DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Zaben Amurka, sabon taken Nijeriya da rumbun lantarki na kasa, na cikin abubuwan da ‘yan Nijeriya su ka fi nema a shafin Google a 2024

-

Kamfanin Google ya fitar da jadawalin abubuwan da ‘yan Nijeriya suka fi nema a kan shafin a shekarar 2024 da muke bankwana da ita.
Bayanin da kamfanin ya fitar a ranar Talata, ya nuna cewa ‘yan Nijeriya sun fi mayarda hankali akan abubuwan da suka shafi siyasa da tattalin arziki.
Tambayar da ta fi shigewa ‘yan Nijeriya duhu ita ce ‘Nawa ne farashin dala zuwa naira a yau?’
Ga jerin abubuwan da aka fi nema a Google cikin shekara ta 2024:
1. Zaben Amurka (US elections)
2. Sabon taken Nijeriya (New national anthem)
3. Rumbun lantarki na kasa (National grid)
4. Albashi mafi karanci (Minimum wage)
5. Fashewar wani abu a Ibadan (Ibadan explosion)
6. Zaben jihar Edo (Edo state election)
7. Zanga-zanga a Nijeriya (Protest in Nigeria)
8. Yajin aikin ‘yan kwadago (Labour strike)
Da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

ECOWAS ta amince John Mahama ya mata takarar shugabancin AU a 2027

Majalisar Ministocin ECOWAS ta amince da Shugaban Ghana, John Mahama, a matsayin É—an takarar kungiyar da zai nemi kujerar Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika (AU) a...

Neman tazarce na hana wasu gwamnoni yin aiki – Umar Bago

Neman tazarce a 2027, ne ke hana ni korar jami'an da ba su da amfani a gwamnatina - In ji Gwamna Umar Bago Gwamnan jihar Neja,...

Mafi Shahara