DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sanatocin Arewacin Nijeriya sun yaba wa Shugaba Tinubu kan umarnin sakin kananan yara da aka gurfanar saboda zanga-zangar#BadGovernance

-

Shugaba Tinubu

Sanatoci daga yankin Arewa sun yabawa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa bayar da umarnin sakin kananan yara da ake tsare da su a lokacin zanga-zangar #BadBadGovernance.

Sanatocin karkashin kungiyar Sanatocin Arewa, a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta, Abdulaziz Musa Yar’adua, a ranar Litinin, sun ce shawarar da Tinubu ya yanke ya nuna aniyarsa ta kare hakki da walwalar matasan Nijeriya.

Ya ce bisa umarnin da shugaban ya bayar ga babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi, da a gaggauta sakin mutanen, wannan wani abin farin ciki ne, kuma sun nuna godiya da jagorancin shugaban kasa wajen magance wannan matsala.

A cewar sanarwar an kuma yaba da kokarin shugabannin Arewa da suka yi namijin kokari wajen ganin an sako wadannan yara kanana.Jajircewarsu da bayar da shawarwari sun taimaka wajen kawo karshen wannan al’amari gaba daya.           

Ya kuma yi kira ga shugabannin Arewa da su ba da fifiko kan tsaro da ilimin yara,ya ce yana da mahimmanci a samar da yanayi mai kyau da matasa za su girma da bunƙasar tattalin arziki tare da ilimi ba tare da cin zarafi ba.

  

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Muna kokarin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan 1 – Kashim Shettima

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ce gwamnatin kasar na kan hanyar bunkasa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan 1 cikin shekaru goma masu zuwa. Kashim...

Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da direba da fasinjoji a Katsina

Jami’an rundunar ‘yan sandan Nijeriya sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane a hanyar Funtua zuwa Gusau a Katsina. Jami’an sun yi artabu da ‘yan...

Mafi Shahara