DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 77

Hukumomin Bénin sun bada sammacin kama Kemi Seba

0

Kotu a kasar Bénin ta bada sammacin kama fitaccen dan gwagwarmayar kasar mai fafitikar kare hakkin Afirka Kemi Seba bisa tuhumar sa da aikata laifuka

A cikin laifukaan da ake zargin shi har da na neman tada zaune tsaye da na kiran al’ummar su yi bore da yin wa gwamnati tawaye

Wannan sammaci ya biyo bayan wani bidiyo da dan fafitikar ya wallafa a shafinsa na sada zumanta inda ya danganta sojojin da suka yi yunkurin juyin mulkin rana 7 ga watan Disemba a Bénin da ‘yan kishin kasa

Fusatattun matasa a Jihar Neja sun aika wani matashi lahira bisa zargin hallaka mahaifiyarsa

0

Wani matashi mai shekaru 25, mai suna Adamu Abdullahi, ya rasa ransa bayan da wasu fusatattun jama’a suka yi masa dukan tsiya har lahira a garin Suleja, ta jihar Neja, bisa zargin da aka yi masa na soka wa mahaifiyarsa wuka.

Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Asabar, bayan wata takaddama da ta barke tsakanin matashin da mahaifiyarsa mai shekaru 45, Hauwa Sanusi, kan rabon gadon mahaifinsa marigayi. Rahotanni sun ce mahaifiyar ta rike rabon gadon ne domin gudun kada a almubazzarance shi.

Wata majiya ta shaida cewa matashin, wanda ya dade baya zama a Suleja, ya dawo garin ne ba tare da sanin jama’a ba, inda ya kai wa mahaifiyarsa hari da wuka sau da dama.

Ihun da matar ta yi ne ya ja hankalin makwabta, suka kamo matashin yayin da yake kokarin tserewa, inda daga bisani wasu matasa suka yi masa dukan tsiya kafin ‘yan sanda su iso. An kuma tabbatar da cewa matar da aka kai wa harin ita ce mahaifiyarsa ta jini.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai bai bayyana dalilin rikicin ba.

Rundunar sojin kasa ta Nijeriya ta yaye sabbin sojoji 3,439

0

Akalla sabbin kananan sojojin Nijeriya 3,439 ne suka kammala horo a cibiyar horas da sojoji ta Nijeriya da ke Zariya.

Sabbin sojojin, wadanda ke cikin rukuni na 89 na daukar sojoji na yau da kullum, sun shafe watanni shida suna horo kafin a gabatar da su a bikin fitar da su wato Passing Out Parade da aka gudanar ranar Juma’a. Bayan kammala horon, za a tura su sassa daban-daban na kasar domin gudanar da ayyukansu.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojojin kasa, Kanal Appolonia Anele, ta fitar, ta ce Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bukaci sabbin sojojin da su rungumi biyayya, ladabi da kwarewa yayin da suke shiga aikin kasa, yana mai cewa karin adadinsu zai kara karfin rundunar wajen tinkarar barazanar tsaro a cikin gida da ma ketare.

Ba tare da sanya siyasa ba, zaman Bello Matawalle a matsayin karamin ministan tsaro ya yi daidai – Sheikh Ahamd Gumi

0

Masana harkar soji sun ce rikice-rikicen al’umma ba sa magantuwa da karfin soja kaɗai; sulhu ne babban jigo.

Babban malamin addini Dr. Ahmad Abubakar Gumi ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook inda ya kara da cewa, Minista Bello Matawalle ya fahimci wannan lokacin shugabancinsa a Zamfara, inda kare rayukan jama’a shi ne babban aiki.

Ta hanyar tuntubar bangarorin da ke rikici, ya kusan kawo karshen ta’addanci, inda hanyoyi da kasuwanni suka dawo lafiya kafin rashin hadin kai daga soja ya sake kawo rikici.

