DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sufeton ‘yan sandan Nijeriya ya ba da umarnin bincike kan cin zarafin yaran da aka kama yayin zanga-zangar#BadGovernance

-

Kayode Egbetokun

Babban Sufeton ‘yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan zarge-zargen cin zarafin kananan yara da aka kama yayin zanga-zangar #BadGovernance

Google search engine

 Jaridar PUNCH  ta rawaito cewa a ranar Juma’a, an gurfanar da mutane 76 da ake zargi, galibinsu kananan yara da ba su samu isasshen abinci mai gina jiki ba,shida daga cikin yara kanana sun fadi a wajen shari’ar hakan yasa aka a fitar da su daga wurin shari’a domin samun agajin gaggawa.

Da yake mayar da martani game da lamarin a ranar Asabar, IG ya yi iƙirarin cewa suman da wasu yara ƙanana sukai a kotun an shirya shi ne don jawo hankulan mutane.

Bayan da al’umma suka nuna bacin ransu kan lamarin, shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin a janye tuhumar da ake yi wa kananan yaran.                    

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Muyiwa Adejobi ya fitar a daren ranar Litinin, ya bayyana cewa IG ya bayar da umarnin gudanar da bincike yaran a lokacin da suke tsare.

 Adejobi ya kara da cewa, da samun rahoton binciken, IG ya sha alwashin magance duk wasu kura-kurai da aka gano.

 Ya ce babban sufeton ‘yan sandan , yayin da yake birnin Algiers na kasar Aljeriya don halartar taron kwamitin hadin gwiwar ‘yan sanda na kungiyar Tarayyar Afirka, ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kenya da Senegal sun kulla yarjejeniyar shige da fice ba tare da biza ba

Gwamnatocin Kenya da Senegal sun bai wa juna damar shige da fice ga 'yan kasashensu ba tare da biza ba na tsawon kwanaki 90. DW Africa...

Majalisar dattawan Nijeriya ta bukaci gwamnati ta kara wa sojoji albashi

Majalisar dattawan Nijeriya ta bukaci gwamnati ta sake yin duba kan albashin da ake biyan jami'an tsaro musamman ma soji a fadin kasar. Majalisar ta bayyana...

Mafi Shahara