DCL Hausa Radio
Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 76

Ya kamata a haramta amfani da kafafen sada zumunta ga ’yan kasa da shekara 16 a Nijeriya – Femi Falana

0

Babban lauya kuma SAN, Femi Falana, ya bukaci a haramta amfani da kafafen sada zumunta ga yara ’yan kasa da shekara 16 a Nijeriya, yana mai cewa hakan na da muhimmanci domin kare lafiyar tunani da tarbiyyar yara.

Falana ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Lagos, yayin bikin kaddamar da gasar Dare2Debate, inda ya ce kasashe da dama a duniya sun fara daukar irin wannan mataki, yana mai ambaton Ostiraliya da ta haramta wa yara ’yan kasa da shekara 16 shiga kafafen sada zumunta.

Ya kara da cewa dole ne Nijeriya ta bi wannan hanya domin amfanin yara, yana mai cewa dole a tsara ka’idoji da dokoki da za su daidaita amfani da kafafen zamani, saboda tasirin da suke da shi kan rayuwar matasa da makomar al’umma.

Ba zan koma APC ba, duk kuwa da bibiyata da fadar shugaban kasa ke yi – Sanata Natasha

0

Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta ce ba ta da niyyar ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC, duk da cewa ana ta yi mata tayin sauya sheka daga wasu mutane da ke da alaka da fadar shugaban kasa da kuma wasu ’yan majalisa.

Ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi a shirin Mic On Podcast, inda ta ce ko da rikicin da ke addabar PDP ya tsananta, ba za ta bi sahun masu sauya jam’iyya ba, tana mai cewa ba ta yarda da barazana ko rarrashi na siyasa.

Sanatar ta kara da cewa an sha tuntubarta a lokuta daban-daban, har da kwanan nan, amma ta fi son ci-gaba da zama a PDP, tana mai cewa har yanzu tana tattaunawa kan makomarta ta siyasa, ciki har da yiwuwar sake tsayawa takara, amma ba a yanke hukunci ba tukuna.

Hukumar EFCC ta gargadi ‘yan Nijeriya kan girmama masu cin hanci da rashawa

0

Hukumar EFCC ta bukaci ’yan Nijeriya da su daina yabawa ko girmama mutanen da aka samu da laifin cin hanci da rashawa, tana mai cewa hakan na raunana yaki da almundahana a kasar.

Shugaban sashen shari’a na EFCC reshen Kaduna, Nasir Salele, ya ce abin takaici ne yadda al’umma ke kare wadanda aka yanke wa hukunci, har ma a wasu lokuta su tarbe su da shagali ko ba su sarautar gargajiya bayan fitowa daga gidan yari.

EFCC ta jaddada cewa yaki da cin hanci ba aikin hukuma kadai ba ne, tana kuma kira ga kafafen yada labarai da jama’a su taimaka wajen wayar da kan al’umma da kin amincewa da cin hanci da rashawa.

John Cena ya yi ritaya daga “wrestling” bayan shafe shekaru 24 yana jan zarensa

0

Fitaccen gwarzon kokawar “Wrestling”, John Cena, ya yi ritaya bayan wasan bankwana da ya yi a Capital One Arena da ke Washington DC. Cena ya fuskanci Gunther a gasar Saturday Night’s Main Event, inda aka tilasta masa mika wuya bayan rike shi da sleeper hold, lamarin da ya jefa magoya baya cikin alhini.

Wasan ya dauki kusan mintuna 25, kuma shi ne karo na farko da John Cena ya taba mika wuya a tarihin kokawarsa. Bayan kararrawa ta buga, ‘yan kokawa daga dakin ‘yan wasa sun fito domin girmama shi, yayin da Cena ya bar abin hannunsa da takalmansa a cikin zobe, alamar yin ritaya, kafin ya yi bankwana da magoya baya.

John Cena na barin “wrestling” a matsayin gwarzo sau 17 na duniya, wanda shi ne mafi yawa a tarihin wasan. Ya fara kokawa a 2002, ya shahara da taken “You Can’t See Me”, sannan daga baya ya yi fice a fina-finai. Masana da magoya baya na kallonsa a matsayin daya daga cikin mafi girman ‘yan kokawa da WWE ta taba samu.

Gwamnatin jihar Bayelsa ta umurci binciken gawar mataimakin gwamnnan domin gano musabbabin mutuwar fuju’arsa

0

Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike (autopsy) kan gawar marigayi mataimakinsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, domin gano ainihin musabbabin mutuwarsa.

Gwamna Diri ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da tsohon Shugaban Nijeriya, Dr Goodluck Jonathan, ya kai masa ziyarar ta’aziyya a fadar gwamnati da ke Yenagoa.

Diri ya ce umarnin ya zama dole ne sakamakon jita-jita da ke yawo a kafafen sada zumunta game da mutuwar mataimakin gwamnan kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A nasa bangaren, Jonathan ya bayyana mutuwar Ewhrudjakpo a matsayin babban rashi ga al’ummar Bayelsa, yana mai cewa marigayin ya kasance mutum mai himma da aminci, wanda ya wakilci gwamnan jihar a shirye-shiryen Gidauniyar Jonathan, ciki har da taron Democracy Dialogue da aka gudanar a Benin, Jihar Edo.

