Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 57

Sojoji sun dakile harin ‘yan bindiga a wasu kauyukan Kano

Rundunar sojin Nieriya ta ce ta dakile yunkurin harin ‘yan bindiga da suka yi kokarin shiga wasu al’ummomi a Shanono na Jihar Kano, bayan gumurzu mai tsanani da ya dauki tsawon lokaci.

Artabun ya fara ne a daren Alhamis zuwa wayewar Juma’a, inda aka gwabza fada a kauyukan Yankwada, Babanduhu da wasu makwabtansu a yankin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga News Agency of Nigeria, kakakin rundunar sojin Nijeriya a Kano, Zubair Babatunde, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi kokarin kutsawa kauyukan ne ta kan babura, suna harbe-harbe ba kakkautawa.

Babban jami’in ya kara da cewa harin ramuwar gayya ne, biyo bayan asarar da ‘yan bindigar suka yi a makon da ya gabata, lokacin da sojoji suka yi musu mummunan luguden wuta a wani artabu da suka yi da su.

‘Yan bindiga sun sace wani basarake da dansa a jihar Kwara

0

Fargaba ta mamaye zukatan al’ummar Aafin da ke yankin Ile Ere a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara, bayan da ’yan bindiga suka sace Sarkin Aafin, Oba Simeon Olaonipekun, tare da guda daga cikin ’ya’yansa mai suna Olaolu.

 

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa an sace sarkin ne a daren Laraba yayin da wasu ’yan bindiga kusan takwas suka kai hari fadarsa, inda suka rika harbi ta ko ina kafin su kutsa kai ciki.

 

Wani ɗan uwa daga cikin iyalan sarkin da ke fadar a lokacin harin ya ce maharan sun zo ne kai tsaye domin daukar sarkin da matarsa, ganin hakan yasa suka rufe kofofin gidan amma da ‘yan bindigar suka fuskanci haka suka rika harbi ta ko ina.

 

Har zuwa wannan lokaci dai babu wata sanarwa daga mahukunta kan lamarin, sai dai al’ummar sun bukaci daukar mataki cikin gaggawa don ceto wadanda aka sace.

An sallami gwarzon dan wasan damben ‘Boxing’ Anthony Joshua daga asibiti bayan samun sauki

An sallami gwarzon dan wasan damben ‘Boxing’ Anthony Joshua daga asibiti bayan an tabbatar da cewa ya samu sauki kuma zai ci gaba da murmurewa a gida, bayan hatsarin mota da ya rutsa da shi a jihar Ogun.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Legas, Gbenga Omotoso ya fitar, ta bayyana cewa an sallami Joshua ne a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce Joshua na cikin alhini sakamakon rashin abokansa biyu na kusa, Lateef Ayodele da Cina Gami, da suka ce ga garinku nan a hatsarin da ya faru.

Sanata Remi Tinubu ta jinjinawa juriyar ‘yan Nijeriya tare da bayyana kwarin gwiwa kan 2026

Uwargidan shugaban Nijeriya Sanata Remi Tinubu ta jinjinawa juriyar ‘yan kasar tare da bayyana kwarin gwiwa kan 2026.

A cikin saƙon sabuwar shekara da ta aikewa ‘yan Nijeriya ta shafinta na X a ranar Alhamis, Sanata Oluremi Tinubu ta ce zuciyarta cike take da jin dadi yayin da ƙasar ke shiga sabuwar shekara da kyakkyawan fata na samun makoma mai kyau.

Ta ce shekarar da ta wuce ta sake nuna juriya da ƙwazon ‘yan Nijeriya, inda ta bayyana su a matsayin jarumai, masu basira da ƙirƙira, tare da imani na samun gobe mai kyau.

Turkiyya da Somaliya sun sanya hannu kan yarjejeniyar fara hakar man fetur da iskar gas a tekun Somaliya

DW Afrika ta ruwaito cewa bayan zaman tattaunawa tsakanin shugabannin ƙasashen biyu Recep Tayyip Erdogan da Hassan Sheikh Mohamud a birnin Istanbul, sun bayyana cewa wannan shi ne karon farko a tarihin Somaliya da za a fara hakar man fetur a tekun ƙasar.

Karkashin yarjejeniyar, Turkiyya za ta tura jirgin hakar mai zuwa tekun, kuma ana sa ran aikin zai taimaka a ɓangaren makamashi ga Somaliya, tare da yin tasiri ga tattalin arziƙin kasar.

Gwamnatin Nijeriya za ta kara mayar da hankali kan tsaurara matakan kudi da gyaran haraji a 2026 – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa shekarar 2026 ta zo da sabon mataki mai karfi na bunkasar tattalin arziki, inda ya ce gyare-gyaren da gwamnatinsa ta aiwatar a 2025 sun fara haifar da sakamako mai kyau.

A cikin sakon sabuwar shekara, Shugaba Tinubu ya ce duk da kalubalen tattalin arzikin duniya, Nijeriya ta samu ci gaban ma’aunin tattalin arziki na GDP sama da kashi 4 cikin 100, saukar hauhawar farashi zuwa kasa da kashi 15, kudin Naira sun fara daidaituwa, da kuma karuwar jarin kasashen waje.

Shugaban ya ce gwamnatin tarayya za ta kara mayar da hankali kan tsauraran matakan kudi da gyaran haraji a 2026, domin gina tattalin arziki mai dorewa.

Ya bayyana cewa sabon tsarin haraji zai rage nauyin haraji da kudade ga jama’a, tare da samar da kudin shiga da za a yi amfani da su wajen gina hanyoyi, wutar lantarki, ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman ababen more rayuwa.

