![]() |
Custom sun kama haramtattun kayayyaki na sama da miliyan 229 |
Hukumar hana fasa kauri ta Nijeriya reshen jihar Ogun, ta yi nasarar kama wasu haramtattun kayayyaki da kudinsu ya kai Naira miliyan 229 da dubu 112 da 424.
Kwanturolan hukumar, Mohammed Shuaibu ne ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin taron tattaunawa da aka gudanar a Idiroko da ke jihar.
Shuaibu wanda a makon da ya gabata ya kama aiki a jihar matsayin kwantirolan hukumar ya zayyana wasu daga cikin haramtattun kayayyakin da suka kama waÉ—anda suka hada da buhu dubu 2 da 169 na shinkafa yar waje, da buhunan tabar wiwi dubu 1 da 128 mai nauyin kilogiram dubu 1 da 109 digo 3 da sauran kayayyakin da aka hana shigowa da su Nijeriya.