DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Babban Hafsan Sojin kasa COAS, Olufemi Oluyede, ya amince da canjawa manyan hafsoshi a Nijeriya wajen aiyyu

-

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu, ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Google search engine

Nwachukwu, ya bayyana cewa, sake tura sojoji wani shiri ne na inganta aiki ayyukan rundunar.

Ya ce jami’an da abin ya shafa sun hada da kwamandojin rundunar, manyan hafsoshi, manyan kwamandojin (GOC), kwamandojin cibiyoyin horar da sojoji, birgediya da sauran manyan mukamai.

 A cewarsa, sake tura dakarun da kuma sauyawa wasu wuraren aiki na nuni da kudurin rundunar na tabbatar da tsarin jagoranci da zai iya magance matsalolin tsaro a fadin kasar.

Mista Nwachukwu ya ce wasu daga cikin manyan hafsoshin da aka canza wa wajen a hedkwatar sojojin sun hada da Manjo Janar Lawrence Fejokwu, daga Kwalejin Tsaro ta kasa zuwa sashin kula da harkokin soji, wanda aka nada shi Shugaban Gudanarwa na rundunar Soji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin Tinubu ba ta tattaunawa da ‘yan bindiga – Daniel Bwala

Hadimin shugaban Nijeriya Bola Tinubu, Daniel Bwala, ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba ta taɓa yin tattaunawa da ’yan ta’adda ko biyan su kuɗin fansa...

Kudin tikitin jiragen sama a wasu sassan Nijeriya ya haura Naira 300,000 – Punch

Wani bincike da jaridar Punch ta gabatar, ya nuna cewa kudin tikitin jiragen sama a wasu sassan Nijeriya ya zarta Naira 300,000.   Binciken ya nuna cewa...

Mafi Shahara