Ministan kasa a Ma’ikatar Tsaron Nijeriya Mohammed Bello Matawalle, ya gabatar ma Shugaban kasa Bola Tinubu jiragen ruwa marasa matuki guda biyu a fadar shugaban kasar da ke Abuja.
Hakan na kunshe a wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai Henshaw Ogubike ya fitar a Abuja.
Sanarwar ta ce Ministan ya shaida wa shugaban kasa cewa, Jiragen biyu za su taimaka wajen yaki da ta’addanci a bakin gabar ruwa.
Matawalle ya sanar da Tinubu cewa wadannan jirage na da nufin inganta sabbin fasahohin da za su kara wa sojojin Najeriya kwarin gwiwa wajen tunkarar kalubalen tsaro.