DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
HomeSiyasaKotu ta sanya ranar sauraron kara kan rikicin jam'iyyar ADC

Kotu ta sanya ranar sauraron kara kan rikicin jam’iyyar ADC

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 14 ga watan Afrilu domin sauraron ƙarar da Nafiu Bala Gombe ya shigar, yana neman hana wani ɓangare na jam’iyyar ADC jagorancin David Mark daga bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya rawaito cewa alkalin kotun, Justice Emeka Nwite, ne ya sanya ranar bayan an aika takardun gayyata ga ɓangarorin da ke cikin shari’ar.

Tun da farko, Justice Emeka Nwite ya dakatar da shari’ar na ɗan lokaci domin jiran hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, bayan lauyoyin ɓangaren waɗanda ake ƙara sun sanar da kotu cewa sun shigar da ƙara a can.

Sai dai a hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke a ranar 12 ga Maris, an umurci ɓangarorin da su koma kotun farko, tare da ci gaba da bin tsarin da yake a baya, har sai an yanke hukunci a kan ƙarar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata