DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Idan shugabanni suka kula da fannin,lafiya,Ilimi da yaki da talauci za a samu gagarumin sauyi a Nijeriya-Obi

-

Idan shugabanni suka kula da fannin,lafiya,Ilimi da yaki da talauci za a samu gagarumin sauyi a Nijeriya-Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya bukaci shugabanni da su yi amfani da dimbin al’ummar Nijeriya wajen samar da ci gaba a fadin kasar.

Google search engine

Ya bayyana hakan ne a yayin bikin tunawa da ranar yawan jama’a ta duniya, wanda ya ce yana tunatar da dukkan bukatar da ake da ita na magance matsalolin da suka shafi jama’a domin samar da ci gaba a cikin al’umma.

Ya ce idan aka yi la’akari da dimbin matasan da ke da tarin yawa, aka tallafa musu da hanyoyin samun cigaba zai samar da al’umma mai albarka.

Nijeriya a matsayinta na kasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka kuma kasa ta 6 a duniya mafi yawan al’umma, Nijeriya ta ci gaba da kasancewa mai albarka ta fannin albarkar dan Adam, wanda idan aka yi nazari sosai ta hanyar yin abin da ya dace a fannoni 3 mafi muhimmanci na ci gaban al’umma kiwon lafiya, ilimi da yaki da talauci, da kasar za ta samu gagarumin sauyi da ci gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

INEC za ta fara sabuwar rijistar katin zaɓe daga ranar 18 ga Agusta a Nijeriya

Hukumar Zaɓen Nijeriya INEC ta sanar da ranar 18 ga watan Agusta, 2025 a matsayin ranar da za ta fara sabuwar rijistar katin zaɓe a...

Kamfanin NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar man birnin Port Harcourt

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar mai ta Fatakwal ga yan kasuwa A Yayin wani taro da kamfanin ya gabatar...

Mafi Shahara