![]() |
Joseph Aoun |
An kada kuri’ar zaben shugaban kasar Lebanon inda aka zabi Joseph Aoun a matsayin shugaban kasa a zagaye na biyu na zaben da ‘yan majalisar dokokin kasar a ranar Alhamis, wanda ya kawo karshen rashin shugaba da kasar ke fama da shi , tare da shafe shekaru biyu ana kasar na fama da rikici.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa Kakakin majalisar kasar Nabih Berri ne ya sanar da cewa Joseph Aoun ne shugaban kasa, bayan ya samu kuri’u 99 daga cikin 128 bayan da aka gaza samun kuri’u da ake bukata a zagayen farko da aka gudanar.
Tuni dai aka rantsar da sabon shugaban mai shekaru 61, wanda ake kyautata zaton zai samu goyon bayan Amurka, Saudi Arabia da kasashen yammacin duniya.