haɗa da damfara, zambar yanar gizo da satar kuɗade.

Haka kuma an kama wani ɗan kasar ta Ghana da ake zargin ya ba da hayar wajen zama ga kusan mutum 100 daga cikin waɗanda ake zargi.

‘Yan sanda sun kama wani da ya yi ajalin dan uwansa kan bashin Naira 4000

0

Mutumin mai suna Lekan Lasisi ya shiga hannun ’yan sanda a jihar Ogun bayan da wata rigima tsakaninsa da ɗan’uwansa kan bashin Naira 4,000 ta yi sanadin mutuwar ɗan’uwan.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a Unguwar Abule Tuntun, cikin karamar hukumar Odeda ta jihar Ogun.

Bincike ya nuna cewa rikicin ya fara ne bayan da Lasisi ya fusata, sakamakon haka ɗan’uwan nasa ya fara fito da adduna, shi kuma wajen kare kansa ya fitar da bindiga, inda ya ce bindigar ya harba ta ne ba tare da niyya ba, harsashin kuma ya samu ɗan’uwansa wanda daga bisani ya rasu.

Kotu ta tasa keyar Malami, matarsa da dansa gidan yarin Kuje kan zargin badakalar sama da Naira biliyan 8

0

Kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami SAN tare da ɗansa da ɗaya daga cikin matansa a gidan gyaran hali na Kuje.

Mai shari’a Justice Emeka Nwite ne ya bayar da umarnin a ranar Talata, 30 ga Disamba 2025, bayan sauraron hujjoji daga lauyoyin wadanda ake tuhuma karkashin jagorancin Joseph Daudu SAN da kuma lauyan masu gabatar da ƙara na EFCC Ekele Iheneacho SAN.

Malami, tare da ɗansa Abubakar Malami da matarsa Asabe Bashir na fuskantar tuhumar badakalar kuɗi guda 16, wadda hukumar EFCC ta shigar a kansu.

EFCC na zargin cewa wadanda ake tuhumar sun haɗa kai a lokuta daban-daban wajen canza salo na kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya, waɗanda darajarsu ta kai Naira biliyan 8.7.

Babu asarar rayuwa bayan fashewar wani abu a asibitin Bagudo ta Kebbi – Ƴan sandan Nijeriya

0

Rundunar ’yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da fashewar wani abu a babban Asibitin Bagudo da ke karamar hukumar Bagudo ta jihar a Talatar nan.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta jihar SP Bashir Usman ya fitar a Birnin Kebbi, inda ya tabbatar cewa rundunar ta ƙillace wajen bayan jin ƙarar fashewar da aka da asubahin Talata, 30 ga Disamba, 2025, a harabar asibitin.

Ya ce rundunar tsaro ta hadin gwiwa wacca ta kunshi ’yan sanda, sojoji da jami’an sa-kai ta garzaya wurin cikin gaggawa dan tabbatar da tsaro.

Kazalika ya bayyana cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoton ana ci gaba da gudanar da bincike kan musabbanin faruwar lamarin.

Yahya Bello zai tsaya takarar Sanatan Kogi ta Tsaki

0

Tsohon Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanatan Kogi ta Tsakiya a zaben shekarar 2027.

Yahaya Bello ya sanar da hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai fadar Basarake Ohinoyin Ebiraland, inda ya gana da sarakunan gargajiya, shugabannin addini da jagororin al’umma daga yankin.

Jaridar Punch ta rawaito cewa an wallafa bidiyon ziyarar da kuma sanarwar tsayawa takarar a shafinsa na Facebook a ranar Litinin.

APC a jihar Kebbi ta dakatar da shugaban karamar hukuma

0

Jam’iyyar APC a jihar Kebbi ta dakatar da shugaban karamar hukumar Birnin Kebbi kuma shugaban Ciyaman ALGON na jihar Dahiru Nayaya daga jam’iyyar bisa zargin aikata rashin da’a da saba wa ka’ida.

Dakatarwar na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mataimakin shugaban APC na yankin Kebbi ta Tsakiya Abubakar Bello ya aikewa manema labarai.

A cewar takardar, jam’iyyar ta dauki matakin ne bayan samun rahotannin binciken cikin gida, wadanda suka danganta Dahiru Nayaya da yin wasu ayyukan da jam’iyyar ta ce suna barazana ga hadin kai da martabar APC.

Tsohuwar Firaministar Bangladesh Begum Khaleda Zia ta rasu

0

Tsohuwar Firaministar ƙasar Bangladesh Begum Khaleda Zia ta rasu da safiyar Talatan nan tana da shekaru 80 kamar yadda jam’iyyarta ta Bangladesh Nationalist Party BNP ta sanar.

Jam’iyyar BNP ta bayyana cewa Khaleda Zia ta rasu ne da misalin karfe 6:00 na safe jim kaɗan bayan kammala sallar Asuba a wani asibiti da ke birnin Dhaka, babban birnin ƙasar Bangladesh.

Marigayiyar ta shafe shekaru tana fama da matsananciyar rashin lafiya tare da zaman gidan yari, sai dai duk da haka, a watan Nuwamba da ya gabata ta bayyana aniyarta ta shiga yakin neman zaben da aka shirya yi a Fabrairun 2026, wanda zai kasance zaɓe na farko tun bayan kifar da tsohuwar abokiyar hamayyarta Firaminista Sheikh Hasina a bara.

Babban layin wutar lantarkin Nijeriya National Grid ya fadi

0

Babban layin wutar lantarki na ƙasa ya fadi Litinin din nan, lamarin da ya jefa ’yan Nijeriya da dama cikin duhu bayan da manyan tashoshin samar da wuta suka daina aiki.

Jaridar PUNCH, ta rawaito cewa wakilinta cewa layin wutar ya faɗi kusan ƙarfe 3:00 na rana, a daidai lokacin da samar da wutar lantarki ya ragu matuƙa a fadin ƙasar.

Bayanan da aka samu sun nuna cewa samar da wuta ya kai kimanin megawatt 4,800 tun da safiyar Litinin, amma daga bisani ya faɗi ƙasa zuwa megawatt 139 zuwa ƙarfe 3:00 na rana.

‘Yan bindiga sun kai hari a wani kauye na jihar Kebbi

0

’Yan bindiga sun kai hari a kauyen Gebbe da ke karamar hukumar Shanga a jihar Kebbi, inda rahotanni ke nuna an rasa rayuka yayin da wasu da dama suka jikkata.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa al’ummar yankin sun ce harin ya faru ba zato ba tsammani, lokacin da ’yan bindigar suka shigo kauyen suka fara harbe-harbe babu kakkautawa, lamarin da ya tilasta mazauna wurin tserewa zuwa dazuzzuka domin tsira.

Rahotanni sun ce cewa har zuwa wannan lokaci ba a tantance adadin waɗanda suka mutu ko suka jikkata ba, saboda girman harin da kuma yadda jama’a suka watse zuwa wurare daban-daban bayan harin.