Yanzu a matsayinsa na ministan tsaro, Matawalle na amfani da iliminsa wajen kawo zaman lafiya, inda hanya ce da gwamnati ke fatan tabbatar da tsaro, hadin kai, da ci gaba a Nijeriya.

Tsohon Sanata a Nijeriya ya bukaci shugaba Tinubu ya yi amfani da karfin soja a kan Burkina Faso domin sako sojojin Nijeriya da ke tsare a kasar

0

Tsohon ɗan majalisar dattawa daga jihar Ekiti kuma jigo a jam’iyyar APC, Sanata Ayodele Arise, ya bukaci Shugaba Tinubu da ya yi la’akari da amfani da karfin soji kan ƙasar Burkina Faso domin ganin an sako sojojin Nijeriya da ake tsare da su a can.

Arise ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wata hira da ya yi a gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce duk da cewa sojojin Nijeriya na fuskantar manyan ƙalubale a gida sakamakon ta’addanci da ‘yan bindiga, bai kamata a kawar da zaɓin daukar matakin soja kan Burkina Faso ba.

Ya tuno da wani misali na tarihi, inda ya ambaci harin da Isra’ila ta kai Entebbe a Uganda a 1976, yana mai cewa irin wannan mataki na iya tilasta wa shugabannin Burkina Faso sake tunani. A cewarsa, Nijeriya na bukatar ta nuna wa makwabtanta cewa duk da kyakkyawar mu’amala, ba za a yarda a raina ƙasar ba.

Sanatan, wanda ya taba wakiltar Ekiti ta Arewa a majalisar dattawa, ya kuma bayyana goyon bayansa ga matakin soja da aka dauka kwanan nan a Jamhuriyar Benin domin dakile yunkurin juyin mulki.

Babu jam’iyyun PDP, ADC a jikin takardar zaben kananan hukumomin da ke gudana a jihar Borno

0

A yayin da masu kada kuri’a a Borno ke zaben shugabancin kananan hukumomi da majalisun tarayya, an lura cewa takardar zabe ba ta dauke da alamomin jam’iyyar PDP da ADC.

Daga farko, jam’iyyun biyu sun bayyana cewa ba za su halarci zaben ranar Asabar ba, sai dai rahoton jaridar Daily Trust daga Maiduguri, Jere da Konduga ya nuna cewa masu kada kuri’a sun yi karanci a wuraren zabe, duk da cewa an fara zabe da karfe 8:00 na safe.

Takardar zaben ta nuna jam’iyyu guda shida kawai: APC, Boot Party, Labour Party (LP), PRP, NNPP da SDP, ba PDP da ADC ba.

Sakataren PDP na Borno, Amos Adziba, ya ce jam’iyyar ta janye daga zaben ne saboda rashin yarda da hukumar zabe da kuma tsadar kudin fom din sha’awa shiga takara da na nadin dan takara.

Shugaban Hukumar Zabe ta jihar Borno, Tahir Shettima, ya ce hukumar na aiki ne bisa doka kuma a muradin dukkan jam’iyyun da suka nuna sha’awa wajen zaben.

Ba ni da wata nadamar goyon bayan Tinubu tun 2022 – Nyesome Wike

0

Ministan Abuja a Nijeriya, Nyesom Wike, ya ce bai taɓa yin nadamar bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu tun kafin zaɓen 2023 ba, yana mai jaddada cewa matsayinsa bai sauya ba kafin zaɓe, lokacin zaɓe da kuma bayan kammala zabe.

Wike ya bayyana hakan ne yayin wani taro na musamman da aka shirya domin cika shekarunsa 58 a gidansa da ke Abuja, inda ya ce ya tsaya tsayin daka kan goyon bayan Tinubu bisa ƙa’idar gaskiya, adalci da kuma ra’ayinsa na cewa mulki ya kamata ya koma Kudu.

Tsohon gwamnan Jihar Rivers ya ce shi kaɗai ne daga manyan ’yan adawa da suka fito fili suka mara wa Tinubu baya a wancan lokaci, yana mai cewa sakamakon zaɓe a Rivers ya nuna irin tasirinsa, inda APC ta lashe zaɓen shugaban ƙasa, yayin da PDP ta yi nasara a sauran matakai.