Shugaba Tinubu ya kuma ce kasuwar hannayen jari ta Nijeriya ta samu gagarumar riba, alamar karuwar amincewar masu zuba jari.

A bangaren tsaro da walwalar al’umma, Shugaban ya jaddada cewa ci gaban tattalin arziki ba zai yiwu ba tare da zaman lafiya ba. Ya ce hukumomin tsaro za su kara hadin gwiwa da kasashen duniya domin dakile ta’addanci da ‘yan bindiga. Haka kuma, gwamnatin za ta aiwatar da shirin Renewed Hope Ward Development Programme domin tallafa wa akalla mutane miliyan 10 a fadin kananan hukumomi, ta hanyar noma, kasuwanci da sarrafa albarkatu. Shugaban ya kammala da kiran hadin kai, yana mai cewa gina kasa nauyi ne na kowa da kowa.

Bankunan Nijeriya za su fara cire harajin N50 daga masu tura kudi ta banki da suka kai N10,000

0

Daga 1 ga watan Janairun, 2026, bankunan Nijeriya za su fara cire harajin N50 kan duk wanda ya tura kudi da ya kai ₦10,000 ko sama da haka, bisa tanadin sabuwar dokar haraji (Tax Act) da aka kafa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa bankunan kasuwanci irinsu UBA da Access Bank, ne suka fara sanar da kwastomominsu game da aiwatar da dokar kafin fara aiki da ita.

A cewar UBA, sabon tsarin ya canza daga yadda ake yi a baya, inda za a rika cire N50 sau ɗaya kacal kan kowane harkar tura kudi da ta kai adadin da aka kayyade.

Bankin ya ƙara da cewa wanda ya tura kuɗi ƙasa da N10,000 ba za a caje su ba, haka kuma masu albashi an keɓance su daga harajin.

KasashenNijar, Burkina Faso da Mali sun sanar da kakaba wa ’yan Amurka takunkumin biza

0

Kasashen Nijar,Burkina Faso da Mali sun sanar da kakaba takunkumin biza ga ’yan ƙasar Amurka, a matsayin martani ga dokar hana shige da fice da Gwamnatin Amurka ta kakaba wa wasu ƙasashe, mafi yawansu a nahiyar Afirka.

TRT Afrika ta rawaito cewa Burkina Faso ta bayyana cewa za ta aiwatar da irin matakin sanya takunkumin biza ga Amurka kamar yadda ta ɗora wa ’yan ƙasarta.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Burkina Faso ta jaddada cewa ƙasar na mutunta kowace ƙasa da kuma daidaito a hulɗar ƙasashe, tare da bayyana cewa tana buɗe ƙofofi ga haɗin gwiwa da dukkan abokan hulɗarta, muddin ana mutunta juna da muradun ɓangarorin biyu.

Kazalika kuma ƙasar Mali ta sanar da ɗaukar irin wannan mataki, inda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce daga yanzu za ta ɗora wa ’yan Amurka sharuddan daidai da waɗanda Amurka ke kakaba wa ’yan Mali,ita ma ƙasar Nijar ta shiga cikin jerin ƙasashen da suka nuna martani kan wannan dokar.

Sojoji sun ceto mutane 1,023, tare da kwato bindigogi 189 Arewa maso Yammacin Nijeriya

0

Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewa ta ceto mutane 1,023 da aka sace, tare da kwato bindigogi AK-47 guda 189 da alburusai 4,338, a sumame daban-daban da ta gudanar a Arewa maso Yammacin Nijeriya cikin shekarar 2025.

Babban kwamandan runduna ta 8, Sakkwato, Manjo Janar Ibikunle Ajose, ya bayyana hakan yayin bikin ba da kyaututtuka da aka gudanar a ranar Laraba a birnin Sakkwato.

Manjo Janar Ajose ya ce nasarorin sun samu ne ta hannun rundunae Operation FANSAN YAMMA, wanda ke yaki da ta’addanci da ’yan bindiga a yankin.

Ya ƙara da cewa daga cikin nasarorin akwai kwace babura 305 da ’yan bindiga ke amfani da su, dawo da dabbobi 4,123 da aka sace, da kuma hallaka wasu manyan shugabannin ’yan bindiga.

Sabbin dokokin haraji za su fara aiki a 1 ga Janairu 2026 — Tinubu

0

Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da cewa sabbin dokokin haraji za su fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2026, kamar yadda aka tsara tun da farko. Dokokin, ciki har da waɗanda suka fara aiki a ranar 26 ga Yuni, 2025, an bayyana su a matsayin wata dama ta musamman wadda ake samu sau ɗaya a ƙarni domin gina tsarin kuɗaɗen ƙasa.

A cikin wata sanarwa da Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya sanya wa hannu, ya jaddada cewa dokokin ba wai an ƙirƙire su ne domin ƙara haraji ba, illa dai domin gyara tsarin haraji gaba ɗaya, daidaita dokoki, da kare mutuncin ‘yan ƙasa tare da ƙarfafa alaƙar amincewa tsakanin gwamnati da jama’a. Ya kuma buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki su goyi bayan matakin aiwatarwa da aka shiga yanzu.

Shugaban ƙasar ya ce duk da hayaniyar da ake yi kan zargin sauye-sauye a wasu sassan dokokin, babu wata babbar matsala da aka tabbatar wadda za ta hana ci gaba da gyaran. Ya tabbatar da cikakken bin doka da oda, tare da alkawarin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da Majalisar Dokoki domin warware duk wata matsala da ka iya tasowa, yana mai tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnati za ta ci gaba da aiki bisa muradin jama’a domin samar da tsarin haraji da ke tallafa wa cigaba.