DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Muna neman kari a kasafin kudi don samar da ayyukan yi – Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Muhammad Dingyadi

-

 

Ministan kwadago Muhammad Dingyadi

Google search engine

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Muhammad Dingyadi, ya ce ma’aikatar na bukatar karin kudade cikin kasafin kudin 2025, domin bunkasa ayyukan ta.

Ya ce za a yi amfani da kudaden musamman wajen gyarawa, sake ginawa da kuma samar da kayan aiki ga cibiyoyin bunkasa sana’o’i da ke karkashin ma’aikatar da hukumomi a fadin kasar, da nufin samar da ayyukan yi ga al’umma.

Dingyadi ya bayyana haka ne a lokacin da yake kare kasafin kudin 2025, a gaban kwamitin majalisun dokoki da na dattawa. Ya ce jimillar kasafin naira biliyan 46 da aka ware wa ma’aikatar a wannan shekarar ba zai wadatar ba wajen cimma manufofin da ake so a cimma.

Dangyadi ya jaddada cewa samar da ayyukan yi ta hanyar bunkasa fasahar zamani na da matukar muhimmanci wajen cimma wani bangare na manufofin gwamnatin shugaba Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An fitar da jihohi 4 a Gasar Kokawar Nijar ta 2025

Kwana na uku da fara gasar kokawar gargajiya a Nijar tuni an yi waje da jihohi hudu daga cikin takwas na kasar daga jerin wanda...

Ya kamata a canza salon yadda ake yakar ‘yan bindiga a Nijeriya

Daga: Farfesa Usman Yusuf Litinin : 22 Disamba 2025 Ban taɓa gudu ko ja da baya ba ko nuna wata fargaba wajen bayyana matsayina a kan yaƙin...

Mafi Shahara