DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnan Jihar Kebbi ya ba da umurnin kamo wasu mutane da ake zargi da hannu wajen kai hari ga fulani

-

 

Gwamnan Kebbi Nasir Idris

Google search engine

Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris ya ba da umurnin kama wasu mutane da ake zargi suna da hannu a harin da aka kai wa wasu fulani biyo bayan harin da kungiyar Lakurawa ta kai Mera

A wata ziyarar jaje da ya kai garin Mera dake karamar hukumar Augie, gwamnan yayi Allah wadai da harin ramuwar gayya wanda yayi sanadiyar halaka wasu Fulani guda shida.

Rahotanni sun nuna cewa an kai harin ne kan Fulanin da ake zargin suna da hannu a harin Mera na farko, inda ‘yan ta’addan Lakurawa suka kashe mutane 17. 

Da yake jawabi ga mazauna yankin da lamarin ya faru Gwamnan ya nuna damuwar sa bisa faruwar lamarin, inda ya ce, ya bayar da umarnin a kamo wadanda ke da hannu wajen harin da aka kai wada Fulanin da ba su ji ba ba su gani ba da sunan ramuwar gayya.

            

Gwamnan ya jaddada cewa bai kamata mutane su dunga daukar doka a hannunsu ba, ya kuma bukace su da sukai rahoto ga jami’an tsaro da zarar suka ga wani abu da basu amince da shi ba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara