Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 59

Gwamnatin Nijeriya ta tara sama da Naira Tiriliyan 8 daga harajin VAT da kuma aika kudi ta banki a cikin 2025

0

Gwamnatin Nijeriya ta tara sama da Naira tiriliyan 8 daga harajin VAT da kuma aika kuɗi ta banki a tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamban 2025 kamar yadda asusunta nuna.

Binciken jaridar Daily Trust ya nuna cewa an tattara Naira tiriliyan 7.69 daga harajin VAT, yayin da Naira biliyan 403.68 suka fito daga aika kudade ta banki da ‘yan kasa suka yi.

Gwamnati ta tattara Naira biliyan 771.86 a watan Janairu, amma kudin ya ragu zuwa Naira biliyan 654.45 a Fabrairu, sannan ya ƙara raguwa zuwa Naira biliyan 637.61 a watan Maris.

A watan Afrilu kudin ya ƙaru kadan zuwa Naira biliyan 642.26, sannan ya tashi zuwa Naira biliyan 742.82 a watan Mayu na shekarar ta 2025.

Gwamnan Zamfara zai yi karin albashi ga Malaman Addini

0

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sanar da shirin ƙara albashi ga limaman Juma’a 11,300 da malaman addinin Musulunci a faɗin jihar, inda sabon tsarin zai fara aiki daga Janairu 2026.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke ganawa da Malaman addini.

Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta walwala da yanayin malamai da limamai a jihar.

A cewarsa, gwamnatin jihar na kashe Naira miliyan 81.8 a kowane wata wajen biyan alawus-alawus ga limamai, malamai da masu tsaftace masallatai.

Ya ce shirin ya biyo bayan shawarar kwamitin da gwamnan ya nada inda ya ba da shawarar a kara albashinsu.

Sojojin sama sun tarwatsa maboyar ’yan bindiga tare da ajalin wasu da dama a Zamfara

0

Rundunar sojin saman Nijeriya ta bayyana samun gagarumar nasara bayan kai hare-hare na musamman kan maboyar ’yan bindiga a jihar Zamfara, inda aka hallaka da dama daga cikinsu tare da tarwatsa sansanoninsu.

Daraktan yada labaran rundunar Air Commodore Ehimen Ejodame ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ya ce hare-haren sun gudana ne a ranar Lahadi a ƙarƙashin Operation Pansar yamma bayan samun bayanan sirri daban-daban.

A cewarsa, an kai harin ne a Turba Hill da kuma sansanin Kachalla Dogo Sule da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara waɗanda aka bayyana a matsayin manyan maboyar ’yan bindiga da ke da alaƙa da hare-haren da suka faru a yankin Arewa maso Yamma.

Dan wasan Damben UFC Anthony Joshua ya tsira, daga wani hatsari a jihar Ogun

Shahararren ɗan dambe Anthony Joshua ya tsira daga wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Makun, jihar Ogun, inda mutane biyu suka rasa rayukansu.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe a ranar Litinin 29 ga Disamba 2025 a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Bincike ya nuna cewa motar da Anthony Joshua ke ciki ta yi karo da babbar mota da ke tsaye a hanya, a yayin da ake ci gaba da bincike kan abin da ya janyo hatsarin.

Wani shaidan gani da ido, Adeniyi Orojo ya ce Anthony Joshua ya samu raunika ƙanana, amma mutane biyu daga cikin motar sun mutu nan take.

Kalaman ‘yan adawa kan tafiyar Tinubu Turai na nuni da rashin sanin tsarin mulki – APC

0

Jam’iyyar APC ta bukaci jam’iyyun adawa su daina magana marar amfani kan ziyarar da shugaba Tinubu ya kai ƙasashen Turai.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta a jihar Legas Seye Oladejo ya fitar a Litinindinnan yayin da yake mayar da martani ga sukar da jam’iyyar ADC ta yi kan tafiyar shugaban kasa.

Oladejo ya ce kalaman ’yan adawar na nuna rashin fahimta kan tsarin mulki na zamani da diflomasiyyar ƙasa da ƙasa.

Wike ya musanta zargin cewa yana goyon bayan Tinubu a boye

0

Ministan Abuja Nyesom Wike ya musanta zargin da wasu ke yi cewa yana goyon bayan Tinubu a ɓoye, yana mai jaddada cewa matsayarsa ta siyasa a fili take kuma ba ta taɓa canzawa ba.

