DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu ta yanke wa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa a Jigawa

-

Kotu ta yanke wa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa

Wata babbar kotu a Jihar Jigawa ta yanke wa wasu masu garkuwa da mutane hukunci  kisa ta hanyar rataya.

Da ya ke zartar da hukunci alkalin kotun mai shari’a Mohammed Musa Kaugama ya ce an sami mutanen biyu da laifuka bakwai da suka hada da yin garkuwa da mutune da hada baki da fashi da makami da haura gidan mutane.

Google search engine

A ranar 21 ga watan Yunin 2021 ne mutanen biyu wato Sani Mohammed da Babannan Saleh, dauke da makami suka haura gidan Hamidi Abdu da ke garin Shangel a karamar Hukumar Ringim inda suka kwace masa kudade masu yawa sannan suka ta fi da shi, daga baya suka nemi kudin fansa har naira miliyan 12 kafin su sake shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

NAHCON ta gargadi maniyyata Hajjin 2026 na Nijeriya kan yin rijista da wuri

By Fatima Aminu Dabo Hukumar jin daɗin alhazai ta kasa NAHCON ta sanar da jadawalin aikin Hajjin 2026, inda ta bayyana cewa 20 ga Maris, 2026...

Ana ci gaba da neman wata dattijuwa bayan kifewar kwale-kwale dauke da fasinja 11 a Sokoto

An gano gawar wani matashi mai shekara 29 da ya rasa ransa a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a Jihar Sokoto.Lamarin ya faru...

Mafi Shahara