DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu ta amince da gyara kan tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon Ministan wutar lantarki Dakta Olu Agunloye.

-

 

Google search engine

Babbar kotun birnin tarayya Abuja, ta amince da bukatar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa na yin kwaskwarima kan tuhumar da ake yi wa tsohon ministan wutar lantarki, Dakta Olu Agunloye.

Mai shari’a Jude Onwuegbuzie ya amince da gyaran ne yayin da yake yanke hukunci kan rashin amincewar wanda ake kara kan karar da aka shigar a ranar 25 ga watan Yuni, 2024.

Dakta Olu Agunloye dai na fuskantar tuhumar laifuka bakwai da EFCC ta shigar a gaban kotu mai lamba FCT/HC/CR/617/2023.

Laifukan sun shafi na  jabu, kin bin umarnin shugaban kasa, da kuma aikata  almundahana da suka shafi aikin tashar wutar lantarki ta Mambila a jihar Taraba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara