DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Custom sun kama haramtattun kayayyaki na sama da miliyan 229 cikin mako guda Ogun

-

Custom sun kama haramtattun kayayyaki na sama da miliyan 229

Hukumar hana fasa kauri ta Nijeriya reshen jihar Ogun, ta yi nasarar kama wasu haramtattun kayayyaki da kudinsu ya kai Naira miliyan 229 da dubu 112 da 424.

Kwanturolan hukumar, Mohammed Shuaibu ne ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin taron tattaunawa da aka gudanar a Idiroko da ke jihar. 

Google search engine

Shuaibu wanda a makon da ya gabata ya kama aiki a jihar matsayin kwantirolan hukumar ya zayyana wasu daga cikin haramtattun kayayyakin da suka kama waɗanda suka hada da buhu dubu 2 da 169 na shinkafa yar waje, da buhunan tabar wiwi dubu 1 da 128 mai nauyin kilogiram dubu 1 da 109 digo 3 da sauran kayayyakin da aka hana shigowa da su Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

INEC ta shiga tsakani kan rikicin shugabanci a PDP

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta shiga tsakani kan rikicin shugabancin PDP, inda ta gayyaci bangarorin jam’iyyar biyu zuwa hedikwatarta da ke...

APC ta yi wa Gwamnan jihar Plateau maraba da shiga cikinta

Jam'iyyar APC reshen jihar Plateau ta bayyana yi wa Gwamnan jihar Caleb Mutfwang maraba da shiga cikinta, bayan ficewa daga jam‘iyyar PDP.   Sakataren jam'iyyar Shitu Bamaiyi...

Mafi Shahara