Shugaba Tinubu da APC sun shirya samu dimbin kuri’u a Kudu da Arewa ta Tsakiya a zaben 2027

0

Jam’iyyar APC na tsara wata sabuwar dabara domin tabbatar wa Shugaba Bola Tinubu nasara a zaɓen 2027, ta hanyar ƙarfafa goyon baya a yankunan Kudu da Arewa ta Tsakiya, a daidai lokacin da wasu ƙungiyoyi a Arewa ke nuna rashin gamsuwa da gwamnatinsa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, majiyoyi a cikin jam’iyyar sun ce an fara wannan shiri tun sama da watanni biyar da suka wuce, bayan rahotanni sun nuna yiyuwar turjiya daga wasu sassan Arewa da kuma haɗin gwiwar ’yan adawa. Sun ce manyan jiga-jigan APC ne ke jagorantar dabarar, da nufin kakkabe barazanar siyasa tun kafin 2027.

A cewar majiyar, APC na da niyyar tabbatar da cewa dukkan jihohin Kudu sun tsaya tsayin daka tare da Tinubu, tare da jingina da muhimmancin ƙuri’un Arewa ta Tsakiya, domin rage tasirin duk wata adawa da ka iya tasowa daga Arewa.

Mo Salah ya kafa tarihi a Firimiya inda ya zama dan wasa mafi ba da gudummuwar kwallaye a kulob daya

0

Dan wasan Liverpool, Mohamed Salah, ya karya tarihin mafi yawan gudummawar kwallaye (zura kwallo da bayarwa) da dan wasa ya taba yi wa kungiya daya a tarihin firimiyar Ingila, bayan ya bayar da taimako a wasansu na yau.

Salah ya kai jimillar gudummawar kwallaye 277 a wasannin Firimiya da Liverpool, inda ya zarce tsohon tarihin Wayne Rooney na Manchester United. Ya cimma hakan ne a wasanni 302, inda ya ci 188 sannan ya bayar da 89 aka ci.

Da wannan nasara, Mo Salah ya kara tabbatar da matsayinsa a matsayin daya daga cikin manyan ‘yan wasa a tarihin Liverpool da kuma firimiyar Ingila baki daya, lamarin da ya kara masa farin jini a Anfield.

Duk inda dan Nijeriya yake bai da wuyar ganewa saboda izza da kwarin guiwa a tafiyarsa da mu’amalarsa – Kashim Shettima

0

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya ce ana iya gane dan Nijeriya a ko’ina cikin duniya, ciki har da London, saboda irin izza da kwarin gwiwa da ‘yan Nijeriya ke nunawa a tafiyarsu da mu’amalarsu.

Shettima ya bayyana hakan ne a wajen bikin kammala karatun Senior Executive Course 47 a cibiyar NIPSS da ke Kuru, jihar Filato, inda ya ce ‘yan Nijeriya na tafiya da cikakken kwarin gwiwa da alfahari da asalinsu.

Hakazalika ya jaddada cewa wannan gwamnati ba za ta bari Nijeriya ta gaza ba, yana mai cewa Nijeriya ita ce ginshikin makomar bakar fata a duniya, kuma dole ne kasar ta yi aiki domin amfanin kanta da duniya baki daya.

Hukumomin Bénin sun bada sammacin kama Kemi Seba

0

Kotu a kasar Bénin ta bada sammacin kama fitaccen dan gwagwarmayar kasar mai fafitikar kare hakkin Afirka Kemi Seba bisa tuhumar sa da aikata laifuka

A cikin laifukaan da ake zargin shi har da na neman tada zaune tsaye da na kiran al’ummar su yi bore da yin wa gwamnati tawaye

Wannan sammaci ya biyo bayan wani bidiyo da dan fafitikar ya wallafa a shafinsa na sada zumanta inda ya danganta sojojin da suka yi yunkurin juyin mulkin rana 7 ga watan Disemba a Bénin da ‘yan kishin kasa

Fusatattun matasa a Jihar Neja sun aika wani matashi lahira bisa zargin hallaka mahaifiyarsa

0

Wani matashi mai shekaru 25, mai suna Adamu Abdullahi, ya rasa ransa bayan da wasu fusatattun jama’a suka yi masa dukan tsiya har lahira a garin Suleja, ta jihar Neja, bisa zargin da aka yi masa na soka wa mahaifiyarsa wuka.

Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Asabar, bayan wata takaddama da ta barke tsakanin matashin da mahaifiyarsa mai shekaru 45, Hauwa Sanusi, kan rabon gadon mahaifinsa marigayi. Rahotanni sun ce mahaifiyar ta rike rabon gadon ne domin gudun kada a almubazzarance shi.

Wata majiya ta shaida cewa matashin, wanda ya dade baya zama a Suleja, ya dawo garin ne ba tare da sanin jama’a ba, inda ya kai wa mahaifiyarsa hari da wuka sau da dama.

Ihun da matar ta yi ne ya ja hankalin makwabta, suka kamo matashin yayin da yake kokarin tserewa, inda daga bisani wasu matasa suka yi masa dukan tsiya kafin ‘yan sanda su iso. An kuma tabbatar da cewa matar da aka kai wa harin ita ce mahaifiyarsa ta jini.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai bai bayyana dalilin rikicin ba.