DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan Nijeriya na rayuwar karya kafin a cire tallafin man fetur in ji Shugaba Tinubu

-

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce ‘yan kasar na rayuwar karya da hakan ya sa tattalin arzikin kasar ya yi mummunar faduwa kafin ya hau mulki ya cire tallafin man fetur.
Shugaban kasar ya ce akwai bukatar a ceto kasar daga yunkurin durkushewa da ya sanya ala-tilas sai an bullo da hanyoyi da dabarun da za su iya rike ta irinsu cire tallafin man fetur da kokarin daidaita canjin kudi.
Shugaban kasar da ya samu wakilcin shugaban jami’ar Ilorin Prof Wahab Egbewole, ya yi wannan furucin ne a wajen taron yaye dalibai karo na 34&35 na jami’ar tarayya da ke Akure jihar Ondo a karshen mako in ji jaridar Daily Trust.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

ADC ta nesanta kanta da Nasiru El-Rufa’i bayan taron jam’iyyar da aka yi tashin hankali a Kaduna

Rikicin siyasa na ƙara kamari a jihar Kaduna bayan jam’iyyar ADC ta nesanta kanta daga wani taron da aka danganta da tsohon gwamnan jihar, Nasir...

Dokar ta-bacin da aka kakaba a jihar Rivers za ta kare a ranar 18 ga watan Satumba, 2025, in ji Nyesom Wike

Ministan Abuja Nyesom Wike, ya bayyana kwarin gwiwar cewa dokar ta-baci da aka ayyana a jihar Rivers za ta ƙare aiki a ranar 18 ga...

Mafi Shahara