Wike ya yi wannan bayani ne yayin da ya ke mayar da martani kan wasu kalamai da aka danganta da gwamnan jihar Rivers Siminalaye Fubara, wanda ya bayyana cewa wasu ’yan siyasa na yin yarjejeniya a boye.

A farkon watan Disamba gwamna Fubara ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC, bayan wata ganawa ta sirri da Shugaba Tinubu a Abuja, matakin da wasu ke ganin wata dabara ce ta siyasa gabanin babban zaɓe mai zuwa.

Wasu ‘yan majalisa sun bukaci a dakatar da dokar haraji

0

‘Yan majalisar wakilai marasa rinjaye sun nuna bukatar gwamnatin Nijeriya ta dakatar da aiwatar da sabbin dokar gyaran haraji har sai an kammala bincike kan zargin cewa an yi wa dokokin sauye-sauye bayan majalisa ta amince da ita.

An bayyana wannan bukata ce a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi wacce Honarabul Kingsley Chinda tare da mataimakinsa Aliyu Madaki da George Ozodinobi suka sanya wa hannu.

’Yan majalisar sun bayyana cece-kucen da ke tattare da dokokin harajin a matsayin abin damuwa sosai, suna cewa ya cancanci cikakken bincike domin kare martabar majalisa da bin doka da oda.

Kasar Birtaniya ta dakatar da bai wa ‘yan Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo biza

0

Gwamnatin kasar Birtaniya ta sanar da dakatar da tsarin ba ’yan Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo biza, lamarin da ake zargin zai shafi matafiya daga ƙasar da dama.

Wannan mataki, kamar yadda hukumomin Birtaniya suka bayyana, ya biyo bayan kin karɓar ’yan ƙasar da suka shiga Birtaniya ba bisa ƙa’ida ba.

Baya ga haka, Birtaniya ta ce manyan jami’an gwamnati da manyan baki daga Congo za su rasa damar shiga kasar kamar yadda suka saba a baya.

Rahotanni sun nuna cewa a cikin watan Nuwamba, ma’aikatar cikin gida ta Birtaniya ta gargadi DR Congo, Angola da Namibia cewa za su fuskanci takunkumin biza matuƙar ba su karɓi ’yan gudun hijira da kuma ’yan ƙasarsu masu aikata laifuka a kasashen ƙetare ba.

Za a kaddamar da aikin bututun iskar gas na AKK a 2026 – Shugaban NNPCL

0

Kamfanin man fetur na Nijeriya, NNPC Limited ya bayyana cewa ana sa ran aikin bututun gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano AKK wanda darajarsa ta kai dala biliyan 2.8 zai fara aiki a farkon shekarar 2026.

Shugaban kamfanin NNPCL Bashir Bayo Ojulari ne ya bayyana hakan bayan kammala duba aikin da Ministan harkokin albarkatun man fetur Ekperikpe Ekpo ya jagoranta tare da manyan jami’an NNPCL.

Ojulari ya ce NNPCL ta kammala manyan layukan bututun gas na AKK, wanda ya shafe shekaru da dama ya ana gudana.

Sojoji sun ceto wani mutum da shanu a tsakanin Kano da Katsina

Sojojin rundunar haɗin gwiwa na Joint Task Force sun yi nasarar ceto wani mutum da aka sace tare da kwato wasu shanu da ‘yan bindiga suka kwace, bayan artabu da suka yi da su a iyakar jihohin Kano da Katsina.

Rahotanni daga rundunar sojin sun nuna cewa lamarin ya faru ne a safiyar Lahadi a yankin Yankwada na jihar Kano, bayan sojoji sun samu bayanan sirri kan motsin wasu ‘yan bindiga da ke shigowa daga yankunan Daurawa da Kira na jihar Katsina zuwa bangaren Kano.

Majiyoyin sojin sun bayyana cewa dakarun sun tare ‘yan bindigar ne a yankin Ungwan Dogo da Ungwan Tudu, inda aka yi musayar wuta mai zafi tsakaninsu.

A yayin artabun, an samu nasarar ceto wani mutum mai suna Rabiu Alhaji Halilu, mai shekaru 38, wanda aka sace,sai dai rahotanni sun ce an harbi Halilu da bindiga a kafa, inda aka gaggauta kai shi asibitin na soji da ke Faruruwa domin samun kulawar likitoci.