Manyan ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban sun halarci taron domin taya Wike murna, tare da yaba rawar da yake takawa a siyasar Nijeriya.

Ministocin kasashen ECOWAS sun yi bitar barazanar tsaro da inganta tattalin arziki a taron kungiyar

0

Taron Ministocin ECOWAS karo na 95 ya kammala a Abuja bayan kwanaki na tattaunawa kan matsalolin tsaro, siyasa da tattalin arziki a yankin Yammacin Afirka.

A taron da aka gudanar daga 10 zuwa 12 ga watan Disamba, ministocin sun tattauna barazanar ta’addanci a yankin Sahel, yaduwar makamai ba bisa ka’ida ba, laifuffukan ƙetare ƙasashe, matsalar tsaron teku a Tekun Guinea, da kuma juyin mulkin da ba bisa tsarin dimokuraɗiyya ba.

Da yake jawabin rufe taron, Ministan Harkokin Wajen Saliyo, Timothy Kabba, ya ce ECOWAS ta jaddada cewa dimokuraɗiyya, bin doka da oda, da tsarin mulki na gaskiya ba za su zama abin sulhu ba, yana mai cewa haɗin kai ne makamin yankin wajen shawo kan kalubalen da ke gabansa.

Hukumomin Bénin na zargin Togo da ba wa jagoran juyin mulkin da bai yi nasara ba mafaka

0

Kwanaki shida bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar Bénin, rahotanni sun nuna har yanzu ba a san inda laftanal kanal Pascal Tigri madugun juyin mulkin yake ba

Sai dai a wani rahoto da jaridar Jeune Afrique ta wallafa ta ce akwai yiwuwar cewa laftanal kanal Pascal Tigri yana kasar Togo, zargin da hukumomin Togo ba su karyata ko tabbatar da shi ba.

Dama dangantakar da ke tsakanin kasashen tana tangarda sakamakon wadansu matsaloli da suka wakana a tsakaninsu da suka hada da na bambancin ra’ayi akan kungiyar AES wacce kasar Togo ke nuna tana tare da ita har ma ta yi ikirarin yiwuwar shiga cikin ta yayin da kuma Bénin ke nuna adawa da kungiyar har ta kasance a sahu na gaba-gaba a kan matakin ECOWAS na kai wa Nijar hari a lokacin da sojoji suka yi wa Bazoum juyin mulki

Kazalika, wani dan majalisar dokokin kasar Bénin ya bayyana cewa a 2021, an masa tayin biliyoyin kudade na CFA daga kasar Togo dan ya bada hadin kai wajen tsara juyin mulki a Bénin

A yanzu haka kuma, ko baya ga Pascal Tigri da ake zargin yana samun mafaka a Togo, da dama daga cikin masu adawa da gwamnatin Bénin da ‘yan fafutukar masu sukar gwamnatin Talon na samun mafaka a Togon

Tsare-tsaren Tinubu na da manufar inganta harkar lafiya a Nijeriya – Mohammed Idris

0

Ministan yaɗa labarai da wayar da Kan jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ya ce manufofin Shugaba Bola Tinubu na fara magance matsalar ficewar ƙwararrun likitoci (japa) da sauran ƙalubalen lafiya a Nijeriya.

Idris ya bayyana hakan ne a Abuja yayin bikin rantsar da daliban MBBS na jami’ar Nile ajin 2025, inda ya ce sabbin likitocin za su taimaka wajen inganta harkar kiwon lafiya da gwamnatin tarayya ke kokarin gyarawa.

A cewarsa, gwamnati na ƙirƙirar yanayi mai kyau da zai sa ƙwararru su zauna su yi aiki a gida, yana mai ƙara da cewa tuni wasu da suka bar ƙasar suna komowa Nijeriya, sakamakon sabbin tsare-tsaren da aka kafa, musamman a bangaren lafiya.