DCL Hausa Radio
Kaitsaye

APC ta lashe zaben Gwamnan jihar Ondo

-

Hukumar zabe a Nijeriya ta bayyana gwamna Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ondo da kuri’u 366,781.

Shi kuwa ‘dan takarar jami’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin gwamna Agboola Ajayi ya samu kuri’u 117,845.
Jam’iyyar Labour Party da ta samu kuri’u 1,162 kamar yadda RFI Hausa ta rawaito.
Shugaban jami’ar gwamnatin tarayya dake Lokoja kuma baturen zaben Farfesa Olayemi Akinwunmi ne ya gabatar da sakamakon zaben a gaban ‘yan jarida bayan kammala tattara alkaluman kananan hukumomi 18 wadanda aka tabbatar da nasarar Aiyedatuwa a cikin su baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan bindiga sun hallaka manoma 32 a jihar Niger

Akalla manoma 32 ne aka hallaka a hare-haren da ’yan bindiga suka kai kan al’ummomin Tugan-Makeri, Konsoko da Pissa a karamar hukumar Borgu ta Jihar...

Peter Obi ya bukaci matasa da su nuna kauna da kishin Nijeriya albarkacin ranar masoya

Tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya, Peter Obi, ya bukaci ’yan Nijeriya musamman matasa su yi bikin ranar masoya ta Valentine cikin nuna kishin ƙasa da...

Mafi Shahara